TARIHIN KUNGIYAR TALIBAN
KUNGIYAR TALIBAN
Daga Alkalamin wani bawan Allah
Mulkin Kasar Afghanistan dai a yau ya koma hannun Taliban, sai naga ya dace na warware wasu daya cikin al’ummar mu wani abu mai rikitarwa game da su:
(1) Wannn suna Taliban, a harcen su na Pashtun yana nufin jam’in dalibai, kamar Musulman ne, abinda ke nufi jam’in Musulmi, su Dalibai ne wadanda suka gogu a karatun zaure, kamar yadda yake a al’adar Kasar su
(2) Mazhabarsu ta Aqeedah Maturidiyya ce ta Abu Mansur Almaturidi, daya ne daga cikin manyan Malaman Sunnah na zamaninsa, Mazhabarsa tana kusa sosai da Mazhabar Abul Hasanil Ash’ari.
Yadda wasu suke munana zato a garesu, Taliban a gurin ‘yan Boko Haram da ISIS suna musu kallon ‘yan bidi’ah ne wadanda jininsu ya halatta, saboda wai Taliban sun sabawa mazhabar Salafiyya wadanda suke binta
(3) Taliban Mazhabarsu ta Fiqhu Hanafiyya suke bi, don Mazahabarsa ce ta yadu a Kasashen su tun farkon zuwan Musulunci, kuma da ita suke shari’ah, kamar dai mu nan Nigeria muke bin mazhabar Malikiyyah
(4) Taliban basu da dangantaka da wata kungiyar ta’addancin addini ko siyasa, balle kungiyoyi masu yawan kafirta Musulmi
(5) Amurka ta tuhumi Taliban da goyon bayan ta’addanci saboda kin mika musu Usama bin Laden don su hukuntashi a shekarar 2001, su kuwa Taliban sunyi aiki da ilmin da suka sani wanda ya haramta sallama Musulmi ga kafurai, har suka yarda da gushewar mulkinsu akan dabbaka Sunnar Manzon Allah (SAW)
(6) Taliban kwararru ne kuma gogaggu ne a iya mulkin jama’a, ba kamar yadda kafofin yada labaran turai ke bata su ba, ko da yake ba’a rasa su da wata kura-kurai wadanda ba wani ‘dan adam dake iya rabuwa da kuskure, amma alherinsu yafi kuskurensu yawa nesa ba kusa ba.
Kuma mulkinsu a Kasar Afghanistan yafi na Amurkawa masu yada addinin Kiristanci karfi da yaki, kamar yadda yafi na Iran da take kokarin shiga ta yayyaga Kasar, ta yada shi’anci kamar yadda takeyi yanzu haka a Iraqi
(7) Wasu mutane na yi musu hukunci da nau’in tufafinsu, ace wai suna tauye hakkin mata, suna yi musu kulle, wannan ba haka bane, irin tufafinsu na al’ada suke sawa mazansu da matansu, ko zaman Amurka a Kasar na shekara 20 bai canza matansu daga yin lullubi da sanya niqabi ba
(8) Bayyanar kungiyoyi masu da’awar jihadi na duniya irinsu Boko Haram, ISIS da sauransu ya sa wasu Musulmi ba su son jin maganar jihadi, abinda ke sa su jin tsoron Taliban, alhali Taliban ta banbanta da irin wadancan kungiyoyi masu yawan kafirta Musulmi.
Su Taliban mutane ne masu kokarin adalci hatta ga abokan gabar su, kuma kasancewar su jagorori a Kasar Afghanistan yafi alheri akan Amurka (Kafirai) ko Iran ‘yan shi’ah
Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmai a duk inda suke Amin
No comments:
Post a Comment