ABINDA YA KAMATA MUYI A DUK LOKACIN DA MASIFA TA SAME MU
UMMU SALMA (R.Ah), tafada cewa, wata rana Abu Salma ya dawo gida daga majalisin Annabi (S.A.Ws) sai ya koyamin wata magana dayaji daga bakin ANNABI (S.A.Ws), maganar data matukar farantamin rai sosai.
Yace dani: "Annabi (S.A.Ws) yace: "Idan wata musiba tasamu mumini sannan yayi istirja'i wato yace, 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un',sannan kuma ya hada da wannan addu'ar yace: "Ya Allah Kabani lada akan wannan musiba data sameni, Ka bani abinda yafi alheri daga wanda na rasa." Idan mutum yayi haka Allah (Swt) zai amsa masa addu'arsa.
Ummu Salma taci gaba da bada labari akan cewa: Sai na kiyaye wannan magana da mijina ya fadamin, da Allah Yayi masa rasuwa bayan nayi istirja'i, sai nayi wannan addu'a.
Ina kammala wannan addu'ar sai nace acikin zuciyata: oh! Ko ina zansamu mijin dayafi Abu Salma?
Wata rana bayan nagama takaba, sai Manzon Allah (S.A.Ws), yazo gidana yayi sallama. A lokacin ina jeme wata fata, sai nayi wuf na tashi na kimtsa sannan nace masa ya shigo.
Lokacin daya shigo na bashi wani pillow wanda cike yake da ganyen dabino sai ya zauna akai. Bayan mun gaisa sai ya bayyana mini cewa yana bukatar ya aureni.
Daya gama maganarsa sai na ce masa: Ya Rasoulullahi (S.A.Ws) bani da ta cewa indai kana sona, Amman inada kishi mai tsanani kada kaga wani abu daga gareni wanda Allah zai min azaba akanshi. Sannan kuma na tsufa kuma inada nauyi akaina (na 'ya'ya).
Da na gama bayani na sai MANZON ALLAH (S.A.Ws) yace; "Batun cewa kin fara tsufa ai nima hakan take, batun nauyin iyali kuma, ai nauyinki dana iyalinki duka akaina suke". Ina jin haka sai nace: "Ya Rasulullahi na sallamar".
Daga nannne MANZON ALLAH (S.A.Ws) ya aureta ta zama matarsa. Allah ya musanya mata Abu Salma da Mafi daukaka da daraja a doron kasa.
Sannan Uwar Muminai Nana Aisha (RA) tace, wata rana muna a cikin dare muna tare da Annabi (S.A.Ws), a cikin daki na Sai fitila ta dauke.
Nan take Naji Annabi (Saww) Yace, "Innalillahi Wa'Inna ilaihin Raji'Un" Sai nace, "Ya Rasulillahi Ina ce sai Abin bakin Ciki ya samu bawa zaiyi istirja'i." Sai Yace dani, "Yake Aisha Hakika duk abinda ya batawa bawa Rai ya kamata yayi istirja'i."
Ya Allah Ka taimake mu da Taimakonka a duk lokacin da wata musiba ta same mu mu zamo masu hakuri.
Babu Shakka Idan ka turawa Wani Wannan tunatarwa a duk lokacin da wata masifa ta same shi ya tuna yayi istirja'i to zaka samu lada koda baka duniyarnan. Daure ka turawa Wasu.
No comments:
Post a Comment