Thursday, October 22, 2020

MABIYA JAGORAN ZAMAN LAFIYA NA DUNIYA SUNYI ABIN AYABA MUSU

Ibnul kayyim Yana cewa addini gaba dayansa kyawawan dabi'u ne, don haka duk wanda ya fika kyawawan dabi'u to ya fi ka addini.


Kyawawan dabi'u suna tsayuwa ne akan turaku guda hudu;


1. HAKURI; Wanda shi ne yake sanya mutum ya zama mai juriya da hadiye fushi, kamar yadda yake sanya tafiya sannu-a-hankali,

da rashin harzuka da kuma rashin gaggawa cikin lamura, kuma yana sanya kamewa daga cutar da wani. Kamar yadda mu yan arewa mukayi a wannan lokaci da aka gona dukiyar yan'uwanmu kuma aka ma wasu kisan gilla



2. KAMEWA: Wacce ita ce take kai mutum ga barin kaskantattun lamura, da abubuwan da ba su dace ba, ta kuma sanya shi ya zama mai kunya, wanda hakan zai sanya shi ya guji karya da rowa da annamimanci da cin naman mutane, da duk wani abu mara kyau. Kamar dai yadda aka harzuka mu domin mufita zanga-zanga amma muka kame


3. GWARZANTAKA : Wacce ita ce take kai mutum zuwa ga kare mutuncin kansa, da aikata abin da zai bashi kima, da yin kyauta ta yadda zai iya rabuwa da abin da yake so,


KUMA gwarzantaka wani abu ne da mutum zai iya rinjayar abokin gabarsa da shi, ta hanyar mallake zuciyarsa yayin fushi, kamar yadda ya zo a hadisi. Hakika mun nuna gwarzontaka a lokacin da ake cin zarafin yan'uwanmu a yankin kudu


4. Adalci; Wanda shi ne zai sanya shi ya daidaita dabi'unsa ta yadda za su zama tsaka-tsaki tsakanin ko-in-kula da wuce gona-da-iri. Kamar dai yadda muka tabbatar da ɗabianmu ta son zaman lafiya


Duk wasu dabi'u masu kyau da ka gani suna faruwa ne daga wadannan turakun guda hudu.


YA ALLAH KA BAMU KYAWAWAN DABI'U KUMA KAYI MANA MAGANIN ABINDA BAMA IYA YIWA KANMU.


https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

HANYA MAFI SAUKI DOMIN MAGANCE KO WACE IRIN FITINA

A Zamanin Manzon Allah (S.A.Ws) Kafirai Sun Takurawa Sahabannsa da Cin zarafi da kuma kuntatawa Da Yaga Irin Halin Kunci Da Takurawar da Makiya Kafirai Da Munafukan Sukeyi Musu, Sai Yayi Musu Huduba Yace Dasu Ya Ku Jama'ar Musulmi Kuyisani Cewa Wannan Halin Da Kuke Ciki Na Musifa Bakome Bane, kuma duk abubuwan nan da suke yi muku, na karshen zamani zasu fi Muni.


Ku sani Fitina Da Bala'i Suna Nan Tafe Akarshen Zamani Idan Zamanin Yazo Zakuga Fitina Da Musifu Da Bala'o'i Sun Kunno Kai Sai Ayi Ta Addu'a Sai Bala'in Da Musifa Sunyi Kamar Sun tafi Sai Wata Musifar Da Bala'in Su Kunno Kai Wanda Sukafi Nabaya hadari.



Manzon Allah (saww) Yaci gaba da cewa Awannan Lokacin Mutane Sunrude Kai Kace Bazasu Mutuba Sun Rasa Ya Zasuyi.


Sai Yace Shawarar Da Zan bawa Al'ummata Na Wannan Zamanin Itace Su rika tunanin Ya Zanyi In cika Da Imani, Yace Duk Wanda Yariki Ya Zanyi Incika Da Imani Shine Yayi Maganin Wannan Musifar Shine Ya Kaucewa Wannan Bala'in.


Amma ba ka tsaya kana tunanin Ya wannan Musibar zata kare ba.


Abin Nufi anan shine, ka rika tunanin cewa;


Yaya Zanyi In daina Giba (Idan har kana yi).


Yaya Zanyi in daina zina (Idan har kana yi).


Yaya Zanyi In daina Sata (Idan har kanayi).


Yaya Zanyi In daina Luwadi (Idan har kana yi).


Yaya Zanyi In daina Madigo (Idan har kina yi).


Wannan Shine Tunanin da Ya kamata Mutum ya tsaya yi ba Yaya wannan Bala'in Zai kwanta ba.


Ya Allah Ina Rokon ka dan Sunayen ka Tsalkakakku Masu daraja Wayanda Muka sani da Wayanda Bamu sani ba, Ya Allah kasa Mu cika da Imani, Ya Allah ka Tsare Mu da Azabar kabari, Ya Allah kasa Aljanna ta zamo makomarmu.


https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Thursday, October 8, 2020

2. TAKATACCEN TARIHIN RUKAYYAH (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)

 2. TAKATACCEN TARIHIN RUKAYYAH (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)


An haife ta shekaru uku bayan haihuwar Zainab (R.Ah), a lokacin da Manzon (S.A.Ws) yake da shekaru 33. Ta auri Uthbah dan Abu Lahab, Baffan Annabi (S.A.Ws). To amma a lokacin tun ba su fara zama tare ba aka saukar da Surah, Al-Lahab. Abu-Lahab ya kira 'ya'yansa Uthbah da Utaibah (wanda shi ne ya auri Ummu Kulthum), har wayau, wata ' yar ta Annabi (S.A.Ws), inda ya ce da su:

Idan ba sakin 'ya'yan Muhammadu ku ka yi ba, ba zan sake kallon fuskokin ku ba.


Sun saki matan nasu. Daga baya aka ci Makkah da yaki, Uthbah ya kar6i Musulunci. RUKAYYAH (R.Ah) bayan wannan saki ta auri Sayyadina Uthman (R.A). Mijin da matar sun yi Hijirah zuwa Habasha har sau biyu.


Tun lokacin da Annabi (S.A.Ws) ya shaida wa Sahabai cewar yana sa ran ya samu umarni daga wajen Allah Ta'ala na yin Hijirah zuwa Madinah, sai suka fara matsawa zuwa can tun kafin Annabi (S.A.Ws) ya yi Hijirasa. Uthman (R.A) da Rukayyah (R.Ah) sun kuma yi Hijirah zuwa Madinah kafin Annabi (S.A.Ws) ya isa garin.


A lokacin yakin Badr, Rukayyah ba ta da Lafiya (wanda ta cika sanadin wannan cuta). Don haka sai Annabi (S.A.Ws) ya bukaci shi Uthman (R.A) ya ci gaba da zama a Madinah don lura da ita. An samu labarin irin nasarar da aka samu a yakin Badr a can Madinah yayin da jama'a ke komowa daga jana'izar Rukayyah. Don haka da Annabi (S.A.Ws) bai samu damar halartar jana'izarta ba.


Rukayyah (R.Ah) ta haifi da a lokacin da suke Habasha. An sa masa suna Abdullah, kuma yana raye mahaifiyar ta rasu, ko da yake shima ya rasu a shekara ta 4, bayan Hijirah. A lokacin yana da shekara 6.


Insha Allahu rubutu na gaba akan Ummu Kulthum (R.Ah) yar Annabi (S.A.Ws) amma kafin nan zan daniyi rubutu akan dan Ahmad Deedat saboda ya samu rauni a safiyar yau.

Muna kuma rokon Allah Ta'ala ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen.

Saturday, October 3, 2020

YADDA TALLAFIN SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI ZAI GUDANA

✍️

Ahmad Musa

Rajista don Tallafin Biyan Kuɗin sashi na farko ya fara ne a ranar Litinin, 21 ga Satumba. Kamar yadda yake a Satumba 25, 2020, tashar aikace-aikacen ta rubuta kusan masu nema 342,500.


A halin yanzu, sashi na biyu na aikace-aikacen neman tallafin  ya fara a ranar 1 ga Oktoba (01/10/2020).


Tsarin da 'yan Nijeriya 9,009 za su amfana a kowace jiha da kuma Babban Birnin Tarayya Aikace-aikacen tallafi na biyan kuɗin ya shiga matakin tabbatarwa



Tsarin zai kasance acikin makonni Biyu a kowani kusurwa uku a duk fadin kasar


Kusurwa na farko za'a fara yin registan ne a ranar ɗaya ga watan Oktoba (01/10/2020) har zuwa Goma ga watan (10/10/2020) a Jihohin

1. FCT

2. Lagos

3. Ondo

4. Kaduna

5. Borno

6. Kano

7. Bauchi

8. Anambra

9. Abia

10. Ribas

11. Plateau

12. Delta


Kusurwa na BIYU za'a fara ne a ranar 19 ga watan Oktoba (19/10/2020) a Jihohin

13. Taraba

14. Adamawa

15. Bayelsa

16. EDO

17. Ogun

18. Ekiti

19. Katsina

20. Kebbi

21. Kogi

22. Kwara

23. Enugu

24. Ebonyi


Kusurwa na Uku kuma za'a fara a ranar 9 ga watan Nuwamba (09/11/2020) har zuwa 21 ga watan (21/11/2020) a Jihohin

25. Akwa-Ibom

26. Cross-River

27. Zamfara

28. Yobe

29. Sokoto

30. Nasarawa

31. Niger

32. Imo

33. Oyo

34. Osun

35. Jigawa

36. Gombe

37. Benue


Yadda zaka samu wannan TALLAFIN shine

Zaka  shiga wannan website ɗin da zai kaika har wurin direct, shine:👇

https://survivalfundapplication.com/auth/register

Ko kuma Main site din ko board din a👇

www.survivalfund.com

 kayi yi rijistan da Ministry of Youths and Sports. Idan kayi zasu tun-tube ka gabar ta email dinka ko ta lambar wayar idan za'a fara bayar da rance.

.

Abubuwan da ake bukata:

1. Active email, email wanda yake aiki.

2. Lambar waya.

3. Address.

4. Wadanda zasu cika, maza ko Mata, daga shekara 18 zuwa 35.

5. C.A.C registration number.

Amma idan baka da CAC Number, baka taba rijistan da hukumar ba, toh ka tsallake shi kawai, registration din zai yiwu ko baka da lambar CAC din.

.

Allah yasa duk wanda ya cika ya dace...

Allah ya taimaki wannan shugaban kasa namu mai kokari da son taimakawa al-umma