Lokacin da wannan jakada ya zo wa Annabi sulaiman(A.S) mabiyansa suna tare da shi da hadiya a tare dasu, sai Annabi sulaiman(A.S)Yace shin zaku 'kare ni da dukiya, bayan abin da Allah(S.W.T)ya bani ? Na Annabta da mulki shine mafifici daga abinda ya baku na duniya, kai bari! Ku dai kuna farin ciki ne da kyautarku saboda al'faharin ku da tarkace-tarkacenku, ka koma da abinda ka zo da shi na hadiya, lallai zamu zo musu da runduna wadda ba su da iko da ita, kuma lallai zamu fisshe su daga garinsu birnin saba'i, kuma zamu fisshe su in basu zo min suna masu mi'ka wuyaba.
Lokacin da jakada ya koma musu da wannan kyautar sai ta sanya gadonta cikin 'kofa bakwai7 daga cikin katangar gidanta, gidan nata kuma yana cikin gidaje bakwai7, ta kulle 'kofofin ta sanya masu tsaro, sannan kuma tayi shirin tawowa gurin Annabi sulaiman(A.S)Dan taga abinda zai umarceta da shi, sai ta maraito acikin makwayo dubu goma sha biyu, ko wamne makwayo dubbai suna tare da shi, har izuwa kusa da Annabi sulaiman(A.S)da mil uku (3-m) , sai Annabi sulaiman(A.S)ya yi hashashe da ita , sai yace yaku wad'annan jama'a wanene zai zo min da gadonta tun kafin su zo min suna masu mi'ka wuya, sai wani gwarzo daga Aljanu, wato mai tsananin 'karfi yce ni zan zo maka da shi kafin ka ta shi daga mazaunin shari'arka, (wato daga safiya zuwa rabin yini)ha'ki'ka ni mai 'karfi ne kuma amintacce ne ni ga abinda yake cikin gadon na jauharori da makamantansu, sai Annabi sulaiman(A.S)Yace ina son mafi sauri daga haka, sai wani wanda yasan ilimin littafi ya ce ni zan zo maka da shi kafin idonka ya koma gareka idan kayi duba da shi izuwa wani abu, sai ya subi sama, yana dawo da idon 'kasa sai ya ganshi a gabansa, lokacin da Annabi sulaiman(A.S)ya ga wannan gadon a gabansa sai yace wannan falalar Ubangiji ce don ya jarrabe ni zan gode masa ko zan butulce masa, wanda ya godewa ni'imar Allah, to tabbas ya gode dan kansa, domin sakamakon godiyar nan nasa ne, To tabbas Ubangiji mawadaci ne ga buran godiyar sa, kuma mai karamane da Baiwa a bisa wanda ta butulce masa.
Sai Annabi sulaiman(A.S)yace ku jirkita gadonta, zuwa halin da bazata ganeshi ba, mu gani zata ganeshin? Domin jarraba hankalinta, lokacin da ta zo sai akace, shin kamar haka gadonki yake? Sai tace kai kace shine kamar yadda suka shigar mata da kwatance, sai Annabi sulaiman(A.S)ya lura da cewa lallai tana da sani da basira, an bamu ilmi tun ga banta, mun kasance masu mika wuya, ya fad'i hakane don nuna godiya ga Allah, abinda kuma take bautawa ba Allah ba,ya tare ta ga Bautar Allah(S.W.T) ha'ki'ka ita ta kasance daga mutane kafirai.
Lokacin da ta tsaya gurin Annabi sulaiman(A.S)Sai aka ce da ita wannan rufi , rufine na gilas fari ruwan dad'i yake kwarara a 'kar'kashisa, akwai kifi da kwado da dabbobin ruwa, Annabi sulaiman(A.S)ya zuba su, lokacin da tagani sai ta zaci kunzomeman ruwa ne, sai ta yaye 'kafafuwanta guda biyu domin tsallaka ruwan, Annabi sulaiman(A.S)yana kan gadonsa gana kallonta, sai yaga 'kafafuwanta kyawawa, sai yace mata wannan rufi ne mai santsi na kaskon 'karau, sai ta ce Ubangiji ha'ki'ka na zalinci kaina da bautar waninka na mika wuya tare da Annabi sulaiman ga Allah Ubangijin Talikai.
Sai ta nemi ya aure ta sai ya 'ki saboda gashin 'kafarta, sai shaid'anu sukayi, masa nur wato farar 'kasa, sai ya kawar da gashin, sai ya aure ta ya tabbatar da ita akan mulkinta, ya kasance yana ziyartarta sau d'aya a wata yana zama a wajanta kwana uku.
Mulkinta ya 'kare da 'karewar mulkin Annabi sulaiman(A.S), An ruwaito cewa An khalifantar da shi gana d'an shekara shia uku(13), ya rasu kuma yana d'an shekara hamsin da uku(53).
WAFATIN ANNABI SULAIMAN(A.S)..
.ZANI GABA INSHA ALLAHU..
No comments:
Post a Comment