Wednesday, December 20, 2023

YADDA ABU ZAR GHIFARI(RADHIYALLAHU ANHU)YA KARƁI MUSULUNCI KASHI NA ƊAYA

YADDA ABU ZAR GHIFARI(RADHIYALLAHU ANHU)YA KARƁI MUSULUNCI KASHI NA ƊAYA Abu Zar Ghifari (R.A) shahararre ne daga cikin Sahabbai, kuma ya yi suna wajen takawa da kuma ilminsa. Sayyadina Ali (R.A) ya sha cewar: 'Abu Zar ya sami wani irin ilmi, da sauran mutane suka kasa samu.' A lokacin da ya samu labarin Manzancin Manzon Allah (S.A.Ws) a karo na farko, sai ya yi maza ya aika da kanensa domin ya tafi Makkah ya binciko masa mutumin da ake cewa shi Annabi ne, watau ana aiko masa da wahayi. Ɗan-uwan nasa ya koma bayan da ya kammala binciken da ya kamata, kana ya nuna masa cewar, lallai Muhammad (S.A.Ws) mutum ne na kirki mai hali na gari, kuma hakika irin wahayin da yake samu mai ban al'ajabi ba sha'irori ba ne ko kuma sihiri. To amma wannan rahoto da ya samu bai gamsar da shi ba sosai, don haka sai ya yanke shawarar tafiya Makkah, don ya binciko wa kansa gaskiyar lamarın. Da zuwansa Makkah, sai ya zarce kai tsaye zuwa Masallacin Ka'abah. To sai dai a lokacin, bai san wane ne Manzon Allah (S.A.Ws) ba, kuma yana ganin bai dace ba lokacin, ya ce zai tambayı wani game da shi.
A lokacin da dare ya fara yi, da Sayyadina Ali (R.A) ya hango shi, ya tabbatar cewar bako ne, don haka ba zai kyale shi ba, Tun da yake abu ne daman da Sahabbai suka riga suka saba da yinsa, watau kyautatawa ɗan hanya, da matalauta tare da baki. Don baka sai ya dauke shi suka tafi gıda tare Bai dai tambaye shi dalilin zuwansa Makkah ba, kana shi kuma Abu Zar bai yi subul da baka ba, ya fadi. Da gari ya waye, sai ya sake komawa Baitullah inda ya zauna har zuwa ketowar magariba, ba tare da sanin ko wane ne Manzon Allah (S.A.Ws) ba. Alal Hakika kowa ya san ana ganawa Annabi da Sahabbansa wahala a Makkah, kuma kila shi yasa shi kansa Abu Zar, yana tsoron abin da zai iya biyowa sakamakon tambaya game da batun Manzon Allah (S.A.Ws) Sayyadına Ali (R.A) ya sake jansa zuwa gida, inda ya sake kwana a wurinsa, amma duk da haka bai yi katsalandan din tambayarsa dalilin zuwansa wannan birni. To amma a dare na uku bayan ya ciyar da shi kuma ya shayar da shi kamar waɗannan ranaku na baya da suka wuce, sai ya tambaye shi cewa: Dan-uwa, me ya kawo ka wannan gari ne?" Kafin Abu Zar ya ba Sayyidina Ali (R.A) ansa, sai da ya yi alkawari da shi akan cewa, lallai ya gaya masa gaskiya. MU HAƊU A KASHI NA BIYU Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️ Ahmad Musa

No comments:

Post a Comment