SABON SALO DA MASU GARKUWA DA MUTANE KEYI GURIN AMSAR KUDI
"Jama'a ga wata matsala babba da take faruwa, wani aboki nah yake sanar dani wannan labari, kuma wannan labari da gaske ne.
Wasu mutane sun zo wajen wani mutum wanda yake dealer ne na sayar da motoci a wajen sana'ar sa (car stand) sai suka yi cinikin wata mota Camry, akan kimanin kudi naira miliyan biyar.
Sai suka karbi Account number dinsa akan zasu yi masa transfer na kudin, sai ga naira miliyan uku sun shigo Account din dealer din, akan zasu ciko masa sauran kudin daga baya.
Bayan wani lokaci sai suka zo suka bashi hakuri akan ba zasu iya sayen motar ba, saboda rashin kudin da zasu cika, sai suka ce to ya basu miliyan biyu da dubu dari biyar, sun bashi saura naira budu dari biyar din saboda dawainiyar da yayi musu. Wannan mutum yana murna ya samu na banza.
Bayan kwana uku yana zaune a car stand dinsa sai ga Jami'an anti kidnapping da anti SARS sunzo suna tambayar sa ko shine aka tura masa miliyan uku yace ehh? Kuma shi bai san su ba, bai taba ganin su ba.
To wata hanya ce ta yan kidnappers da suke yi wajen amsar kudin fansa (ransom) daga yan uwan Wadan da suka kama (victims)
Dan ALLAH a yada wannan a sanar da yan uwa ayi yekuwa a masallatai da dukkan wurare dama gidajen radio, makarantu.
Haka nan kada ku yarda koda dan uwan ka ne ya nemi ka bashi Account number sai ka bincike shi, kuma idan wani amini gare ka ya bukaci zai tura maka kudi ko za'a tura masa kudi, idan kaga kudi ne masu yawa to kuyi rahoto a ofishin yan sanda mafi kusa domin kada wani tarko ne baku sani ba.
Idan da hali ka turawa wasu groups dan su fadaka.
ALLAH Ya karemu." Aameen
Daga. Zauren fiqhus Sunnah
No comments:
Post a Comment