Akashi na ɗaya mun tsaya a daidai inda Huzaifah (R.A) yaji amsar Annabi (S.A.Ws), sa'annan ya ƙara nuna damuwarsa ƙwarai da gaske, don haka sai ya ci gaba da irin tambayoyi na irin bala'in da za su aukamma Musulmi.
Huzaifah: 'Ya Rasulallah! Wai shin yaya za mu samu wani alherin bayan wannan masifa?'
Annabi: 'Ih, alheri zai sauka bayan wannan, toh amma sai dai cibiyoyin jama'a ba za su kai irin na da ba (ta fuskar fahimtar abubuwa na addini).
Huzaifah: 'Wata masifar kuma za ta auku bayan wannan alheri?'
Annabi: 'Ih, sai dai a wannan lokaci akwai mutanen da za su ɓatar da jama'a su jefa su wuta.'
Huzaifah: 'Me ka ga ya kamata in yi idan na iske wannan lokaci?'
Annabi: 'Idan ka taras da wata ƙungiyar Musulmi sun haɗe karkashin Amir guda to ka bi su. Idan ko ba haka ba, toh ka guji bin duk wasu 'yan ƙungiyoyi, gwamna ka koma ƙurya ko kuma ka koma gindin bishiya (watau daji) kayi ta zama a can, har mutuwa ta zo maka.'
A lokacin da Huzaifah (R.A) ke shirin barin duniya, ya yi ta kuka saboda damuwa da kuma turarradi. Jama'a suka ce da shi
Kana kuka ne don za ka bar wannan funiyar?
Ya ce: 'A'a ba wai ina kuka ba ne saboda haka, Ina ƙaunar in mutu. Ina kuka ne saboda a halin yanzu lokacin da nake shirin ƙaura daga nan duniya ban sani ba ko Allah Ta'ala Yana farin ciki da ni ko kuma a'a.'
Daga nan sai ya yi addu'a:
'Ya Allah! Wannan shi ne lokaci na ƙarshe a rayuwata (ta duniya). Ka san cewa a ko da yaushe ina ƙaunarka. Don haka ka albarkaci saduwa ta da kai.'
Ya Allah muma ka albarkaci saduwar mu da kai Kasa aljannar Firdausi itace mskomarmu.
*✍️Ahmad Musa
No comments:
Post a Comment