Ali dan Abi dalibi ya bada wani labari da yake nuna makircin shaidan da yake shiryawa a hankali har ya rugurguza mana imani.
Wannan labari akan wani mutum ne mai imani da yawan aiyukan addini, da yake zaune nesa da garinsu domin kuwa garin
mamaye yake da alfasha.
A cikin wannan garin akwai wasu mazaje su uku ‘yan uwan juna da suke kula da
kanwarsu wadda ita ma babu ruwanta.
Wata rana sai sukayi shawara su dauke ta su kaita can wajen gari inda wancan bawan-Allah yake zaune ko ta kubuta
daga munanan dabi’un da suka mamaye garin.
Daga farko wannan bawan-Allah ya ki don kuwa yasan hadarin kadaituwa da budurwar da ba matarsa ba.
Amma sai nan da nan shaidan ya rada masa “kaga, kai ne mutumin da yafi kowa tsoron Allah a wannan waje.
Idan kaki karbar wannan yarinya har ta koma wancan garin, lallai da sannu zata lalace.” Don haka sai ya karbe ta.
Sai ya kar beta.
Da farko yana bar mata abinci a bakin kofar dakin ya tafi abinsa, sai shaidan ya dawo ya kuma rada masa cewa” ta yaya kasan cewa hakika tana samun abincin?
Zai fi ka rinka dakatawa kadan kana
tabbatar da cewa tana samun abincin ba wata dabbar bace ke cinyewa.” Saboda haka sai ya rinka tsayawa.
Bayan wani dan lokaci sai shaidan ya rada masa “kaga ga yarinya mai hazaka a kulle a gidan nan kai kuma gaka da irin wannan tarin ilimi.
Ba zai fi ba ace ka fara koyar da ita in yaso zamanta anan baya zama hasara ba gaba daya?”.
To daga nan fa sai ya fara koyar da ita darussa.
Da farko yana barin wani abu a tsakaninsu saboda gudun fitina, amma sai shaidan ya bashi shawara a zuci cewa ya kamata ya rinka kallon idanunta yayin karatun domin ya tabbatar da cewa tana koyon, ba barci kawai take yi ba abinta.
Daga nan fa shaidan yasan cewa tarkon nasa ya danu. A hankali a hankali har sai da mutumin nan yayi wa yarinya ciki.
Bayan hakan ya auku sai ya dawo ya rada masa cewa ”to fa kai ne mafi imani a garin nan.
Yanzu ko mutuncin ka ya gama yawo (in
har aka gano wannan katobara).
Abin da yafi sai ka kashe ta ka binne, in yaso sai ka cewa ‘yan uwanta ‘rashin lafiya tayi, kuma duk da kokarin ka na neman magani sai da cutar ta kashe ta’.
Wannan tabbas zai fi wancan abin kunyar”. Haka kuwa ya yi.
Da ‘yan uwanta suka zo duba ta, mutumin har da hawaye, yana basu labarin yadda cuta ta kamata, da irin kokarin da yayi na magani har ta mutu.
Babu wata jayayya suka yarda, don kuwa kowa ya san shi mutumin kirki ne.
A ranar da daddare duk su ukun sukayi mafarki cewa wannan mutumin ne ya kashe musu ‘yar uwa ya binne a wani wuri.
Da safe sukayi ta mamaki da ta’ajabi ga yadda duk su ukun sukayi mafarki iri daya, sai suka yi shawara da su je wannan wuri da suka gani a mafarki su tone.
Ai kuwa sai ga gawar yarinya har da juna biyu. Suka kamo wannan mutum suka tafi da shi cikin gari gaban jama’a.
Mutane suna can suna shawarwarin yadda za’a yi da shi sai shaidan ya zo masa ya nemi mutumin da yayi masa sujjada inyaso shi kuma zai fitar da shi daga wannan bala’i.
Da mutumin ya ga ba mafita sai ya yarda kuma ya aikata hakan (wal iyazu billahi).
Daga nan shaidan ya bace ya rabu dashi ya barshi a cikin masifa da halin da na sani.
Haka kuma wato shaidan bazai taba hakura ba har sai ya ga mutum ya cika.
Ya 'Yan Uwa kunji Fa Makircin Shaidan akan mu....Ya Allah ka tsare mu da Shaidan Alfarmar Annabi (S.A.Ws)
https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1
No comments:
Post a Comment