BAMA GOYON BAYAN ADAKATAR DA ALMAJIRANCI, AMMA MUNA GOYON BAYAN ADAKATAR DA BARA. Repost
Daga Ahmad Musa
Duk mutumin da ya bar inda yake da zama ya tafi wani guri domin neman iilmi sunan shi Almajiri, kalmar Almajiri ya samo asali ne daga Almuhajir (wanda ya bar inda yake yakoma wani guri domin neman yardar Allah)
Saboda haka bama goyon bayan adakatar da Almajiranci, domin dakatar dashi tamkar fada da addini ne
Idan kuma har yunkurin Gwamnati na ta dakatar da Bara ne ba Almajiranci ba (Karatun Allo) muna goyon bayan haka saboda Bara kaskanci ne Bara ba addini ba ne kuma Sahabban annabi basuyi bara ba kuma Almuhajirun basuje Habasha ko Madina sunyi bara ba
Addinin Musulunci addini ne mai girma bai kamata duk matsayin da addinin yake dashi ace ana neman iliminsa cikin halin tozarta da wulakanci ba. Gaskiya sam bai kamata irin matsayin da AlQur'ani yake dashi ace ananeman iliminsa cikin halin tozarci ba saboda haka muna goyon baya da adakatar da Bara.
Ya kamata iyayen yara idan zasu tura yaransu karatun allo (Almajiranci) su turasu da sutura da abinda zasu ci fiye da yadda suke yi idan zasu turasu makarantun boko.
Daga karshe muna rokon Allah ya bamu Ilimi mai amfani. Ameen
No comments:
Post a Comment