Sai Allah(S.W.T)Ya umarci Annabi sulaiman(A.S)da ya sauka yayi sallah acikinsa, kuma ya kusance shi da wani abin kusanta, sai Annabi sulaiman(A.S)ya aikata haka, ance Annabi sulaiman(A.S)ya yanka ra'kuma dubi biyar, da Bajimayan shanu dubu biyar,da akuyoyi dubu ashirin, a daf da ka'aba ,sai Annabi sulaiman(A.S)ya gaya wa wasu manya daga cikin mutanansa cewa, wannan gurin wani Annabi Balarabe zai fito daga gareshi, za'a bashi taimako da nasara ga duk wanda yayi taurin kai agareshi, kuma takobi zata kasance a wuyan duk wanda ya sa'ba masa, kuma kwarjininsa zai kai musalin tafiyar wata guda, wanda yake a kusa da wanda yake a nesa duk d'aya ne a gurinsa, baya jin tsoran zargin mai zargi acikin bin Ubangiji, Aljanna ta tabbataga wanda ya riskeshi kuma ya gasgatashi, sai suka ce tsakaninmu da shi zai shekara nawa ya kai Annabin Allah? sai yace zai kusa shekara dubu(1000).
Sai Annabi sulaiman(A.S)ya cigaba da tafiya har ya isa wani kwari da ake kira (WADIS-SADID)sannan kuma ya 'karasa kwarin wannan tururuwar wanda shima ake kiransa(WADIN NAMLI)sai wannan tururuwa ta tashi tana tafiya tana d'an rangaji, ya kasance girmanta kamar girman kura , ma'abociyar fukafukai guda biyu.
Malamai sunyi sa'bani a kan sunanta wasu suka ce sunanta (DAKHIYA)wasu kuma sukace sunanta(KHIRMA), sai tayi kiran 'yan uwanta tururuwai saboda rundunar Annabi sukaiman(A.S)da ta gani, shine fad'in Ubangiji(S.W.T)cewa:-" YA KU JAMA'AR TURURUWAI! KU SHIGA GIDAJANKU KADA SULAIMAN DA RUNDUNONINSA SU KARKARYA KU, A HALIN SU BA SU SANI BA." suratun namli.
Dama kamar yadda muka fad'a cewa babu wata halitta da zatayi magana face sai iska ta dakkota ta kawo wa Annabi sulaiman(A.S), aka ce Annabi sulaiman(A.S)yaji maganar wanann tururuwar misalin tsawon mil uku(3-m), sai Annabi sulaiman(A.S)yayi murmushi saboda jin maganar wannan Tururuwar, sai yace Ubangijina ka cusa min in godewa ni'imarki wacce ka ni'imta ta gareni da kuma mahaifana guda biyu, kuma in aikata aiki na 'kwarai, wanda kake yarda da shi kuma ka shigar dani rahamarka acikin bayinka managarta.
Haka tsarin maganarsa tazo acikin Alkur'ani mai girma cikin suratun Namli aya ta 19. Awasu sauran 'kissa kuma akace, Annabi sulaiman(A.S)lokacin da yaji zancen wannan tururuwar sai ya sakko zuwa gareta, sai yace; azo da ita, sai aka zo da ita, sai yace da ita, saboda me wad'annan Tururuwan suka tsorata sunji ance ni azzalimine? Saboda me kikace kada sulaiman da rundunarsa su karkaryaku? Sai Tururuwar tace ya Annabin Allah bakaji a cikin maganata nace, "A HALIN BAKU SANI BA." Kuma duk da cewa na san banyi nufin karkaryawa na jikiba ina nufin karkaryawa na rai, saboda naji tsoro kada suyi burin abinda Allah yabaka, sai su fitinu su kuma shagala da kallonka akan TASBIHIN DA SUKEYI.
Sai Annabi sulaiman(A.S)yace wa'azantar dani yake Tururuwa, sai Tururuwa tace kasan ko saboda me ake kiran sunan mahaifinka da DAUDA? Sai yace a'a sai tace da shi ana kiransa da Dauda saboda yayi maganin raunin da zuciyarsa take dashi, sai ta kuma cewa, Shin kasan ko saboda me ake kiranka da sulaiman? Sai yace a'a sai tace saboda kai ku'butaccene acikin abin da aka baka, saboda ku'butar zuciyarka, kuma ha'k'kine a gareka ka had'u da mahaifinka Dauda, sannan sai ta kuma cewa kasan ko saboda me Allah (S.W.T)ya hore maka iska? Sai yace a'a sai tace domin duniya iskace, sai Annabi sulaiman(A.S)yayi murmushi saboda maganarta, yana mai mamaki, shine wannan addu'ar wacce muka fad'a abaya.
Nana Maimuna(R.A)ta bada labarin cewa Manzon Allah(S.A.W)ya hana a kashe masu tafiya akan 'kasa guda hud'u 4 daga cikin kwari da tsuntsaye, acikinsu akwai Tururuwa.
Yana daga cikin abinda Allah(S.W.T)ya hore wa Annabi sulaiman(A.S)Horewa dayayi masa ta mutane da Aljanu da Tsuntsaye da 'kwari da shaid'anu sunayi masa aiki na duk abinda yaga dama, shine fadin Ubangiji(S.W.T)cewa:-
"KUMA DAGA ALJANNU(MUKA HORE MASA)WANDA DA SUKE AIKI NAN GAMA GARESHI DA IZNIN UBANGIJI WANDA YA KARKATA DAGA CIKINSU, DAGA UMARNINMU SAI MU 'DAN'DANA MASA DAGA AZABAR SA'IRA"suratun saba'i aya ta (12).
Haka Allah (S.W.T)ya wakilta wani mala'ika, wanda a hannunsa akwai wata bulala ta wuta, duk wanda Ya'ki bin umarnin Anmabi sulaiman(A.S)daga acikin Aljanu, sai ya dokeshi da ita nan da nan ya'kone.
Daga cikin Aljanu akwai wad'anda suke nutso cikin ruwa, suke fito masa da nau'i nau'i na ma'adanai kamar lu'u lu'u da zubarjadi da ya'kutai, wad'annan Aljanu sune farkon wad'anda suka fara irin wannan aikin.
Zanci gaba insha Allahu
Musha ruwa lpy.
No comments:
Post a Comment