Saturday, December 2, 2023

BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU

BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU A kashi na ɗaya mun tsaya a dai-dai inda "Mai makon ma su amsa wannan gayyata da ya yi musu", sai ma suka ki ko saurarensa. Kuma duk da cewar an san larabawa da karimci, maimakon gwada wannan karimci nasu sai suka shiga yi masa abin da bai kamata ace ya fito daga bakinsu ba, a matsayinsu na shugabanni. In gajarce muku labari, fitowa ma fili suka yi ɓaro-ɓaro suka ce da shi, basa son ganinsa a wannan garin nasu. Da dai a kalla kamata ya yi ace Manzon Allah (S.A.Ws) ya samu kyakkyawan tarbo da kuma jawabi mai daɗaɗawa daga gare su Tun da yake sune shugabannin kabilarsu.
To amma maimakon haka, kurum sai ɗaya daga cikinsu ya kaɗa baki ya ce, 'Kai ne Allah Ya zaɓa a matsayin Annabi!' Wani kuma da ba'a ya ce: 'Duk yanzu Allah Ya rasa wanda zai zaɓa ya zama Annabinsa sai kai? Shi kuma na uku sai ya ce: 'Kai ni ba na ma son yin magana da kai, domin idan kai Annabi ne, yin gardama da kai jawo wa kai rigima ne, idan kuma kana kwaikwayon Annabawa ne, to don me zan ɓata lokaci na, ina magana da Annabin karya?" Manzon Allah (S.A.Ws) wanda yake kamar dutse ne wajen dauriya da hakuri, bai ɓata rai ba, kan irin abin da waɗannan shugabannin suka yi masa. Maimakon haka, sai ya shiga ƙoƙarin saduwa da talakawan garin. Amma duk cikinsu, babu wanda ya tsaya ya saurare shi. Maimakon haka ma sai suka nuna gara ma ya san inda dare ya yi masa, ya bar musu, garinsu. Lokacin da ya fahimci cewar duk irin abin da yake son nuna musu, ba za su fahimce shi ba, don haka sai ya yanke shawarar barin garin. To, amma su ma kyale shi ya fita lami lafiya, basu yi haka ba. Maimakon haka, sai suka tara fitinannun yaran garin, inda suka fito titi suna yi masa ature, kana suna (faɗa masa rashin kunya da bakaken maganganu), wasu kuma na jifansa. Allah Sarki! An yi ta jifansa da duwatsu, ko ina jikinsa yayi jina-jina, yadda har takai, takalmansa suka manne da kafafunsa saboda jinin da ke zuba. Ya bar garin cikin wannnan zullumi na bakin ciki. MU HAƊU A KASHI NA UKU Allah yasa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️*Ahmad Musa*

No comments:

Post a Comment