2. TAKATACCEN TARIHIN RUKAYYAH (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)
An haife ta shekaru uku bayan haihuwar Zainab (R.Ah), a lokacin da Manzon (S.A.Ws) yake da shekaru 33. Ta auri Uthbah dan Abu Lahab, Baffan Annabi (S.A.Ws). To amma a lokacin tun ba su fara zama tare ba aka saukar da Surah, Al-Lahab. Abu-Lahab ya kira 'ya'yansa Uthbah da Utaibah (wanda shi ne ya auri Ummu Kulthum), har wayau, wata ' yar ta Annabi (S.A.Ws), inda ya ce da su:
Idan ba sakin 'ya'yan Muhammadu ku ka yi ba, ba zan sake kallon fuskokin ku ba.
Sun saki matan nasu. Daga baya aka ci Makkah da yaki, Uthbah ya kar6i Musulunci. RUKAYYAH (R.Ah) bayan wannan saki ta auri Sayyadina Uthman (R.A). Mijin da matar sun yi Hijirah zuwa Habasha har sau biyu.
Tun lokacin da Annabi (S.A.Ws) ya shaida wa Sahabai cewar yana sa ran ya samu umarni daga wajen Allah Ta'ala na yin Hijirah zuwa Madinah, sai suka fara matsawa zuwa can tun kafin Annabi (S.A.Ws) ya yi Hijirasa. Uthman (R.A) da Rukayyah (R.Ah) sun kuma yi Hijirah zuwa Madinah kafin Annabi (S.A.Ws) ya isa garin.
A lokacin yakin Badr, Rukayyah ba ta da Lafiya (wanda ta cika sanadin wannan cuta). Don haka sai Annabi (S.A.Ws) ya bukaci shi Uthman (R.A) ya ci gaba da zama a Madinah don lura da ita. An samu labarin irin nasarar da aka samu a yakin Badr a can Madinah yayin da jama'a ke komowa daga jana'izar Rukayyah. Don haka da Annabi (S.A.Ws) bai samu damar halartar jana'izarta ba.
Rukayyah (R.Ah) ta haifi da a lokacin da suke Habasha. An sa masa suna Abdullah, kuma yana raye mahaifiyar ta rasu, ko da yake shima ya rasu a shekara ta 4, bayan Hijirah. A lokacin yana da shekara 6.
Insha Allahu rubutu na gaba akan Ummu Kulthum (R.Ah) yar Annabi (S.A.Ws) amma kafin nan zan daniyi rubutu akan dan Ahmad Deedat saboda ya samu rauni a safiyar yau.
Muna kuma rokon Allah Ta'ala ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen.
No comments:
Post a Comment