Ibnul kayyim Yana cewa addini gaba dayansa kyawawan dabi'u ne, don haka duk wanda ya fika kyawawan dabi'u to ya fi ka addini.
Kyawawan dabi'u suna tsayuwa ne akan turaku guda hudu;
1. HAKURI; Wanda shi ne yake sanya mutum ya zama mai juriya da hadiye fushi, kamar yadda yake sanya tafiya sannu-a-hankali,
da rashin harzuka da kuma rashin gaggawa cikin lamura, kuma yana sanya kamewa daga cutar da wani. Kamar yadda mu yan arewa mukayi a wannan lokaci da aka gona dukiyar yan'uwanmu kuma aka ma wasu kisan gilla
2. KAMEWA: Wacce ita ce take kai mutum ga barin kaskantattun lamura, da abubuwan da ba su dace ba, ta kuma sanya shi ya zama mai kunya, wanda hakan zai sanya shi ya guji karya da rowa da annamimanci da cin naman mutane, da duk wani abu mara kyau. Kamar dai yadda aka harzuka mu domin mufita zanga-zanga amma muka kame
3. GWARZANTAKA : Wacce ita ce take kai mutum zuwa ga kare mutuncin kansa, da aikata abin da zai bashi kima, da yin kyauta ta yadda zai iya rabuwa da abin da yake so,
KUMA gwarzantaka wani abu ne da mutum zai iya rinjayar abokin gabarsa da shi, ta hanyar mallake zuciyarsa yayin fushi, kamar yadda ya zo a hadisi. Hakika mun nuna gwarzontaka a lokacin da ake cin zarafin yan'uwanmu a yankin kudu
4. Adalci; Wanda shi ne zai sanya shi ya daidaita dabi'unsa ta yadda za su zama tsaka-tsaki tsakanin ko-in-kula da wuce gona-da-iri. Kamar dai yadda muka tabbatar da ɗabianmu ta son zaman lafiya
Duk wasu dabi'u masu kyau da ka gani suna faruwa ne daga wadannan turakun guda hudu.
YA ALLAH KA BAMU KYAWAWAN DABI'U KUMA KAYI MANA MAGANIN ABINDA BAMA IYA YIWA KANMU.
https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1