Tuesday, March 10, 2020

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...1O..

LABARIN BILKISU DA ALHUDA-HUDA.

     Malamai sukace, acikin labarun , Lokacin da  Annabi sulaiman(A.S)ya gama ginin Baitul Mu'kaddis, sai yayi nufin fita zuwa harami, sai ya tattara tawagarsa ta mutane da Aljanu da tsuntsaye da 'kwari, sun kai yawan Bataliya d'ari , sai iska ta d'aukesu zuwa harami, sai ya sauka anan yayi kwanaki iya yadda Allah yaso, har yayi aikin HAJJI , da sauran wasu ibadu, kuma ya gayawa mutanansa labarin zuwan Annabi Muhammad(S.A.W)sannan sai yayi nufin tafiya 'kasar yaman, sai ya fita daga makka da safe, ya nufi 'kasar yaman, su kai wani gari da ake SAN'A'A , a dai dai lokacin zawali( Wato lokacin sallar azahar)Tafiyar wata d'aya kenan,amma yayita a d'an wannan lokacin, sai ya ga wannan garin kyakkyawan garine, ga haske ga kuma kayan marmari 'kanshi sai tashi yake, sai ya sauka a wannan garin don yin sallah da kuma cin abincin rana, sai suka nemi ruwa basu samuba, Dama Alhuda-huda shine  d'an jagora gurin neman ruwa domin yana ganin ruwa a duk inda yake koda kuwa a 'kar'kashin 'kasane kamar yadda mutum yake kallon ruwa a kofi idan yana gabansa, idan ya hango ruwan sai ya tona, sai su kuma shaid'anu su tona su d'ebo, sai aka nemi Alhuda-huda baya nan.
       'Katadata ya rawaito cewa, Manzon Allah(S.A.W)yace, (NA HANEKU DA KASHE HUDAHUDA DOMIN SHINE JAGORA ANNABI SULAIMAN (A.S)GURIN RUWA) sai Annabi sulaiman(A.S)ya nemi Alhuda-huda Bai ganshiba, sai yayi masa wannan Al'kawarin na narko, shi kuma HUDAHUDA lokacin da yaga Annabi sulaiman(A.S)ya shagala da sauka a 'kasar SAN'A 'A, sai ya tashi sama domin ganin tsahon duniya da fad'inta, ya duba gabas da yamma, sai ya hango gonar BILKISU, sai ya sauka a cikinta , sai ya had'u da wani huda hudan wanda ake kiransa da suna (AFIR) shi kuma ALHUDA-HUDAN Annabi sulaiman(A.S)ana kiransa da suna(YA'AFUR)sai Afir yace da Ya'afur ina zaka! Kuma daga ina? Sai Ya'afur yace daga SHAM nake tareda sahibina sulaiman d'an Dauda(A.S)sai Afir yace waye sulaiman? Sai Ya'afur yace sarkin mutane da Aljanu da shaid'anu da 'kwari da dabbobi da iska,  sai Ya'afur yace to kai kuma daga ina? Sai Afir yace anan garin nake, sai Ya'afur yace waye sarkin garin? Sai Afir yace wata macece , sai yace ya sunanta? Sai Afir yace BILKISU, Amma fa sulaiman yana da mulki babba, sai dai bai kai na BILKISU ba, domin ita tana mulkin Yaman ne gaba d'aya, A 'k'kashinta akwai jagorori guda Dubu goma sha biyu(12,000)kuma kowa ne jagora yana da maya'ka dubu d'ari(100,000)ko zamu je kaga mulkinta? Sai yace ai kuma ina tsoro kada sulaiman ya nemeni lokacin sallah, idan yana bu'katar ruwa, sai Afir yace, ai Annabi sulaiman(A.S)Zai ji dad'i idan ka bashi labarinta, sai suka tafi domin yaje ya gani bayan ya gani, sai ya koma gurin Annabi sulaiman(A.S)dai dai lokacin sallar la'asar, to Dama wannan lokacin an nemi ruwa an rasa kuma an nemi Alhuda-huda baya nan.
      Amma wannan zance marar Tushe ne a malamai.
     A ruwayar d'an Abbas kuma cew  akayi, wani yanki na rana ya saraya akan Annabi sulaiman(A.S)sai ya duba gurin da Alhuda-huda yake bayanan sai ya yi kiran wannan tsuntsun mai suna Nasir ya tambaye shi cewa ina HUDAHUDA? Sai yace Ranka ya dad'e! Bansan inda yayi ba, kuma ban aike shi ko ina ba dayake shine shugaban tsuntsaye, sai Annabi sulaiman(A.S)yayi fushi sai yace , sai na azabtar da shi azabtarwa ko kuma in yankashi, ko kuma yazo min da wata hujja mai 'karfi, sai ga HUDAHUDA ya dawo, sai Nasir yace dashi ina kashiga yau? Ga shi Annabi sulaiman(A.S)Ya yi rantsuwa sai ya azabtar da kai,   sai HUDAHUDA yace kuma bai togace komaiba,  sai yace  a'a yace sai dai in kazo masa da hujja mai 'karfi,  sai ya ce yawwa, sai ya tashi ya tafi gurin Annabi sulaiman(A.S)yana zaune akan kujerarsa, lokacin da ALHUDA-HUDAN ya kusanci Annabi sulaiman(A.S)sai ya d'aga kansa sama ya shin fid'a fuka fukansa a 'kasa da jelarsa yana jansu domin nuna Tawaki'u ga Annabi sulaiman(A.S)Sai Annabi sulaiman yasa hannu akan ALHUDA-HUDAN sai ya funcika yana mai cewa ina kake ina nemanka, to zan azabtar da kai azaba mai tsanani, sai HUDAHUDA yace ya Annabin Allah kaji tsoran tsayiwarka agaban Allah, sai Annabi sulaiman(A.S)ya girgiza, sai ya yi masa rangwame, sannan sai Annabi sulaiman(A.S)yace ina ka tafi? Sai HUDAHUDA yace , kamar yadda Allah yake fad'a ackin Alkur'ani cikin suratun namli ayata 22 cewa:-

Zanci gaba insha Allahu

Musha ruwa lpy.

No comments:

Post a Comment