Tuesday, December 12, 2023
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA BIYU
YARJEJENIYAR HUDAIBIYA DA KUMA LABARIN ABU JANDAL DA KUMA ABU BASIR (R.A) KASHI NA BIYU
A kashi na ɗaya mun tsaya a inda "Mahaifinsa Suhail, (wanda a lokacin bai Musulunta ba), shi ne jakadan Kuraishawa a wajen wannan yarjejeniya, ya kaiwa Abu Jandal (Radhiyallahu anhu) mari, inda kuma ya tsaya kai da fata cewar, lallai sai ya koma da shi Makkah."
Manzon Allah (S. A.Ws) ya yi ƙoƙarin tsoma baki kan batun, ya ce; Tun da ba a sa hannu akan yarjejeniyar ba, babu wata hujjar komawa da Abu jandal. To amma Suhail ya kafe, inda ya ki sauraren duk wata hujja da za'a bashi, ya ma nuna cewar, shi kam lallai ba zai bar ɗansa a baya hannun Musulmi ba, duk da cewar Manzon Allah (S.A.Ws) da kansa ya yi wannan roko. Don haka harma ya nuna kamar zai yi watsi da wannan yarajejeniyar.
Abu Jandal (R.A) ya ɗaga murya, ya dinga lissafa irin wahalhalun da yake sha a hannun Ƙuraishawa. Amma kuma abin ya ƙara ma Sahabbai suno, lokacinda Manzon Allah (S.A.Ws) ya yarda da a koma da shi. Duk da haka ya bashi haƙuri, yana mai cewa:
Kada ka yanke ƙauna, Ya Abu Jandal, bada jimawa ba, Allah Ta'ala zai kawo maka mafita.
Bayan an ƙulla wannan yarjejeniya kuma Manzon Allah (S.A.Ws) ya koma Madinah, sai kuma wani Musulmin shima daga Makkah, da ake kira Abu Basir (R.A) ya sulale zuwa Madinah, ya nemi mafaka a wurin Manzon Allah (S.A.Ws). Amma kuma yaki, don gudun karya ɗaya daga cikin sharuɗɗan sulhun, ya kuma hannuntashi ga mutane biyun da Ƙuraishawa suka aiko, don komawa da shi.
Shima, kamar Abu Jandal (R.A), ya neme shi da ya yi hakuri ya jira zuwan taimako daga Allah Ta'ala. Lokacinda Abu Basir da 'yan rakiyarsa suke kan hanyarsu ta komawa Makkah, Abu Basir ya kaɗa baki ya ce ma ɗaya daga cikinsu; 'Aboki! Amma takobinnan naka yana da ban sha'awa.' Wannan zancen ya burge mutumin, sai ya fitar da shi daga gidansa, ya ce: 'Haka ne, hakika takobin yana da kyau matuka, na gwada amfani da shi akan mutane masu yawa, karbi ka ga yadda yake.'
Cikin bacewar basira, wannan mutum ya mikawa Abu Basir (R.A) takobin, shi ko baiyi wata wata ba, ya gwada shi akan mai shi, ya kashe shi. Na biyun ya ranta cikin na kare, ya isa Madinah don kai kara ga Manzon Allah (S.A.Ws). Ana cikin haka Abu Basir (R.A) shi ma ya isa. Ya cewa Manzon Allah (S.A.Ws): 'Ya Rasulallah! (S.A.Ws), ka riga ka hannunta ni gare su can farko, ka cika sharuɗɗan sulhu. Ni, bai zama tilas a kaina ba. Don haka na ƙubuce musu da wannan dubarar, saboda ina tsoron su cilasta mini rabuwa da Addini na.'
MU HAƊU A KASHI NA UKU
Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws)
✍️ AHMAD MUSA
👉👇Ku shiga nan don samun kashi na ɗaya
https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/yarjejeniyar-hudaibiya-da-kuma-labarin.html
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment