Wednesday, November 29, 2023

TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI?

TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI? Malam, menene bambanci tsakanin nifakul amali da i'itikaadi? To Malam: Nifaqul i'itikadi (wanda ake kudurcewa a zuciya) shi ne boye kafurci da kuma bayyana Musulunci, kamar yadda wasu mutane suka yi a zamanin Manzon Allah (S.A.Ws), duk wanda ya siffantu da wannan to ba musulmi ba ne, kamar yadda Allah ya yi bayani a suratul Munafikun. Amma nifakul-amali (munafuncin aiki) kuwa to shi ne wanda ya zo a cikin hadisin Abdullahi dan Amr inda Annabi (S.A.Ws) yake cewa: "Dabi'u guda hudu duk wanda suka kasance tare da shi, to ya zama cikakken munafiki, wanda kuma ya ke da daya daga cikinsu to yana da dabi'ar munafukai har sai ya bar ta: idan ya yi zance ya yi karya, idan aka amince masa ya ci amana, idan ya yi alkawari ya yi yaudara, idan ya yi husuma sai ya yi fajirci". Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: (34) da Muslim a hadisi mai lamba ta: (106). In mutum ya siffantu da daya daga cikin wadannan dabi'u guda hudu, to bai fita daga Musulunci ba, saidai yana da tawayar imani. Allah Ne Mafi sani.

Tuesday, November 28, 2023

BULAGORON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF: KASHI NA ƊAYA (01)

BULAGORON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF: KASHI NA ƊAYA (01) Bayan shekaru tara tun lokacin da Allah Ta'ala Ya fara saukan masa da wahayi, Manzon Allah (S.A.Ws), ya yi ta kokarin isar da sakon Allah Ta'ala ga mutanen Makkah, kuma ya dukufa don kokarin shiryarwa da kuma gyaran al'ummarsa. In ban da wasu 'yan kalilan da suka karbi sakon Musulunci, ko kuma suke taimaka masa ko da yake basu Musulunta ba, kusan sauran mutanen Makkah sun tashi ne haikan, wajen kokarin azabtar da Shi da kuma wulakanta Shi, tare da Sahabbansa.
Baffansa Abu Ɗalib, yana daya daga cikin mutanen kirki da suke agaza masa duk da cewar bai shiga Addinin Musulunci ba. Shekara guda bayan rasuwar Abu Ɗalib, sai Kuraishawa suka samu abin da suke so, inda suka kara tashi haikam wajen irin musgunawar da suke yi, ba tare da samun mai kwaban su ba. A can Ɗaif, wanda shi ne gari na biyu mafi girma a dukkan yankin Hijaz (watau kasar Makkah), akwai wata kabila da ake kira banu Thakif, wadanda suma masu fada a ji ne, kuma suna da 'yar dama. Don haka sai Manzon Allah (S.A.Ws) ya kama hanya zuwa garin na Ɗaif, domin kokarin shawo kansu, su shiga Musulunci, kana kuma su taimakawa Adddinin na Islama, tare da Musulmin da Kuraishawa ke ganawa ukuba, yadda a nan gaba kuma zai zama wata cibiya ko kuma sansanin yada Addinin Musulunci. Da isarsa Ɗaif, sai ya zarce (zuwa) (Jaula) ziyarar manyan hakiman garin, su uku, inda ya ziyarci ko wannensu ɗai-ɗai da ɗai-ɗai. Kana ya kira su don amsa wannan muhimmin sako na (Musulunci) da kuma bayar da tasu gudunmuwar ga Annabin Allah Ta'ala. Mai makon ma su amsa wannan gayyata da ya yi musu, MU HAƊU A KASHI NA BIYU Ya Allah kayi salati ga Annabin rahama Muhammad (S.A.Ws) *✍️*Ahmad Musa*

Tambaya NA BIYU (0002)SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) NE FARKON HALITTA?

Tambaya NA BIYU (0002)SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) NE FARKON HALITTA? Akwai hadisin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne farkon wanda aka fara halitta, sai dai hadisin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba (458), sun ce hadisin karya ne. Fadin cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ne farkon wanda aka halitta, ya sabawa Alkur'ani, ta bangarori da dama, ga wasu daga ciki: 1. Allah Ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad (S.A.Ws) mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah Ya tabbatar da cewa gabadaya mutane daga Annabi Adam aka same su, kun ga idan ka ce Annabi Muhammad shi ne farkon halitta hakan ya sabawa ayoyin Alkur'anin da suka yi bayanin hakan. 2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad (A.A.Ws), tun daga mahaifinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kun ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan. Zance mafi inganci shi ne : farkon abin da Allah Ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba (2653): "Allah Ya kaddara abubuwa kafin Ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa", Kun ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta, ba Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba. Allah Ne Mafi sani.

Monday, November 27, 2023

Tambaya NA ƊAYA (1) SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO?

Tambaya NA ƊAYA (1) SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO? Ya halatta macen da ba Musulma ba ta yiwa Musulma kitso, saboda a zance mafi inganci, al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace, shi ne daga guiwa zuwa cibiya, babu bambanci tsakanin kafira da Musulma a cikin haka, domin a zamanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Yahudawa mata suna shiga gidan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ba a samu suna yin shiga ta musamman ba, idan za su shigo, sai dai in kafirar ta na da wani sharri da ake jin tsoro, to wannan mace za ta iya suturta daga ita, sannan kuma mutukar akwai Musulma, to ita ta fi dacewa ayi hulda da ita. Allah Ne ma fi sani.