Wednesday, November 29, 2023
TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI?
TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI?
Malam, menene bambanci tsakanin nifakul amali da i'itikaadi? To Malam: Nifaqul i'itikadi (wanda ake kudurcewa a zuciya) shi ne boye kafurci da kuma bayyana Musulunci, kamar yadda wasu mutane suka yi a zamanin Manzon Allah (S.A.Ws), duk wanda ya siffantu da wannan to ba musulmi ba ne, kamar yadda Allah ya yi bayani a suratul Munafikun.
Amma nifakul-amali (munafuncin aiki) kuwa to shi ne wanda ya zo a cikin hadisin Abdullahi dan Amr inda Annabi (S.A.Ws) yake cewa: "Dabi'u guda hudu duk wanda suka kasance tare da shi, to ya zama cikakken munafiki, wanda kuma ya ke da daya daga cikinsu to yana da dabi'ar munafukai har sai ya bar ta: idan ya yi zance ya yi karya, idan aka amince masa ya ci amana, idan ya yi alkawari ya yi yaudara, idan ya yi husuma sai ya yi fajirci". Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: (34) da Muslim a hadisi mai lamba ta: (106). In mutum ya siffantu da daya daga cikin wadannan dabi'u guda hudu, to bai fita daga Musulunci ba, saidai yana da tawayar imani. Allah Ne Mafi sani.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment