Idan mutum ya yi NAZARIN wahalar da IYAYE suka sha wajen tashinsa, da daure ma kurciyarsa har zuwa sadda zai yi hankali shi kadai ya isa ya nuna masa
girman hakkin IYAYE a kan sa.
To, ina ga kuma in mun koma ga alhakin uwa na daukar ciki wata tara tsakanin lafiya da ciwo, laulayi da haraswa, da kyamar abinci da raunin jiki da nauyin ciki har zuwa ga nakuda wadda wata 'yar karamar lahira ce mata suke zuwa a mafi
yawan lokuta!
Annabi (saww) Ya nuna mana Muhimmancin Iyaye a hadisai da dama musamman ita Uwa.
YA DAN UWA/'YAR UWA musulmi/ma
Mu gode wa Allah da ya sa mu cikin inwar addinin musulunci da karantarwarsa.
Daga cikin abinda TURAWA ke fama da shi a yau mai tada hankali shine;
Akwai tanadin da kowane mutum yake yiwa kansa na kuddi don tsufansa.
Dole ne mutum ya tara wasu makudan kudade da zasu amfane shi idan ya tsufa. Don me?
Don babu wanda zai kula da shi idan ya tsufa. In ba haka ba kuwa lalle ne zai kare rayuwarsa a gidan nakasassu da
gajiyayyu wanda gwamnati ta tanada wanda kuma ba shi da banbanci da zaman fursuna a kurkuku.
A lokacin su kuma 'ya'yansa maza da mata na can suna soyayya da abokai da kawayensu ba wanda ya damu da shi.
A kasashen turawa akwai kowace doka har da ta hakkin karnuka amma babu wata doka akan hakkin IYAYE. Don me? Wai don kada a takura wa 'ya'ya! Za
a shiga cikin 'yancinsu!!
Musulunci ya banbantamu da su ta in da ya nuna mana cewa iyaye suna da hakki sosai ga 'ya'yan su koda kuwa bayan sun MUTUNE.
Wata likita ta bada labarin wani mutum mai biyayya mai ban mamaki.
Tace wata Tsohuwa ce wawiya da ba a haife ta ma da hankali ba.
'Dan ta ya zo da ita yana mai tsananin kula da ita. Ba ya son komi ya same ta. Kullum idonsa na kan wannan mahaifiyar tashi.
Saboda mamakin irin yanda yake kula da mahaifiyar tasa, yasa wannan likita ta tambaye shi, kuma ya sanar da ita cewa tun lokacin da aka haifeta (ita mahaifiyar tasa) tana fama da tabuwar hankali kuma bata san abinda take yi ba.
An aurar da ita ga mahaifinsa bayan ta samu cikinsa sai mahaifin ya kasa hakura da zama da ita, ya sauwake mata ta koma hannun iyayenta. wannan abin ba karamin tashin hankali ya saka wannan matar ba.
Akan haka yasa ta kara shiga tsananin tashin hankali.
Tashin hankalin da wannan matar ta shiga shine, yasa ya bar komai baya komai sai kula da ita mahaifiyarsa.
Ku duba fa shi wannan ya kula da uwar da cikinsa kawai ta dauka bata san wahalarsa kowace iri ba yana ta tarainiya da ita haka.. To, mu da iyayenmu suka sha kowace irin wahala a kanmu ya zamu yi kenan?!
A cikin tarihin magabata akwai labarai masu kayatarwa game da bin wannan umurni na ubangiji na kwautaatawa iyaye.
1. Mis'ar bin Kidam (rta) ya taba kawo ma
mahaifiyarsa ruwa bayan ta nemi haka amma ko da ya zo ta yi bacci. Sai ya tsaya har gari ya waye bai tashe ta ba kuma bai tafiyarsa ba.
2. Muhammad bin Al-Munkadir ya ce, na kwana ina murza kafar mahaifiyata don ta ji dadin bacci, kanena kuma ya kwana yana sallah. Bana tunanin a bamu lada daya sai dai ni na fishi samun ladar.
3. Sayyidina Abu Huraira (rta) ya ga wani mutum yana tafiya bayan wani dattijo. Sai ya tambaye shi, wane ne? Ya ce, mahaifina. Sai ya ce: kada ka kira shi
da sunansa, kada ka zauna kafin sa, kuma kada kayi tafiya a gabansa.
Bayan haka ya kai dan uwa musulmi! Ka sani ba wani laifi a wurin Allah wanda yake gaggauta kama mai yinsa, ya debe masa albarka, ya barkata masa rayuwa tun a nan duniya kamar cuta wa iyaye.
Sai ka ga mutum ya damu da matarsa, ya kula da 'ya'yansa amma bai ko san halin da mahaifiyarsa take ciki ba.
Ankarbo daga Abu kahil, cewa Manzon Allah (saww) yace; ku cewa wanda yayi biyayya ga mahaifansa, a halin suna raye ko suna mace, to lalle Allah (SWT) ya yarda da shi a ranar Qiyama, sai muka ce yaya mutum zaiyi biyayya ga mahaifansa Alhali suna mace Ya Rasulillahi? Sai yace; ya nema musu gafara, kar ya zagi mahaifan wani balle a zagi na sa mahaifan.
YA ALLAH KA GAFARTAWA IYAYEN MU, KA YAFE MUSU KURAKURANSU...(AMEEN)
NI DAI KU SHAIDA NA TURO WANNAN BADAN KOMAI BA SAI DON TUNA WA DA MAHAIFANA DA KUMA ROKA MUSU GAFARA.
KACE AMEEN KUMA KA TURA GA 'YAN UWANKA DOMIN ROKAWA IYAYENKA GAFARA.
No comments:
Post a Comment