KUSKUREN DAYA KAMATA MUSANI GAMEDA TA'ADDANCIN WASU FULANI
Akwai matsaloli masu tarin yawa acikin Fulanin jeji wadda ya kamata asan dasu domin magance ta'addancin dake faruwa acikin al'ummar mu na yanzu, amma kafin mu san mataki da za a ɗauka, Lallai sai munsan dalilin wannan matsala mai ban takaici idan fa ba haka ba duk wani mataki da za a ɗauka toh za a yi cuta daban magani daban
Ya kamata musan cewa babban abinda ya haifar da wannan tashinhankali shine
Anyi watsi da fulanin jeji da gurɓatac ciyar imani, babu karatun addini da na zamani, sai wannan ya baiwa makiya Addinin Allah dama (irinsu Faransa), suka shiga ta karkashin kasa suka gurɓata fulanin, suke basu makamai ta hannun karnukan farautar su, duk wani makamin ta'addanci da ake shigo dashi Nigeria daga kasashe renon Faransa ne
Lallai ne muyi tunani a kan yadda za a fuskanci wannan ƙalubale. Akwai wasu sanannun abubuwa waɗanda su ne suka sa akayi watsi da fulanin jeji kuma hakan ya jefa mu cikin halin ƙaƙa-niƙa-yi da muke ciki a yau
Waɗannan abubuwan sune:-
1. Duk mutane mun ɗauka cewa tabbatar da nagarta a tsakanin al'ummah da kuma tafiyar da mutane a kan hanya ta ƙwarai aikin malamai ne kaɗai, alhali bayani daga Alƙur'ani mai tsarki sun nuna cewa aiki ne akan kowane Musulmi mai nunfashi kamar yadda Annabi (S.A.Ws) yace Addini nasiha ce ga dukkan Musulmi
2. Sa'annan mun ɗauka cewa idan mutum ya tsare imanin sa kuma yana ibadarsa, to ƙafircin sauran jama'a da fasadinsu ba zai shafe shi ba alhali umarni da akayiwa kowa shi ne, ya yi umarni da aikata alheri da hani daga mummuna ko kuma Allah ya aiko mana da masifu kala-kala a wannan duniyar inji Annabi (S.A.Ws)
3. Mutane masu hannu da shuni da talakawa da malamai da kuma jahilai, duk babu wanda ya damu da rayuwar Fulanin jeji, hakan kuma ya jefamu cikin wannan mawuyacin hali, don haka akwai haɗari sosai idan ba muyi ƙokarin musu nuni akan hanya ta kwarai ba, doloe ne mutashi tsayi haikan mu karantar dasu Addini domin amfanin kanmu da kuma anfanin zuriyar da zasu zo nan gaba.
4. Da yawa daga cikin mu tunanin mu shi ne, tun da mu kanmu ba ma aikata wasu aiyukan alheri, to bamu cancanci muyi kira zuwa ga waɗannan siffofi ba. Wannan kuskuren fahimta ce tamu. Tunda Allah Ya yi umurni da yin aikin ƙwarai, to Lallai ne mu yi umurni da aikata wannan aikin ko da kuwa mu ba ma aikatawa.
5. Mafi yawancin mu mun ɗauka cewa, makarantun koyar da addini da malamai waɗanda suka yi suna a fannoni daban-daban na Addini da littafan Addini da mujalloli na Addini, sun wadatar wajen tsamo ta'addancin dake faruwa a yau, babu ko shakka cewa sune suka tsare musulunci har kawowa yanzu, to amma a marra irin ta yanzu ba su wadatar ba, saboda idan muna son cin moriyar waɗannan kafafen wa'azi, to dole ne mu gina Imani mai karfi a cikin zukatanmu da Fulanin jeji da ingantacciyar ƙoƙarin kawo Islam a aikace.
Yanzu munsan maƙasudin faruwar wannan bala'i kuma munsan cutar dake addabar mu da maganinta. Don haka babu wata wahala domin yin amfani da magani domin samun lafiya da muka rasa. Idan muka iya amfani da abubuwan da muka tattauna a baya kuma muka yi aiki da basira, to duk hanyar kyara da muka ɗauka 'insha Allahu' za a cimma nasara.
Insha Allahu rubuta na gaba zanyi ne akan hanya da zata kaimu matakin cimma nasara
Muna rokon Allah madaukakin sarki ya bamu lafiya da zama lafiya da abinda lafiya zata ci. Āmīn ya Qādiyal Hājah.
https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1
No comments:
Post a Comment