Coronavirus - wanda aka sani da COVID-19 - yana yaduwa daga mai cutar zuwa mara cutan ta hanyar shagar numfashi
Coronavirus shine cuta mafi saukin yaduwa cikin hanzari ta shagar numfashi, tari, da kuma cudanya da mai cutar kamar musayan hanu ko shafar fatar jikinshi da sauransu.
Cutar CORONOVIRUS yana iya kai kwana goma sha huɗu kafin ya fara bayyana a jikin ɗan Adam
A cewar WHO, coronaviruses dangi ne na ƙwayoyin cuta waɗanda ke haifar da cututtukan da ke kama da mura na yau da kullun zuwa ga mafi tsananin cututtuka irin su ciwo mai saurin kamuwa da sanyin jiki (SARS) da kuma cututtukan da ke addabar yankin shagar numfashi (MERS).
Menene alamu?
A cewar WHO, alamun kamuwa da cuta sun hada da zazzabi, tari, gazawar numfashi da kuma wahalar numfashi.
Sa'annan zai iya haifar da ciwon huhu, gazawar ƙwayoyin cuta da yawa har ma da mutuwa.
Game da kare kai daga kamuwa da kwayar cutar, kwararru sun yarda cewa yana da mahimmanci ku wanke hannayenku akai-akai kuma tare da sabulu, Sa'annan a lokacinda kake tari ko amai ka rufe fuskarka da wani abu ko da dudduniyar hanunka ka ziyarci likita idan kana da alamun cutar; da kuma guje wa hulɗa kai tsaye tare da dabbobi masu rai a wuraren da abin ya shafa.
Annabi (S.A.Ws) yace: "Idan wata musiba tasamu mumini sannan yayi istirja'i wato yace, 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un',sannan kuma ya hada da wannan addu'ar yace: "Ya Allah Kabani lada akan wannan musiba data sameni, Ka bani abinda yafi alheri daga wanda na rasa." Idan mutum yayi haka Allah (Swt) zai amsa masa addu'arsa.
Muna rokon Allah ya kare mu da kariyarsa
https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1
No comments:
Post a Comment