Saturday, December 2, 2023

SHAHADAR ANAS BIN NADR (Radhiyallahu anhu) KASHI NA ƊAYA

SHAHADAR ANAS BIN NADR (Radhiyallahu anhu) KASHI NA ƊAYA Anas bin Nadr (R.A) yana daya daga cikin Sahabban da basu samu sukunin shiga yakin Badar ba. Ya yi matukar bakin cikin rashin samun wannan babbar dama, wadda kuma ita ce irinta ta farko, kuma mafi ɗaukaka daga dukkan jihadin da aka yi a cikin tarihın Addinin Musulunci. Ya yi ta tunanin Allah Ta'ala Ya kawo wani yakin da zai samu damar bayar da tasa gudunmuwar, Tun da yake Allah Ta'ala bai sa ya samu sukunin shiga na Badar ba. Ai kuwa ba a dade ba, sai ga yakin Uhudu, watau shekara guda bayan na Badar. Ya shiga sahun jerin gwanon askarawan Islama, tare da zuciya guda. Duk da cewar kafirai sun fi yawa wajen wannan yaki, amma duk da haka, Allah Ta'ala Yana taimakon Musulmi har zuwa bayan lokacin da wasu mutane suka yi katoɓara, sa'annan reshe ya juye da mujiya, Musulmi suka daina cin galaba.
A wannan lokaci dai, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya umurci wasu maharba 'yan baka su hamsin, da su rika lura da baya, domin kada abokan gaba da ke kan doki, su ɓullo masu kwatsam. An dai riga an ja kunnensu cewar, lallai kada su kuskura su motsa daga inda suke, har sai sun samu umurnin yin haka daga wajensa. To amma a lokacin da suka ga Musulmi suna samun nasara, kana kafirai suna ta ranta a na kare, sai suka bar inda suke, da tsammanin cewar an gama yakin. Don haka suna ganin kamar wannan lokaci ne, na kwasar ganima. Shi jagoran 'yan bakan, ya yi iya matukar bakin kokarinsa don hana su wannan abu, don haka ya roke su da su ci gaba da tsayuwa wurin da suke, amma wadanda ma suka saurare shi basu fi mutane goma ba, inda suke ta jayayyar cewar, wannan umurni dai na Manzon Allah (S.A.Ws) kurum har zuwa lokacin da ake yin faɗa ne. MU HAƊU A KASHI NA BIYU Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️Ahmad Musa

No comments:

Post a Comment