Wednesday, December 20, 2023
YADDA ABU ZAR GHIFARI(RADHIYALLAHU ANHU)YA KARƁI MUSULUNCI KASHI NA ƊAYA
YADDA ABU ZAR GHIFARI(RADHIYALLAHU ANHU)YA KARƁI MUSULUNCI KASHI NA ƊAYA
Abu Zar Ghifari (R.A) shahararre ne daga cikin Sahabbai, kuma ya yi suna wajen takawa da kuma ilminsa. Sayyadina Ali (R.A) ya sha cewar: 'Abu Zar ya sami wani irin ilmi, da sauran mutane suka kasa samu.'
A lokacin da ya samu labarin Manzancin Manzon Allah (S.A.Ws) a karo na farko, sai ya yi maza ya aika da kanensa domin ya tafi Makkah ya binciko masa mutumin da ake cewa shi Annabi ne, watau ana aiko masa da wahayi.
Ɗan-uwan nasa ya koma bayan da ya kammala binciken da ya kamata, kana ya nuna masa cewar, lallai Muhammad (S.A.Ws) mutum ne na kirki mai hali na gari, kuma hakika irin wahayin da yake samu mai ban al'ajabi ba sha'irori ba ne ko kuma sihiri.
To amma wannan rahoto da ya samu bai gamsar da shi ba sosai, don haka sai ya yanke shawarar tafiya Makkah, don ya binciko wa kansa gaskiyar lamarın. Da zuwansa Makkah, sai ya zarce kai tsaye zuwa Masallacin Ka'abah. To sai dai a lokacin, bai san wane ne Manzon Allah (S.A.Ws) ba, kuma yana ganin bai dace ba lokacin, ya ce zai tambayı wani game da shi.
A lokacin da dare ya fara yi, da Sayyadina Ali (R.A) ya hango shi, ya tabbatar cewar bako ne, don haka ba zai kyale shi ba, Tun da yake abu ne daman da Sahabbai suka riga suka saba da yinsa, watau kyautatawa ɗan hanya, da matalauta tare da baki. Don baka sai ya dauke shi suka tafi gıda tare Bai dai tambaye shi dalilin zuwansa Makkah ba, kana shi kuma Abu Zar bai yi subul da baka ba, ya fadi.
Da gari ya waye, sai ya sake komawa Baitullah inda ya zauna har zuwa ketowar magariba, ba tare da sanin ko wane ne Manzon Allah (S.A.Ws) ba. Alal Hakika kowa ya san ana ganawa Annabi da Sahabbansa wahala a Makkah, kuma kila shi yasa shi kansa Abu Zar, yana tsoron abin da zai iya biyowa sakamakon tambaya game da batun Manzon Allah (S.A.Ws) Sayyadına Ali (R.A) ya sake jansa zuwa gida, inda ya sake kwana a wurinsa, amma duk da haka bai yi katsalandan din tambayarsa dalilin zuwansa wannan birni.
To amma a dare na uku bayan ya ciyar da shi kuma ya shayar da shi kamar waɗannan ranaku na baya da suka wuce, sai ya tambaye shi cewa: Dan-uwa, me ya kawo ka wannan gari ne?"
Kafin Abu Zar ya ba Sayyidina Ali (R.A) ansa, sai da ya yi alkawari da shi akan cewa, lallai ya gaya masa gaskiya.
MU HAƊU A KASHI NA BIYU
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws)
✍️ Ahmad Musa
Sunday, December 17, 2023
BILAL (R.A) DA KUMA IRIN WAHALAR DA YA SHA KASHI NA ƊAYA
BILAL (R.A) DA KUMA IRIN WAHALAR DA YA SHA KASHI NA ƊAYA
Bilal (R.A) yana ɗaya daga cikin Sahabbban da suka fi shahara a matsayinsa na Ladanin Masallacin Annabi (S.A.Ws) Shi dai Bilal (R.A) mutumin Habasha ne, kuma bawan wani kafiri a Makkah.
Hakika ubangidansa bai ji daɗin yadda ya Musulunta ba. Saboda ganin haka ne ma yasa ya hasala inda ya yi ta azabtar da shi ba ji ba gani. Ummayah bin Khalf wanda babban makiyin Musulmluci ne, shi ne yake tilasta Bilal (R.A) da ya kwanta a tsakiyar rairayi mai zafi da tsakar rana, kana kuma sai ya samu katon dutse ya ɗora masa a kirjinsa, yadda ba zai iya motsa ko da hannunsa ba.
Daga nan kuma sai ya ce da shi: 'Ka rabu da Musulunci ko kuma in barka ka mutu a cikin wannan hali. Amma shi Bilal (R.A), duk da wannan wahala da ake bashi, sai ya kaɗa baki yake yi yana mai cewa 'Ahad' (Watau Allah Ɗayn ne) 'Ahad' (Allah Ɗaya ne) Idan dare kuma ya yi, sai ya yi ta tsula masa bulala.
Da wannan zane da aka yi masa a jikin nasa, washegari za'a sanya shi ya kwanta a tsakiyar rairayin mai zafi. Watau ko dai ya bar Musulunci ya huta da azaba, ko kuma ya bar shi ya mutu saboda wannan raunika da ya samu.
Su da kansu masu azabtar da Bilal (R.A) sukan gaji, don haka sai suyi canji (Watau Abu Jahal, Ummayah da sauran wasu kafiran) har kokawa suke don baiwa Bilal (R.A) horo mai tsanani.
MU HAƊU A KASHI NA BIYU
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws)
✍️Ahmad Musa
Ku shiga nan don karanta
👉👇
https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/yarjejeniyar-hudaibiya-da-kuma-labarin_15.html
Friday, December 15, 2023
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA UKU
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA UKU
A kashi na biyu mun tsaya a dai-dai inda Abu Basir yace "Don haka na kubuce musu da wannan dubarar, saboda tsoron su cilasta mini rabuwa da Addini na.'"
Manzon Allah (S.A.Ws) ya ce: 'Abu Basir mai tayar da zaune tsaye ne. Na yi gurin da zai yiwu a taimaka masa.' Abu Basir (R.A) ya fahimta daga wannan zancen cewa, ko yanzu Kuraishawa suka neme shi, za'a hannunta shi gare su. Don haka sai ya bar Madinah, ya tafi wani wuri cikin hamada, kusa da gabar teku.
Shima Abu Jandal (R.A) ya samu ya silale, yaje ya haɗu da shi a can. Bayan haka wasu Musulmin daga Makkah, suka samu suka tsere suka hadu acan. Kafin 'yan kwanaki kadan, Sahabban sun hadu, sun kafa 'yar rundunarsu, ta masu gudun Hijirah.
Ala tilas dai suka ci gaba da zaman wahala a cikin wannan yanki na Hamada, inda babu mutane ko abin da zasu rayu. To amma Tun da yake yarjejeniyar da aka kulla kusan bata shafe su ba, don haka sai suka zamewa Kuraishawa kamar kayar kifi a wuya, inda suka yi ta kaiwa matafiyansu hare-hare.
Don haka ala tilas wannan abu ya sanya Kuraishawa, sun rasa yadda za su yi. Saboda haka, suka tuntuɓi Manzon Allah (S.A.Ws) don ya tsoma baki, ya sa a mayar da waɗannan Sahabbai, kana matafiya su samu su rika wucewa lami lafiya.
An ce shi Abu Basir yana kan gadonsa, dab da lokacin da zai rasu, ya sadu da wasikar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam), inda ya yarje masa da ya koma Madinah da zama. An ce ya rasu a lokacin da yake rike da takardar Annabi a hannunsa.
Hakika babu abin da zaisa mutum ya canza imaninsa, idan har ya kasance imani ne na gaskiya. Bayan haka kuma, daman Allah Ta'ala Ya yi alkawarin taimakawa Musulmi na gaskiya.
Rubutu na gaba akan
BILAL (Radhiyallahu anhu) DA KUMA IRIN WAHALAR DA YA SHA.
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws)
✍️ Ahmad Musa
Ku shiga nan dan karanta kashi
👉👇
https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/yarjejeniyar-huda
Tuesday, December 12, 2023
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA BIYU
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA BIYU
A kashi na ɗaya mun tsaya a inda "Mahaifinsa Suhail, (wanda a lokacin bai Musulunta ba), shi ne jakadan Kuraishawa a wajen wannan yarjejeniya, ya kaiwa Abu Jandal (Radhiyallahu anhu) mari, inda kuma ya tsaya kai da fata cewar, lallai sai ya koma da shi Makkah."
Manzon Allah (S. A.Ws) ya yi ƙoƙarin tsoma baki kan batun, ya ce; Tun da ba a sa hannu akan yarjejeniyar ba, babu wata hujjar komawa da Abu jandal. To amma Suhail ya kafe, inda ya ki sauraren duk wata hujja da za'a bashi, ya ma nuna cewar, shi kam lallai ba zai bar ɗansa a baya hannun Musulmi ba, duk da cewar Manzon Allah (S.A.Ws) da kansa ya yi wannan roko. Don haka harma ya nuna kamar zai yi watsi da wannan yarajejeniyar.
Abu Jandal (R.A) ya ɗaga murya, ya dinga lissafa irin wahalhalun da yake sha a hannun Ƙuraishawa. Amma kuma abin ya ƙara ma Sahabbai suno, lokacinda Manzon Allah (S.A.Ws) ya yarda da a koma da shi. Duk da haka ya bashi haƙuri, yana mai cewa:
Kada ka yanke ƙauna, Ya Abu Jandal, bada jimawa ba, Allah Ta'ala zai kawo maka mafita.
Bayan an ƙulla wannan yarjejeniya kuma Manzon Allah (S.A.Ws) ya koma Madinah, sai kuma wani Musulmin shima daga Makkah, da ake kira Abu Basir (R.A) ya sulale zuwa Madinah, ya nemi mafaka a wurin Manzon Allah (S.A.Ws). Amma kuma yaki, don gudun karya ɗaya daga cikin sharuɗɗan sulhun, ya kuma hannuntashi ga mutane biyun da Ƙuraishawa suka aiko, don komawa da shi.
Shima, kamar Abu Jandal (R.A), ya neme shi da ya yi hakuri ya jira zuwan taimako daga Allah Ta'ala. Lokacinda Abu Basir da 'yan rakiyarsa suke kan hanyarsu ta komawa Makkah, Abu Basir ya kaɗa baki ya ce ma ɗaya daga cikinsu; 'Aboki! Amma takobinnan naka yana da ban sha'awa.' Wannan zancen ya burge mutumin, sai ya fitar da shi daga gidansa, ya ce: 'Haka ne, hakika takobin yana da kyau matuka, na gwada amfani da shi akan mutane masu yawa, karbi ka ga yadda yake.'
Cikin bacewar basira, wannan mutum ya mikawa Abu Basir (R.A) takobin, shi ko baiyi wata wata ba, ya gwada shi akan mai shi, ya kashe shi. Na biyun ya ranta cikin na kare, ya isa Madinah don kai kara ga Manzon Allah (S.A.Ws). Ana cikin haka Abu Basir (R.A) shi ma ya isa. Ya cewa Manzon Allah (S.A.Ws): 'Ya Rasulallah! (S.A.Ws), ka riga ka hannunta ni gare su can farko, ka cika sharuɗɗan sulhu. Ni, bai zama tilas a kaina ba. Don haka na ƙubuce musu da wannan dubarar, saboda ina tsoron su cilasta mini rabuwa da Addini na.'
MU HAƊU A KASHI NA UKU
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws)
✍️ AHMAD MUSA
👉👇Ku shiga nan don samun kashi na ɗaya
https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/yarjejeniyar-hudaibiya-da-kuma-labarin.html
Friday, December 8, 2023
TAMBAYA NA TARA (0009) SHIN MAI CIKI TANA YIN HAILA?
TAMBAYA NA TARA (0009) SHIN MAI CIKI TANA YIN HAILA?
Yawanci idan mace ta ɗau ciki jini yakan daina zuwa mata, Imamu Ahmad yana cewa (Mata suna gane samuwar ciki da yankewar jini) Idan mace mai ciki ta ga jini idan hakan ya kasance kafin haihuwa da kwana biyu ko uku kuma a tare da shi akwai ciwon haihuwa to wannan jinin haihuwa ne, idan kuma kafin haka ne da lokaci mai tsawo, ko kuma tsakaninsa da haihuwa ba yawa amma ba zafin haihuwa to wannan ba biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda hukunce- hukuncen haila ba za su shafe shi ba?
Anan Malamai sun yi saɓani: Abin da yake daidai shi ne jinin haila ne in dai ya zo a yadda ta saba yin jinin haila, saboda asali duk jinin da ya zowa mace ana ɗaukarsa a jinin haila, in dai ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma babu wani dalili a Alkur'ani ko a Sunna da zai hana shi ya zama haila. Wannan shi ne mazahabar Maliku da Shafi'i, kuma Baihaki ya hakaito hakan daga cikin maganganun Ahmad. Don karin bayani duba: Dima'uddabi'iyya shafi na 11.
Allah ne Mafi sani.
Don samun amsar tambaya na takwas ku shiga nan👉👇
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA ƊAYA
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA ƊAYA
Ashekarata shidda bayan Hijrahn Manzon Allah (S.A.Ws) tare da Sahabbansa, sun bar Madinah zuwa Makkah don yin Umrah, A lokacin da Ƙuraishawa suka samu labarin wannan zuwa nasu, sun yi ƙoƙarin hana shi shiga cikin Makkah duk da cewa aikin hajji yake shirin yi.
Don haka wannan abu ala tilas, tasa ya kafa sansani a Hudaibiyya. Sahabbansa su dubu daya da dari hudu (1400), sun (tsaya kai da fata cewar, lallai sai sun shiga Makkah, ko da za ta kaisu ga yin yaki ne. Amma ra'ayin Manzon Allah (S.A.Ws) a wannan lokaci ya sha bamban da nasu. Duk da cewar Sahabbansa shirye suke a gwabza yaki da su, maimakon haka ta faru, sai ma ya kulla yarjejeniya da Ƙuraishawa, kuma ya amince da dukkan sharuɗɗan da suka gicciya.
Wannan yarjejjeniya maras ma'ana a zahiri, wadda ta fi kyautatawa su Kuraishawa, ta yi matukar wahalar karba ga Sahabbai. Amma kuma cikakkar ɗa'arsu ga Manzon Allah (S.A.Ws) ta hana su hawa kujerar na ki a kan yarjejeniyar. Ko da jarumai irin su Sayyadina Umar (R.A) ala tilas, shima ya haƙura da irin shawarar da Annabi ya zartas.
Kamar yadda daya daga cikin ka'idodin wannan yarjejjeniya ya nuna; Mutanen da suka Musulunta a lokacin da ake kulla wannan yarjejeniyar, tilas ne a mayar da su hannun Kuraishawa. Amma su kuma Kuraishawan da suka gudu daga hannun Musulmi, ba za'a maida su ba.
Abu Jandal (R.A) wanda yake Musulmi ne a Makkah, Yana matukar shan wahala a hannun Kuraishawa. Kullun a ɗaure yake da sarkoki. Da ya sami labarin isowar Manzon Allah (S.A.Ws) Hudaibiyyah, ya samu ya kubuta, inda ya kurɗa har ya samu ya isa inda Musulmi suke, ana gab da rattaɓa hannu akan wannan yarjejjeniya. Mahaifinsa Suhail, (wanda a lokacin bai Musulunta ba), shi ne jakadan Kuraishawa a wajen wannan yarjejeniya, ya kaiwa Abu Jandal (R.A) mari, inda kuma ya tsaya kai da fata cewar, lallai sai ya koma da shi Makkah.
MU HAƊU A KASHI NA BIYU
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbi
✍️AHMAD MUSA
Ku shiga nan domin samun yadda Anas bin Nadr yayi shahada
👉👇
https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/shahadar-anas-bin-nadr-ra-kashi-na-biyu.html
Monday, December 4, 2023
SHAHADAR ANAS BIN NADR (R.A) KASHI NA BIYU
SHAHADAR ANAS BIN NADR (R.A) KASHI NA BIYU
A kashi na ɗaya mun tsaya a dai-dai inda
"Wannan umurni dai na Manzon Allah (S.A.Ws) kurum har zuwa lokacin da ake yin fada ne".
Don haka masu dawakai da suka hango babu wanda ke lura da baya, sai suka yunkuro a guje, inda suka samu suka kutsa, kana suka shammaci Musulmi ta baya, waɗanda suka dukufa wajen kwasar ganima. Ana cikin wannan hali ne fa, Anas (R.A) ya hango Sa'ad bin Ma'az (R.A) yana kokarin wucewa ta gabansa. Nan take ya yi masa tsawa, inda ya jawo hankalinsa yana mai cewa; 'Ya Sa'ad! Ina ka ke shirin zuwa? Na rantse da Allah Ta'ala, na jiyo kamshin Aljannah ya na kunnowa daga Dutsen Uhudu Ai kuwa faɗın haka keda wuya, sai ya yi kururuwa, inda ya yi tsalle, ya kutsa tsakiyar filin daga, aka yi ta ɗauki ba daɗi tare da shi, har sai da ya yi Shahadah. Bayan kammala yakin an yi daga-daga da jikinsa.
Inda aka yi ɗai-ɗai da shi. Wanda ta kai, sam babu wanda zai iya gane shi, sai kurum kanwarsa ce ta shaida shi, shima bayan da ta dubi yan yatsunsa. Irin rauninkan da aka yi masa wanda ya kama daga na kibbau zuwa na takubba, sun fi tamanin.
Don haka dai waɗanda suka yi jihadi fi sabilillah, tsakani da Allah, tare da juriya da hakuri, har kamshin Aljannah suke jiyowa tun daga nan duniya, kamar yadda wannan bawan Allah Anas (Radhiyallahu anhu) ya jiyo kamshin Aljannah
MU HAƊU A RUBUTU NA GABA AKAN
Yarjejeniyar Hudaibiyyah Da Kuma Labarin Abu Jandal Da Kuma Abu Basir (R.A).
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws)
✍️ Ahmad Musa
Sunday, December 3, 2023
TAMBAYA NA TAKWAS (0008) A WANI SHEKARU NE MATA SUKE FARA YIN HAILA DAKUMA SHEKARUN DA SUKE DAINAWA
TAMBAYA NA TAKWAS (0008) A WANI SHEKARU NE MATA SUKE FARA YIN HAILA DAKUMA SHEKARUN DA SUKE DAINAWA
Yawancin mata suna fara yin haila ne daga shekara 12-50 amma wani lokacin mace tana iya yin haila kafin shekara 12 ko kuma bayan shekara 50, wannan ya danganci yanayinta da kuma wurin da take zaune, da abincin da take ci.
Malamai sun yi saɓani: shin akwai wata shekara ta musamman da mace take fara haila ko kuma take dainawa, ta yadda jinin da ya sameta kafin wannan ko bayan wannan shekarun ba za'a kira shi jinin haila ba?
Darimi -Allah Ya yi masa rahama-ya ce bayan ya ambaci saɓanin da aka yi: "Wannan duk kuskure ne a wajena, domin abin lura shi ne samuwar jinin, don baka duk lokacin da aka samu jinin a cikin kowacce shekara ne ya wajaba a sanya shi ya žarna haila", abin da Darimi ya faɗa shi ne daidai saboda Allah da ManzonSa sun rataya hukunce hukuncen jinin haila ne da samuwarsa, ba su kuma iyakance wasu shekaru na müsamman ba, kamar yadda aya ta (222) a suratul bakara take nuni zuwa hakan, wannan yake nuna mana iyakance shi da lokaci na musamman yana bukatar dalili ne daga litttafi Allah ko daga Sunnar ManzonSa, ba'a kuma samu ba.
Don neman karin bayani duba: Dima'uɗɗabi'iyya shafi na :6
Allah ne Mafi sani
Kushiga nan domin samun amsar tambaya na 0007
👉👇
https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/tambaya-na-0007-mecece-hukuncin.html
Saturday, December 2, 2023
TAMBAYA NA (0007) MECECE HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BUKATA A BANDAKI ?
TAMBAYA NA (0007) MECECE HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BUKATA A BANDAKI ?
To Malamai sun yi saɓani akan wannan hukuncin, Abu- hanifa ya hana hakan, Malik ya tafi akan cewa mutukar a gida ne to babu laifi, saboda hadisin Abdullahi dan Umar wanda yake cewa: "Na hau ɗakin Hafsa sai na ga Annabi (S.A.Ws) yana biyan bukatarsa, yana fuskantar Sham ya kuma juyawa alkibla baya", kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (145).
Saidai abin da ya fi shi ne kar mutum ya fuskanci Alkibla, ko da a gida ne, saboda hadisin Abu-ayyub wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa: "Idan kuka zo yin bahaya to kada ku fuskanci alkibla kada kuma ku bata baya" Bukhari a hadisi mai lamba ta: (394) d aMuslim a hadisi lamba ta: (264),
Tabbas barin kallon alkibla yayin biyan bukata shi ne ya fi, saboda hadisin da ya gabata da kuma fita daga sabanin Malamai, don haka idan mutum zai gina masai a gidansa zai yi kyau ya kautar da ita daga alkibla. Don neman karin bayani duba: Bidayatul-mujtahid 1\115. Allah ne Mafi sani
TAMBAYA NA SHIDA (0006) YAYA IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA?
TAMBAYA NA SHIDA (0006) YAYA IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA?
To yan'uwa dole ne, sai ta yi jini uku kamar yadda Hanafiyya suka fada, ko kuma tsarki uku kamar yadda Malikiyya suka tafi akai, ko da kuwa duk shekara take yin haila sau daya, saboda Allah Madaukaki ya rataya idda ne da samuwar jini, kamar yadda yake cewa a cikin suratul Bakara aya ta : (228)
"Kuma matan da aka saka, to za su jira tsawon jinane uku" Don haka duk tsawon lokacin da za ta zauna to dole sai ta jira su, kamar yadda ayar take nunawa.
Allah ne Mafi sani.
TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA?
TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA?
Yan'uwa janaba wani hukunci ne da yake faruwa saboda ɗaya daga cikin abubuwa guda biyu :
1. Ko dai mutum ya yi mafarki kuma ya ga maniyyi,
2. Ko kuma mutum ya sadu da matarsa, duka waɗannan suna wajabta wanka, wankan janaba tana da siffofi guda biyu, duk wacce ka ɗauka ta yi:
I/. Siffar da ta fi kamala ita ce wacce ta zo a hadisin A'isha cewa Manzon Allah (S.A.Ws) idan ya zo wankan janaba yana farawa ne da wanke hannunsa, sannan sai ya wanke farjinsa da hannun hagu, sai kuma ya yi alwala amma ban da wanke kafa, sannan sai ya ɗebi ruwa sau uku ya zuba a gashinsa, bayan haka sai ya zuba a ragowar jikinsa, sannan sai ya wanke kafarsa. Bukari da Muslim.
II/. Akwai kuma siffa ta biyu wacce ta zo a hadisin Ummu-salama lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake siffanta mata wankan janaba, inda yake ce mata: "Ya isar miki ki zuba ruwa sau uku a kanki, sannan ki zuba a duka jikinki, mutukar kin yi haka to kin tsarkaka" Muslim ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (330). Allah ne Mafi sani.
SHAHADAR ANAS BIN NADR (Radhiyallahu anhu) KASHI NA ƊAYA
SHAHADAR ANAS BIN NADR (Radhiyallahu anhu) KASHI NA ƊAYA
Anas bin Nadr (R.A) yana daya daga cikin Sahabban da basu samu sukunin shiga yakin Badar ba. Ya yi matukar bakin cikin rashin samun wannan babbar dama, wadda kuma ita ce irinta ta farko, kuma mafi ɗaukaka daga dukkan jihadin da aka yi a cikin tarihın Addinin Musulunci.
Ya yi ta tunanin Allah Ta'ala Ya kawo wani yakin da zai samu damar bayar da tasa gudunmuwar, Tun da yake Allah Ta'ala bai sa ya samu sukunin shiga na Badar ba. Ai kuwa ba a dade ba, sai ga yakin Uhudu, watau shekara guda bayan na Badar.
Ya shiga sahun jerin gwanon askarawan Islama, tare da zuciya guda. Duk da cewar kafirai sun fi yawa wajen wannan yaki, amma duk da haka, Allah Ta'ala Yana taimakon Musulmi har zuwa bayan lokacin da wasu mutane suka yi katoɓara, sa'annan reshe ya juye da mujiya, Musulmi suka daina cin galaba.
A wannan lokaci dai, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya umurci wasu maharba 'yan baka su hamsin, da su rika lura da baya, domin kada abokan gaba da ke kan doki, su ɓullo masu kwatsam. An dai riga an ja kunnensu cewar, lallai kada su kuskura su motsa daga inda suke, har sai sun samu umurnin yin haka daga wajensa.
To amma a lokacin da suka ga Musulmi suna samun nasara, kana kafirai suna ta ranta a na kare, sai suka bar inda suke, da tsammanin cewar an gama yakin. Don haka suna ganin kamar wannan lokaci ne, na kwasar ganima. Shi jagoran 'yan bakan, ya yi iya matukar bakin kokarinsa don hana su wannan abu, don haka ya roke su da su ci gaba da tsayuwa wurin da suke, amma wadanda ma suka saurare shi basu fi mutane goma ba, inda suke ta jayayyar cewar, wannan umurni dai na Manzon Allah (S.A.Ws) kurum har zuwa lokacin da ake yin faɗa ne.
MU HAƊU A KASHI NA BIYU
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws)
✍️Ahmad Musa
BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU
BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU
A kashi na ɗaya mun tsaya a dai-dai inda "Mai makon ma su amsa wannan gayyata da ya yi musu", sai ma suka ki ko saurarensa. Kuma duk da cewar an san larabawa da karimci, maimakon gwada wannan karimci nasu sai suka shiga yi masa abin da bai kamata ace ya fito daga bakinsu ba, a matsayinsu na shugabanni.
In gajarce muku labari, fitowa ma fili suka yi ɓaro-ɓaro suka ce da shi, basa son ganinsa a wannan garin nasu. Da dai a kalla kamata ya yi ace Manzon Allah (S.A.Ws) ya samu kyakkyawan tarbo da kuma jawabi mai daɗaɗawa daga gare su Tun da yake sune shugabannin kabilarsu.
To amma maimakon haka, kurum sai ɗaya daga cikinsu ya kaɗa baki ya ce, 'Kai ne Allah Ya zaɓa a matsayin Annabi!' Wani kuma da ba'a ya ce: 'Duk yanzu Allah Ya rasa wanda zai zaɓa ya zama Annabinsa sai kai? Shi kuma na uku sai ya ce: 'Kai ni ba na ma son yin magana da kai, domin idan kai Annabi ne, yin gardama da kai jawo wa kai rigima ne, idan kuma kana kwaikwayon Annabawa ne, to don me zan ɓata lokaci na, ina magana da Annabin karya?"
Manzon Allah (S.A.Ws) wanda yake kamar dutse ne wajen dauriya da hakuri, bai ɓata rai ba, kan irin abin da waɗannan shugabannin suka yi masa. Maimakon haka, sai ya shiga ƙoƙarin saduwa da talakawan garin.
Amma duk cikinsu, babu wanda ya tsaya ya saurare shi. Maimakon haka ma sai suka nuna gara ma ya san inda dare ya yi masa, ya bar musu, garinsu. Lokacin da ya fahimci cewar duk irin abin da yake son nuna musu, ba za su fahimce shi ba, don haka sai ya yanke shawarar barin garin.
To, amma su ma kyale shi ya fita lami lafiya, basu yi haka ba. Maimakon haka, sai suka tara fitinannun yaran garin, inda suka fito titi suna yi masa ature, kana suna (faɗa masa rashin kunya da bakaken maganganu), wasu kuma na jifansa. Allah Sarki! An yi ta jifansa da duwatsu, ko ina jikinsa yayi jina-jina, yadda har takai, takalmansa suka manne da kafafunsa saboda jinin da ke zuba. Ya bar garin cikin wannnan zullumi na bakin ciki.
MU HAƊU A KASHI NA UKU
Allah yasa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws)
✍️*Ahmad Musa*
TAMBAYA NA HUƊU (0004) MENE NE ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA
TAMBAYA NA HUƊU (0004) MENE NE ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA
To yan'uwa akwai abubuwan da malamai suka yi bayani cewa, suna kawo nutsuwa a zuciya, ga su kamar haka:
1. Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar duk wata shirka da bidi'a da abin da yake kaiwa zuwa gare su.
2. Shiriya da hasken da Allah Yake jefawa a zuciyar bawa, wanda duk lokacin da aka rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci.
3. Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da ilimin mutum ya yalwata, zai samu jindadi a zuciyarsa.
4. Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin Allah "Wadanda suka yi imani, zuciyoyinsu suna nutsuwa da zikirin Allah" Suratu Arra'ad aya ta (28).
5. Kyautatawa bayin Allah, saboda duk mutumin da yake yin kyauta zai kasance cikin kwanciyar hankali, kamar yadda marowaci yake kasancewa cikin kunci.
6. Fitar da kyashi da hassada daga zuciya.
7. Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida.
8. Barin baccin da ba shi da amfani.
9. Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin karawa akan haka.
10. Rashin cakuduwa da mutane sai gwargwadon bukata. Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke jawo bakin ciki da damuwa da kuma kunci. Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad 2\22. Allah Ne Mafi sani.
Subscribe to:
Posts (Atom)