YAFARA SHIGOWA CIKIN HAUSA FULANI Artificial Virginity Hymen.(BUDURCI NA WUCCIN GADI), AKWAI MATSALA
-HYMEN a turance wata fatace datake gaban mata dab a cervix, a hausance tana daukan sunan
BUDURCI, kuma rashinta shine rashin budurci.
Fatar bata da karfi sosai kuma ruwa kan iya wucewa ta cikinta, tana dauke Da kananan hanyoyina jini, shiyasa fashewa ko tsagewarta kansa jini ya fita.
Mafi akasari wannan fata kan tsage ne idan daya daga cikin wadannan abubuwa suka faru ga macce:
1. Idan an sadu da mace (copulation)
2. Wajen neman fitar da sha'awa da wani abu mai karfi (vaginalinsertion or mastubation)
3.Yawan tsalle ko hawa mashin, keke, doki ko jaki.
Kasancewa mafi yawan Maza kanyi amfani da fashewar wannan fata da fitar jini wajen gwada budurcin 'Ya mace don tabbatarwa bata ta6a saduwa da ko wane namiji ba, Sai turawa suka zauna sukayi nazarin yin Jabun wannan Fatar (mai suna Artificial Virginity Hymen) domin matan da suka rasa budurci kafin Aure.
Shi wannan FAKE HYMEN roba ce da akayita da sinadare masu narkewa dazai dace da jikin mutum (prosthetic in nature) yanda idan macen da ta rasa budurcinta tasa zai zauna daidai gurbin ta, sannan da zarar ta sadu da angonta wani jan sinadari zai fashe daga cikin Artificial Virginity Hymen din mai kama da jini, toh dazarar ango yaga haka sai ya zaci matar sa budurwa ya aureta.
Babu shakkah akwai abubuwanda ya kamata mata su kula da su game da wannan Fake Hymen din.
Kasancewar bayan saduwa fake hymen zai iya fitowa, in kuma bai fito ba zai iya narkewa a cikin gaban mace, don haka zai iya kawo matsalolin lafiya ga macen datayi amfani dashi.
Haka zalika jan ruwan da wannan FAKE HYMEN din ke fitarwa mai kama da jini, shima zai iya canza ka'idar tsaftar vagina mace, saboda cikinsa akwai (chemicals) dauke da kalar JA, don haka wannan abin zai iya kawo matsaloli kamar haka:
Yana canza yanayin sinadaran dake kiyaye vagina.
Yana iya kawo cancer of vagina.
Yana toshe ma haifa akasa samun haihuwa.
Yana canza tsarin hailar mace (ta yanda hailar zata rikice).
Yana kawo rashin haihuwa (infertility) ga maza.
Hakika idan bamu kula ba zai cutar damu matuka domin ya fara shigowa yankin Hausa Fulani
Muna rokon Allah ya karemu daga aikin danasani. Ãmīn ya Qãdiyal Hãjah
Monday, March 2, 2020
TAKAITACCEN TARIHIN YA'YAN ANNABI (S.A.Ws) MAZA

Annabi (S.A.Ws) yana da 'ya'ya maza uku, mata hudu. Dukkan ' ya'yansa ya same su ne wajen Khadijah (R.Ah) in banda dansa Ibrahim. Qasim shi ne baban dansa na farko, da aka haifa masa kafin fara saukar wahayi. Ya rasu a lokacin yana shekara biyu.
Dansa na biyu Abdullah, an haife shi bayan fara saukar wahayi. Don haka daga baya ake kiransa Tayyab da kuma Tahir. Shima ya rasu yana dan yaro. Alokacin rasuwarsa Kuraishawa sun yi ta murna suna cewa:
Muhammadu ba shi da (namiji), don haka ba shi da wanda zai gaje shi. Don haka sunansa zai 6ace bayan mutuwarsa.
A saboda haka ne Allah (Subhanahu wa Ta'ala) ya saukar da suratul Kauthar 1-3)
Dansa na uku, kuma na karshe, Ibrahim, an haife shi ne a Madinah, a shekara ta 8 bayan Hijirah. Baiwar Annabi (S.A.Ws) Mariya ita ce ta haifa masa yaron. An yanka raguna guda biyu, sa'annan wani Sahabi da ake kira Abu-Hind Bayazi (R.A) shi ne ya aske kan yaron, kana daga baya aka bayar da azurfa daidai nauyin sumarsa a matsayin sadaka, sa'annan aka binne sumar.
Annabi (S.A.Ws) ya ce:
Zan baiwa da na sunan kakana, Ibrahim (As).
Shima wannan yaron ya rasu ranar 10 ga watan Rabi'ul-Awwal, shekara ta goma, bayan Hijirah. Alokacin yana da watanni 18 kadai a duniya. Manzon Allah (S.A.Ws) ya ce:
Allah Ta'ala Ya nada wata mai reno, da za ta lura da Ibrahim a cikin lambunan Aljannah.
Insha Allahu rubutu na gaba akan 'Ya'yan Annabi (S.A.Ws), Mata amma kafinnan zan danyi tsokaci akan mai kirma Gwamnan Borno. Muna kuma rokon Allah ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen ya Qadiyal Haajah.

WAYA CEN-CENTA YAYI WA MUTANE LIMANCI ******************************************
WAYA CEN-CENTA YAYI WA MUTANE LIMANCI
******************************************
Yana da Kyau Idan Zakuyi Sallah A Wurin da Ba Liman Ne Kuke da shi ba To ku Lura da Wasu Abubuwa Kan Wanda Zai Jaku Sallah daga Cikin Ku;
Na farko: Wanda ya fi karatun Alqur’ani, wato wanda ya fi yawan haddace shi, kuma yafi sauran fahimtar hukunce-hukuncensa.
Na biyu: Wanda ya fi sanin Sunnah, wato wanda yasan ma’anoninta da hukunce-hukuncenta.
Na uku : Wanda ya dade da yin hijira, daga garin kafirci zuwa garin musulunci. Idan ba hijira a lokacin sai a gabatar a kan wanda ya riga tuba da qaurace wa sabo.
Na hudu : Idan su yi daidai a duk abin da ya gabata, to sai a sa wanda ya fi yawan shekaru.
Dalili akan abin da ya gabata hadisin Abu Mas’ud Al-ansari (RA), ya ce, Manzon Allah (Saww) ya ce, “Wanda ya fi mutane karatun Alqur’ani shi zai limance su, idan sun yi daidai a karatu, to wanda ya fi su sanin sunnah, in sun yi daidai a sanin sunnah, to wanda ya fi dade wa da hijira, idan sun yi daidai a hijira to wanda ya dade da musulunta” (Imamu Muslim ne ya rawaito shi).
Haka kuma Ana kula da wannan jerin yayin nada limamin masallaci, ko in a cikin jama’a ne wadanda babu lmami ratibi a cikinsu, in akwai limami a ratibi a cikinsu, ko kuma wanda ake gidansa yana nan, ko kuma wanda yake jagora to shi za a gabatar da wanda ba shi ba (Kamar a ce sarki ne ko shugaban wurin da makamancinsu).
Saboda fadin Manzon Allah (Saww) “Kada wani mutum ya yi wa wani mutum limanci a wurin ikonsa, kada ya zauna a wurin zamansa a gidansa [Wurin zamansa, shi ne wurin da aka tanadarwa baqo don ya zauna], sai dai da izininsa” (Imamu Muslim ne ya rawaito shi).
Allah ya Taimake mu da Taimakonsa.

Friday, February 28, 2020
SABON SALO DA MASU GARKUWA DA MUTANE KEYI GURIN AMSAR KUDI

"Jama'a ga wata matsala babba da take faruwa, wani aboki nah yake sanar dani wannan labari, kuma wannan labari da gaske ne.
Wasu mutane sun zo wajen wani mutum wanda yake dealer ne na sayar da motoci a wajen sana'ar sa (car stand) sai suka yi cinikin wata mota Camry, akan kimanin kudi naira miliyan biyar.
Sai suka karbi Account number dinsa akan zasu yi masa transfer na kudin, sai ga naira miliyan uku sun shigo Account din dealer din, akan zasu ciko masa sauran kudin daga baya.
Bayan wani lokaci sai suka zo suka bashi hakuri akan ba zasu iya sayen motar ba, saboda rashin kudin da zasu cika, sai suka ce to ya basu miliyan biyu da dubu dari biyar, sun bashi saura naira budu dari biyar din saboda dawainiyar da yayi musu. Wannan mutum yana murna ya samu na banza.
Bayan kwana uku yana zaune a car stand dinsa sai ga Jami'an anti kidnapping da anti SARS sunzo suna tambayar sa ko shine aka tura masa miliyan uku yace ehh? Kuma shi bai san su ba, bai taba ganin su ba.
To wata hanya ce ta yan kidnappers da suke yi wajen amsar kudin fansa (ransom) daga yan uwan Wadan da suka kama (victims)
Dan ALLAH a yada wannan a sanar da yan uwa ayi yekuwa a masallatai da dukkan wurare dama gidajen radio, makarantu.
Haka nan kada ku yarda koda dan uwan ka ne ya nemi ka bashi Account number sai ka bincike shi, kuma idan wani amini gare ka ya bukaci zai tura maka kudi ko za'a tura masa kudi, idan kaga kudi ne masu yawa to kuyi rahoto a ofishin yan sanda mafi kusa domin kada wani tarko ne baku sani ba.
Idan da hali ka turawa wasu groups dan su fadaka.
ALLAH Ya karemu." Aameen
Daga. Zauren fiqhus Sunnah

Thursday, February 27, 2020
ABINDA YA KAMATA MUYI A DUK LOKACIN DA MASIFA TA SAME MU

UMMU SALMA (R.Ah), tafada cewa, wata rana Abu Salma ya dawo gida daga majalisin Annabi (S.A.Ws) sai ya koyamin wata magana dayaji daga bakin ANNABI (S.A.Ws), maganar data matukar farantamin rai sosai.
Yace dani: "Annabi (S.A.Ws) yace: "Idan wata musiba tasamu mumini sannan yayi istirja'i wato yace, 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un',sannan kuma ya hada da wannan addu'ar yace: "Ya Allah Kabani lada akan wannan musiba data sameni, Ka bani abinda yafi alheri daga wanda na rasa." Idan mutum yayi haka Allah (Swt) zai amsa masa addu'arsa.
Ummu Salma taci gaba da bada labari akan cewa: Sai na kiyaye wannan magana da mijina ya fadamin, da Allah Yayi masa rasuwa bayan nayi istirja'i, sai nayi wannan addu'a.
Ina kammala wannan addu'ar sai nace acikin zuciyata: oh! Ko ina zansamu mijin dayafi Abu Salma?
Wata rana bayan nagama takaba, sai Manzon Allah (S.A.Ws), yazo gidana yayi sallama. A lokacin ina jeme wata fata, sai nayi wuf na tashi na kimtsa sannan nace masa ya shigo.
Lokacin daya shigo na bashi wani pillow wanda cike yake da ganyen dabino sai ya zauna akai. Bayan mun gaisa sai ya bayyana mini cewa yana bukatar ya aureni.
Daya gama maganarsa sai na ce masa: Ya Rasoulullahi (S.A.Ws) bani da ta cewa indai kana sona, Amman inada kishi mai tsanani kada kaga wani abu daga gareni wanda Allah zai min azaba akanshi. Sannan kuma na tsufa kuma inada nauyi akaina (na 'ya'ya).
Da na gama bayani na sai MANZON ALLAH (S.A.Ws) yace; "Batun cewa kin fara tsufa ai nima hakan take, batun nauyin iyali kuma, ai nauyinki dana iyalinki duka akaina suke". Ina jin haka sai nace: "Ya Rasulullahi na sallamar".
Daga nannne MANZON ALLAH (S.A.Ws) ya aureta ta zama matarsa. Allah ya musanya mata Abu Salma da Mafi daukaka da daraja a doron kasa.
Sannan Uwar Muminai Nana Aisha (RA) tace, wata rana muna a cikin dare muna tare da Annabi (S.A.Ws), a cikin daki na Sai fitila ta dauke.
Nan take Naji Annabi (Saww) Yace, "Innalillahi Wa'Inna ilaihin Raji'Un" Sai nace, "Ya Rasulillahi Ina ce sai Abin bakin Ciki ya samu bawa zaiyi istirja'i." Sai Yace dani, "Yake Aisha Hakika duk abinda ya batawa bawa Rai ya kamata yayi istirja'i."
Ya Allah Ka taimake mu da Taimakonka a duk lokacin da wata musiba ta same mu mu zamo masu hakuri.
Babu Shakka Idan ka turawa Wani Wannan tunatarwa a duk lokacin da wata masifa ta same shi ya tuna yayi istirja'i to zaka samu lada koda baka duniyarnan. Daure ka turawa Wasu.

Wednesday, February 26, 2020
3. TAKATACCEN TARIHIN UMMU KULTHUM (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)

Ita ce 'yar Annabi (S.A.Ws) ta uku daga cikin 'ya'yansa mata. Ta
auri Utaibah dan Abu Lahab, amma a lokacin ba su fara zama ba, lokacin da Utaibah ya sake ta bayan saukar da Sura Al-Lahab (watau Tabbat-Yada) kamar yadda aka riga aka ambata a baya. Bayan ya sake ta sai Utaibah ya zo wajen Manzon Allah (S.A.Ws) yana yi mishi rashin kunya.
Annabi (S.A.Ws) ya la'ance shi ya yi addu'a kamar haka:
Ya Allah Ta'ala! Ka hada shi da daya daga cikin karnukanka, don ya azabtar da shi.
Abu Talib wanda bai Musulunta ba, ya kadu da jin wannan la'anar, don haka sai ya ce da Utaibah:
Kai shi ke nan! Babu makawa, kashinka ya bushe.
Wata rana Utaibah yana tafiya tare da Abu Lahab cikin wata tawaga da za ta je Sham (Siriya), sai Abu Lahab duk da kafircinsa ya ce da jama'a:
Ni fa ina gudun la'anar Muhammadu. Don haka kowa ya lura da dana. Sun kuwa yada zango a wani wuri da yake da zakuna.
Jama'a duk sai suka yi lodin kayansu wuri daya, sa'annan suka sanya Utaibah ya kwanta saman kayan, kana su kuma sauran jama'a suka kewaye kayan. Zaki ya lallo6o cikin dare, inda ya sunsuna duk jama'ar da suke kwance jikin kayan. Daga nan sai ya tsallake jama'a inda ya hau sama wurin da Utaibah ke kwance. Da ya isa sai Utaibah ya yi ihu. Amma Ina! Kafin ka ce uffan, ya raba kansa da jikinsa.
Don haka wannan wata ishara ce gare mu, ya kamata lallai mu guji sa6awa bayin da Allah Ta'ala ke kauna. Annabi ya ruwaito cikin Hadisil-Kudusi, inda Allah Ta'ala ke cewa:
Duk wanda ke gaba da masoyina, zan shirya yaki da shi.
Bayan rasuwar Rukayyah (R.Ah), an sake auradda Ummu Kulthum (R.Ah) ga Sayyadina Uthman (R.A) a cikin watan Rabi'ul Awwal, shekara ta 3, bayan Hijirah.
Annabi (S.A.Ws) na cewa:
Na bayar da UMMU Kulthum aure ga Uthman bisa ga Umarnin Allah Ta'ala.
Ta rasu a cikin Watan Sha'aban na shekara ta 9, bayan Hijirah, ba tare da samun haihuwa ba. Bayan rasuwar ta an ji Manzon Allah (S.A.Ws) yana cewa;
Da ina da 'ya'ya mata 100, zan iya bayar da su aure ga Uthman (R.A) (daya bayan daya)
Insha Allahu rubutu na gaba akan Fatimah (R.Ah) yar Annabi (S.A.Ws) amma kafinnan zan dan yi rubutu akan wani al'amari da yake so ya haifar da barazana ga tsaron Nigeria. Muna kuma rokon Allah Ta'ala Ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen ya Qadiyal Haajah.

Sunday, February 23, 2020
IDANU UKKU BAZASU KUKA BA
IDANU UKKU BAZASU KUKA BA
A ranar kiyama, dukkan idanuwa za su yi kuka, in banda guda uku: Idon da yaki barci don gadin musulmai (dukiyoyinsu, kasarsu da dai sauransu), saboda Allah;
Sanan Idon da ya yi kuka don tsoron Allah; da kuma idon da aka rufe shi daga kallon abubuwan da Allah Ya haramta.
Ya Allah muna tawassili da sunayenka da siffofinka muna kuma kamun kafa da fiyayyen halitta Annabin rahama (S.A.Ws), muna kuma tawassili da wannan azumi da mukeyi domin neman kariyarka dama duk wani ibada da mukayi wacce ka yarda da ita,
Ya Allah kafimu sanin Abinda ke faruwa akasarmu, ya Allah ka yaye mana wannan masifa da ke addabarmu ba dan HALINMU ba, ya Allah dukkan mai hanu acikin wannan al'amar,i idan ba mai shiryuwa bane ya Allah Ka maida kaidinsa garesa Ka nesantashi daga garemu Ka Karemu da Kariyarka Ka bamu lafiya da zama lafiya da abinda lafiya zata ci
Ya Allah Ka Sa Mu dace da dacewarka ka tsaremu da Azabarka. Ãmīn ya Qādiyal Hājah
https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Subscribe to:
Posts (Atom)