Tuesday, November 28, 2023

Tambaya NA BIYU (0002)SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) NE FARKON HALITTA?

Tambaya NA BIYU (0002)SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) NE FARKON HALITTA? Akwai hadisin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne farkon wanda aka fara halitta, sai dai hadisin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba (458), sun ce hadisin karya ne. Fadin cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ne farkon wanda aka halitta, ya sabawa Alkur'ani, ta bangarori da dama, ga wasu daga ciki: 1. Allah Ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad (S.A.Ws) mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah Ya tabbatar da cewa gabadaya mutane daga Annabi Adam aka same su, kun ga idan ka ce Annabi Muhammad shi ne farkon halitta hakan ya sabawa ayoyin Alkur'anin da suka yi bayanin hakan. 2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad (A.A.Ws), tun daga mahaifinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kun ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan. Zance mafi inganci shi ne : farkon abin da Allah Ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba (2653): "Allah Ya kaddara abubuwa kafin Ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa", Kun ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta, ba Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba. Allah Ne Mafi sani.

No comments:

Post a Comment