Friday, December 15, 2023

YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA UKU

YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA UKU A kashi na biyu mun tsaya a dai-dai inda Abu Basir yace "Don haka na kubuce musu da wannan dubarar, saboda tsoron su cilasta mini rabuwa da Addini na.'" Manzon Allah (S.A.Ws) ya ce: 'Abu Basir mai tayar da zaune tsaye ne. Na yi gurin da zai yiwu a taimaka masa.' Abu Basir (R.A) ya fahimta daga wannan zancen cewa, ko yanzu Kuraishawa suka neme shi, za'a hannunta shi gare su. Don haka sai ya bar Madinah, ya tafi wani wuri cikin hamada, kusa da gabar teku. Shima Abu Jandal (R.A) ya samu ya silale, yaje ya haɗu da shi a can. Bayan haka wasu Musulmin daga Makkah, suka samu suka tsere suka hadu acan. Kafin 'yan kwanaki kadan, Sahabban sun hadu, sun kafa 'yar rundunarsu, ta masu gudun Hijirah. Ala tilas dai suka ci gaba da zaman wahala a cikin wannan yanki na Hamada, inda babu mutane ko abin da zasu rayu. To amma Tun da yake yarjejeniyar da aka kulla kusan bata shafe su ba, don haka sai suka zamewa Kuraishawa kamar kayar kifi a wuya, inda suka yi ta kaiwa matafiyansu hare-hare. Don haka ala tilas wannan abu ya sanya Kuraishawa, sun rasa yadda za su yi. Saboda haka, suka tuntuɓi Manzon Allah (S.A.Ws) don ya tsoma baki, ya sa a mayar da waɗannan Sahabbai, kana matafiya su samu su rika wucewa lami lafiya.
An ce shi Abu Basir yana kan gadonsa, dab da lokacin da zai rasu, ya sadu da wasikar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam), inda ya yarje masa da ya koma Madinah da zama. An ce ya rasu a lokacin da yake rike da takardar Annabi a hannunsa. Hakika babu abin da zaisa mutum ya canza imaninsa, idan har ya kasance imani ne na gaskiya. Bayan haka kuma, daman Allah Ta'ala Ya yi alkawarin taimakawa Musulmi na gaskiya. Rubutu na gaba akan BILAL (Radhiyallahu anhu) DA KUMA IRIN WAHALAR DA YA SHA. Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️ Ahmad Musa Ku shiga nan dan karanta kashi 👉👇 https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/yarjejeniyar-huda

No comments:

Post a Comment