Friday, April 3, 2020

TAMBAYA MAI MA'ANA KU TSAYA KU KARANTA

Nakasance inayin azumin litinin da alhamis. Sai ake cewa wai yanzu sha'aban yashigo Ramadan ya gabato wai bai halalta incigaba ba saidai inanjeyishi har bayan idi sallah incigaba shin malam hakane?

AMSA
*****
Watan Sha’aban wata ne da Manzon Allah (SAWW) yake yawaita azumin tadawwa’i a cikinsa fiye da kowane wata a bayan Ramadan. Kamar yadda
Uwar Muminai A’isha (Allah Ya yarda da ita da mahaifinta) ta ruwaito cewa “Manzon Allah (SAWW) ya kasance yana
azumi har mu ce ba ya shan ruwa, kuma in yana sha ruwa har mukan ce ba ya azumi.

Amma ban ga Manzon Allah (SAWW) ya cika wata yana azumi ba, sai na watan Ramadan, kuma ban gan shi yana yawaita azumi ba kamar
yadda yake yi a watan Sha’aban.” (Buhari da Muslim).

Ibn Hajar ya ce,"Wannan Hadisi dalili ne kan falalar azumin Sha’aban." (Fathul Bari Mujalladi na 4 shafi na 253).

A cikin Lada’iful Ma’arif shafi na 247 Ibn Rajab ya ce “Amma azumin Manzon Allah (SAWW) a mafi shaharar Sunnah ya ksance yana azumtar Sha’aban fiye da kowane wata.” Yayin da San’ani ya ce "A cikinsa (Hadisin) akwai dalilin cewa ya kebance Sha’aban da yin azumi fiye da waninsa.” (Subulus
Salam, Mujalladi na 2 shafi na 342).

Kuma Sayyada A'isha (RA) ta ce “Watan da Manzon Alla (SAWW) ya fi so ya azumnta a cikin watanni shi ne Sha’aban, sannan ya sadar da shi da Ramadan.” Ahmad ya ruwaito shi a Musnad, kuma Abu Dawuda da Nisa’i sun ruwaito shi, kuma Hakim ya ce Sahihi ne a bisa sharadin Buhari da
Muslim, yayin da Albani ya inganta shi a cikin Abu Dawud. Hadisi na 2124.

Akwai ruwayoyi da dama kan falalar yawaita azumi a watan Sha’aban, kuma malamai sun karfafa haka tare da yin maganganu a kai. Ni dai ban san in da akace baabu kyau azumtar SHA'ABAN ba.

JAN HANKALIN DA ZANYI ANAN

• Jama'a Kowane bangare na rayuwa ana lura da abin da ake kira da harshen nasara “Specialization” don sauraro
da auna mai magana a bangaren, da kuma bashi kima ko rashin kima.

Likita da cuta.. lawyer bangaren
kare tuhuma da sauransu…
'Politician' abin da siyasa…
“Engineer”… da dai sauran
bangarori na rayuwa.
To shin bangaren da ya shafi addini ba shi da irin wannan
“Specialization” ne? sai ka ga…

kowa yana tsoma baki game da abin da ya shafi addini? Kowa yakan yi fatawa sannan ya dage bisa matsayinsa, ko da kuwa ba zai iya karanto maka aya guda ta kur’ani daidai ba? ballanta ma a ce ya san harshen da wannan shari’a ta sauka da shi?

Magabata masu dimbin sani na
shari'a har Alla-alla suke idan a ka samu mas’ala sabuwa ya zamanto wani daga cikinsu ya hutasshe amsarta, saboda girman hadarin gaggawa cikin bayar da fatawa.

A kan hukuncin shiga garin da
annoba ya fadawa, sai da Umar
(RA) ya tara kusan dukkan
Sahabbai da suke tare da shi, ko akwai wanda ya taba jin
hukuncinsa, duk suka ce ba su da masaniyar hakan, sai daga can karshe ne, aka samu AbdurRahman bn Auf (RA) ya yi bayanin hukuncin…

JAMA’A LALLAI MU YI HATTARA! MU RIKA MAGANAR DA MUKE DA MASANIYA BISA HUJJA DA DALILI!

ABIN DA BA MU SANI BA MU CE
ALLAH SHINE MASANI.

*WALLAHU A'ALAM*

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

No comments:

Post a Comment