GININ ANNABI SULAIMAN(A.S)
ALLAH UBANGIJI(S.W.T)YA CE:-
TSARKI YA TABBATARWA WANDA YAYI TAFIYAR DARE DA BAWANSA(Annabi mai tsira da amincin Allah) a d'an yanki na dare, cikin mudda 'kan'ka nuwa daga masallaci mai Alfarma (MAKKA)izuwa masallaci mafi nisa(BAITUL MU'KADDAS), "An ambaceshi mafi nisa saboda nisansa daga gareshi" wanda mukayi Albarka Daura da shi "duk Annabawa masu tsira da Amincin Allah(S.W.T)ya yarda dasu, da 'koramu da 'ya'yan itatuwa don mu nuna masa mamakin ikonmu.
Ance Allah(S.W.T)ya yiwa Al'karyar da Baitul Mu'kaddas yake acikinta Albarka ta ruwan dad'i da 'ya'yan itatuwa da bishiyoyi iri-iri.
An rawaito cewa, Manzon Allah(S.A.W)Ya ce:-FAN BAITUL MU'KADDAS TA KASANCE AKAN WATA BASHIYAR DABINO DAGA CIKIN BISHIYOYIN BADINON ALJANNA, ITA KUMA WANNAN BISHIYAR DABINON TAKASANCE AKAN WATA KORAMA, DAGA CIKIN KORAMUN ALJANNA, A WAJAN WANNAN 'KORAMUN ANAN ASIYA "YAR MAZAHIM DA MARYAM "YAR IMRANA (R.T.A)SUKE TSARA KAYAN ADO NA MUTANE 'YAN ALJANNA RANAR ALKIYAMA" daga khakil d'an ma'adan daga ubaidata d'an samit.
Farkon ginin Baitul Mu'kaddas da kuma siffar ginin kamar yadda aka ambata.
Shine:-
Allah UBANGIJI(S.W.T)yayi albarka ga tsatson Annabi Ibrahim(A.S)ta wajen yawa har sun kasance basa 'kirguwa, a zamanin Annabi Dauda(A.S), Annabi Dauda(A.S)ya zauna acikinsu lokaci mai tsaho a 'kasar falasd'in, sai yaga suna 'karuwa adadinsu yana yawaita a kowace rana sai abin ya bashi mamaki, sai yayi nufin yasan yawansu,sai yayi unarni da a 'kidayasu, amma hakan bai yuwuba, sai Allah(S.W.T)yayi masa wahayi da cewa:- KASAN CEWA NA YIWA MAHAIFINKA IBRAHIM (A.S)AL'KAWARIN RANAR DANA UMARCE SHI DA YA YANKA 'DANSA, YAYJ HAKURI YA CIKA UMARNI NA , AKAN CEWA ZAN SA ALBARKA ACIKIN ZURIYYARSA, HAR SAI SUN KAI YAWAN ADADIN TAURARI, TA YADDA BAZA'A IYA 'KIDAYA ADADIN SUBA, SAI KAI KUMA KAYI NUFIN SANIN ADADINSU, TO KASANI BABU WANDA ZAI SAN ADADINSU SAI NI, AMMA ZAN JARRABESU DA 'KARANCIN YAWA DOMIN WANNAN MAMAKIN DA KAKE NA YAWANSU YA FAKU DAGA GAREKA.
Sai ALLAH(S.W.T)ya bawa bani Isra'ila za'bi ,akan ya jarrebesu da yinwa ko da fari na shekara uku, ko kuma ya sallad'a ma'kitansu akansu har tsahon wata uku, ko kuma ya sa musu mutuwa ta kwana uku, sai Annabi Dauda(A.S)ya basu labari da abinda Allah(S.W.T)yayi masa wahayi da kuma za'bin da ya basu, sai sukace ai kai ne mafi sani daga garemu, kaza'bar mana abinda yafi sau'ki, kayi duba sosai, amma kasan cewa bamu da ha'kuri wajen yunwa, kuma sallad'a ma'kiya Al'amarine mabayyani a garemu, idan dai babu makawa sai an jarrebemu to mutuwar tafi, domin a hannunsa take ba a hannun wanin saba, sai aka umarci Annabi Dauda(A.S)da ya gaya musu suyi shirin mutuwa, suyi wanka susa turare su kuma sa likkafani su warwatsu a gurin Baitul Mu'kaddas kafina gina shi, sai ya umarce su dasuyi kan-kan da kai ga Allah(S.W.T)ko ya ji'kansu, sai Allah(S.W.T)ya aiko musu da Annoba, sai kaga mutane dubunnai sun mutu a dare d'aya, wanda ba'asan adadin suba, ba'a daina binne wad'anda suka mutuba saboda yawansu sai bayan wata d'aya.
Lokacin da rana ta biyu ta kewayo sai Annabi Dauda(A.S)ya fad'i yana mai sujjada yana rokon Allah(S.W.T)akan ya yaye wa Bani Isra'ila wannan musibar, sai Allah (S.W.T)ya amshi addu'ansa, ya d'auke musu wannan Annobar suka daina mutuwa,sai Annabi Dauda(A.S)ya umarci Bani Isra'ila dasu godewa Allah saboda Baiwar da yayi musu, sai sukace dame zamu gode masa?sai yace ku gina masallaci a gurin da yayi muku Rahmarsa, saboda wad'anda za su zo bayanku su ringa tuna Ubangiji da ambatonsa, sai Annabi Dauda(A.S)ya fara shirin gina masallaci sai ga wani mutum Salihi talaka ya zo masa domin ya jarrebe shi akan cewa shin da IKHLASI za suyi wannan ginin?
ZANCI GABA INSHA ALLAHU.
JUMA@KAREEM
RAMADHAN MUBARAK.
No comments:
Post a Comment