Saturday, December 2, 2023

TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA?

TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA? Yan'uwa janaba wani hukunci ne da yake faruwa saboda ɗaya daga cikin abubuwa guda biyu : 1. Ko dai mutum ya yi mafarki kuma ya ga maniyyi, 2. Ko kuma mutum ya sadu da matarsa, duka waɗannan suna wajabta wanka, wankan janaba tana da siffofi guda biyu, duk wacce ka ɗauka ta yi: I/. Siffar da ta fi kamala ita ce wacce ta zo a hadisin A'isha cewa Manzon Allah (S.A.Ws) idan ya zo wankan janaba yana farawa ne da wanke hannunsa, sannan sai ya wanke farjinsa da hannun hagu, sai kuma ya yi alwala amma ban da wanke kafa, sannan sai ya ɗebi ruwa sau uku ya zuba a gashinsa, bayan haka sai ya zuba a ragowar jikinsa, sannan sai ya wanke kafarsa. Bukari da Muslim.
II/. Akwai kuma siffa ta biyu wacce ta zo a hadisin Ummu-salama lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake siffanta mata wankan janaba, inda yake ce mata: "Ya isar miki ki zuba ruwa sau uku a kanki, sannan ki zuba a duka jikinki, mutukar kin yi haka to kin tsarkaka" Muslim ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (330). Allah ne Mafi sani.

No comments:

Post a Comment