BIRNIN DA ANNABI SULAIMAN(A.S)YAKE TAFIYA DA SHI ACIKIN ISKA.
Annabi sulaiman(A.S)yana da birni(gari)wanda yake tafiya a kansa an ginashi da 'kwarir girmansa kamu DUBU GOMA(10,000)acikinsa akwai tarago guda biyu, acikin kowane tarago akwai duk abinda miskinai suke bu'kata,tarago na 'kasa yafi 'karfe kauri da 'karfi karago na sama kuma yafi ruwa garai-garai da sirantaka, wanda yake cikinsa yana ganina abinda yake wajen taragon saboda garai-garai d'insa, acikinsa akwai wata 'kubba fara, akansa akwai wata tuta fara wacce take haskakawa askarawansa haske idan dare yayi.
KUJERAR ANNABI SULAIMAN(A.S)
Allah Ubangiji(S.W.T)yana cewa:-"MUNJEFA JIKI KAN GADONSA,"suratun sad aya ta 33.
An ruwaito cewa Annabi sulaiman(A.S)ya umarci shaid'anu da suyi masa kujera wacce zai ringa zama akai don yin hukunci wato Al'kalanci, ya umarcesu da suyi mata 'kira wacce idan wani mai 'Barna ko wani mai shaidar zur ya ganta za ta yi masa kwarjini, ya kuma tsorata.
Sai suka 'kera masa kujera da Hauran Giwa suka kuma kewaye ta da lu'u-lu'u da zubardaji da dai nau'i-nau'i na jauhari, suka kuma kewayeta da bishiyoyin dabino na zinare ganyanta na ya'kutai koraye, akan bishiyar dabino guda biyu akwai da'wisu na zinare, akan sauran bishiyoyin kuma akwai wani tsuntsu da ake kira Nasran shima anyishi da zinare sashinsu na kallon sashi suka kuma sanya wasu zakuna guda biyu agefen kujerar na zinare, akan kowane d'aya daga cikinsu akwai wani ginshi'ki na zubardaju kore, sun kuma yiwa wannan bishiyoyin ado da filawoyi na alfarma, sai suka sanyawa kowace fulawa narkakkun ya'kutu wanda zai ringa yiwa wannan gadon inuwa da kuma sauran bishiyoyin wannan kujera, sannan kuma akayi matattakala wacce idan Annabi sulaiman(A.S)yayi niyyar hawa sai ya d'ora 'kafarsa akan matattakalar ta 'kasa sai kurum tayi sama dashi har kan kujerar, kuma sai ya d'ora 'kafarsa akan matattakalar ta ringa juyawa da shi idan yayi nufin hutawa, su kuma wad'annan d'awisan da Nasran d'innan su ringa bud'e fuka fukansu, su kuma wad'annan zakuna guda biyu suna shimfida hannayensu suna dukan 'kasa da kunnuwansu, haka suke tayi akowace matattakala har sai Annabi sulaiman(A.S)ya zauna daidai akan kujerarsa ta mulki, sannan kuma sai wad'annan tsuntsaye guda biyu nakan dabino sai su fara zuba turaren muski da ambar agareshi, sannan Sai wata Kurciya ta zinare ta miko masa littafi daga cikin wasu ginshi'kai najikin kujerar sai ta bud'e masa littafin, sai ga fara karantawa mutane don yin hukunci a tsakaninsu, su kuma manya manyan mutanen bani isra'ila suna zaune akan wasu kujeru na zinare da azurfa a hagun sa, su dubu(1000)suna kewaye dashi, tsuntsaye sunyi musu inuwa, su kuma mutane suna zuwa gurinsa domin yayi musu hukunci, idan wani mai yin shaida yazo sai wannan kujera ta rabe biyu sai zakunan nan su fara dukan 'kasa sa kunnuwansu, su kuma tsuntsaye subud'e fuka fukansu, sai wanda ya zo shaidannan ya tsorat tsoro mai tsanani bazai shaida ba sai akan abinda ya tabbatar, babu zancen shaidar zur.
Wannan shine kad'an daga cikin abubuwan mamaki na kujerar Annabi sulaiman(A.S).
Lokacin da Allah(S.W.T)ya d'auki ran Annabi sulaiman(A.S)sai sarki BUKHUNASAR ya aika da a d'akko wanann kujerar to da aka d'akkota, sai yayi nufin ya ringa hawanta, amma sai dai bashi da ilmin sanin yanda take, lokacin da yayi niyyar ya hauta ya d'ora 'kafarsa akan matattakala ta farko sai wannan zakin ya daga hannunsa na dama yadaki 'kafarsa duka mai tsanani, sannan ya jefashi sama, bai gushe yana ta yin sama ba , har sai da ya mutu, ita kuma kujerar aka barta anan har saida wani sarki daga cikin sarakuna da ake kira ('Kaddashi 'Dan Saddad)ya ya'ki garin da wannan kujera take, ya kuma rusa mulki MUKHTANASAR d'in, sai ya maida kujerar Baitul Mukaddas, babu wani sarki da ya ta'ba zama akanta, sai kuma aka sata a 'kar'karshin wani fan dutse , sai ta 'buya, har yanzu babu wanda yasan inda take sai Allah, ALLAH SHINE MASANI.
ZANCI GABA INSHA ALLAHU.
RAMADHAN MUBARAK.
No comments:
Post a Comment