WAYA CEN-CENTA YAYI WA MUTANE LIMANCI
******************************************
Yana da Kyau Idan Zakuyi Sallah A Wurin da Ba Liman Ne Kuke da shi ba To ku Lura da Wasu Abubuwa Kan Wanda Zai Jaku Sallah daga Cikin Ku;
Na farko: Wanda ya fi karatun Alqur’ani, wato wanda ya fi yawan haddace shi, kuma yafi sauran fahimtar hukunce-hukuncensa.
Na biyu: Wanda ya fi sanin Sunnah, wato wanda yasan ma’anoninta da hukunce-hukuncenta.
Na uku : Wanda ya dade da yin hijira, daga garin kafirci zuwa garin musulunci. Idan ba hijira a lokacin sai a gabatar a kan wanda ya riga tuba da qaurace wa sabo.
Na hudu : Idan su yi daidai a duk abin da ya gabata, to sai a sa wanda ya fi yawan shekaru.
Dalili akan abin da ya gabata hadisin Abu Mas’ud Al-ansari (RA), ya ce, Manzon Allah (Saww) ya ce, “Wanda ya fi mutane karatun Alqur’ani shi zai limance su, idan sun yi daidai a karatu, to wanda ya fi su sanin sunnah, in sun yi daidai a sanin sunnah, to wanda ya fi dade wa da hijira, idan sun yi daidai a hijira to wanda ya dade da musulunta” (Imamu Muslim ne ya rawaito shi).
Haka kuma Ana kula da wannan jerin yayin nada limamin masallaci, ko in a cikin jama’a ne wadanda babu lmami ratibi a cikinsu, in akwai limami a ratibi a cikinsu, ko kuma wanda ake gidansa yana nan, ko kuma wanda yake jagora to shi za a gabatar da wanda ba shi ba (Kamar a ce sarki ne ko shugaban wurin da makamancinsu).
Saboda fadin Manzon Allah (Saww) “Kada wani mutum ya yi wa wani mutum limanci a wurin ikonsa, kada ya zauna a wurin zamansa a gidansa [Wurin zamansa, shi ne wurin da aka tanadarwa baqo don ya zauna], sai dai da izininsa” (Imamu Muslim ne ya rawaito shi).
Allah ya Taimake mu da Taimakonsa.
No comments:
Post a Comment