Saturday, February 22, 2020

4. TAKATACCEN TARIHIN FATIMAH (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)

4. TAKATACCEN TARIHIN FATIMAH (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)

Fatima (R.Ah) ita ce 'yar sa ta hudu, kuma 'yar autar Annabi (S.A.WS). Kuma ita zata kasance shugaban matan Aljannah. An haife ta a farkon saukar wahayi, watau a lokacin yana da shekara 41. An ce wannan suna na Fatimah (wanda ma'anarsa kusan itace, (ta tsira daga wuta). Allah Ta'ala ne ya saukar dashi.

An aurar da ita ga Sayyadina Ali (R.A) a shekara ta 2 bayan Hijirah, kuma an ce ta fara zama da shi watanni bakwai da rabi bayan daurin auren. A lokacin da aka yi aurensu, tana da kusan shekaru 15, shi kuma Ali yana da wajen shekaru 21. Duk daga cikin 'ya'yansa mata. Kusan Annabi (S.A.Ws) ya fi nuna mata kauna; a duk lokacin da zai tafi wani bulaguro kusan ita ce ta karshe da suke rabuwa, idan kuma ya komo ita ce ta farko da suke saduwa.

An ce kamar watanni 6 bayan fakuwar Annabi (S.A.Ws), sai Fatimah ta kamu da rashin lafiya. Wata rana ta ce da baiwarta:
Ina son in yi wanka. Ki kawo mini ruwa.

Sai tayi wanka, ta canza katayyakinta. Sai kuma ta ce a kaimata gadonta tsakiyar daki. Daga nan sai ta kwanta akan gadon tana fiskantar al-kiblah, kana ta sanya hannunta na dama karkashin har6arta ta dama, daga nan kuma sai ta ce:
Yanzu zan rasu.

Kan ka ce Kwabo! Ta riga ta cika. Tana da 'ya'ya maza guda uku da mata uku. An haifi Hassan da Hussain (R.Anh) a shekara ta biyu da ta uku bayan aurensu. Muhassan (R.A) dansu na uku, an haife shi ne a shekara ta hudu bayan Hijirah. Amma ya rasu tun yana dan yaro. Ita kuma Rukayyah wadda ita ce 'yar su ta farko, ta rasu tana jaririya, don haka shi ya sa ba a ambace ta ba sosai a tarihi. Sai kuma 'yar su ta biyu Ummu Kulthum da kuma 'yar su ta uku Zainab.

Insha Allahu rubutu na gaba shi ne: Mata da ya Haramta mu aura. Muna kuma rokon Allah Ta'ala Ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen ya Qadiyal Haajah.

No comments:

Post a Comment