3. TAKATACCEN TARIHIN UMMU KULTHUM (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)
Ita ce 'yar Annabi (S.A.Ws) ta uku daga cikin 'ya'yansa mata. Ta
auri Utaibah dan Abu Lahab, amma a lokacin ba su fara zama ba, lokacin da Utaibah ya sake ta bayan saukar da Sura Al-Lahab (watau Tabbat-Yada) kamar yadda aka riga aka ambata a baya. Bayan ya sake ta sai Utaibah ya zo wajen Manzon Allah (S.A.Ws) yana yi mishi rashin kunya.
Annabi (S.A.Ws) ya la'ance shi ya yi addu'a kamar haka:
Ya Allah Ta'ala! Ka hada shi da daya daga cikin karnukanka, don ya azabtar da shi.
Abu Talib wanda bai Musulunta ba, ya kadu da jin wannan la'anar, don haka sai ya ce da Utaibah:
Kai shi ke nan! Babu makawa, kashinka ya bushe.
Wata rana Utaibah yana tafiya tare da Abu Lahab cikin wata tawaga da za ta je Sham (Siriya), sai Abu Lahab duk da kafircinsa ya ce da jama'a:
Ni fa ina gudun la'anar Muhammadu. Don haka kowa ya lura da dana. Sun kuwa yada zango a wani wuri da yake da zakuna.
Jama'a duk sai suka yi lodin kayansu wuri daya, sa'annan suka sanya Utaibah ya kwanta saman kayan, kana su kuma sauran jama'a suka kewaye kayan. Zaki ya lallo6o cikin dare, inda ya sunsuna duk jama'ar da suke kwance jikin kayan. Daga nan sai ya tsallake jama'a inda ya hau sama wurin da Utaibah ke kwance. Da ya isa sai Utaibah ya yi ihu. Amma Ina! Kafin ka ce uffan, ya raba kansa da jikinsa.
Don haka wannan wata ishara ce gare mu, ya kamata lallai mu guji sa6awa bayin da Allah Ta'ala ke kauna. Annabi ya ruwaito cikin Hadisil-Kudusi, inda Allah Ta'ala ke cewa:
Duk wanda ke gaba da masoyina, zan shirya yaki da shi.
Bayan rasuwar Rukayyah (R.Ah), an sake auradda Ummu Kulthum (R.Ah) ga Sayyadina Uthman (R.A) a cikin watan Rabi'ul Awwal, shekara ta 3, bayan Hijirah.
Annabi (S.A.Ws) na cewa:
Na bayar da UMMU Kulthum aure ga Uthman bisa ga Umarnin Allah Ta'ala.
Ta rasu a cikin Watan Sha'aban na shekara ta 9, bayan Hijirah, ba tare da samun haihuwa ba. Bayan rasuwar ta an ji Manzon Allah (S.A.Ws) yana cewa;
Da ina da 'ya'ya mata 100, zan iya bayar da su aure ga Uthman (R.A) (daya bayan daya)
Insha Allahu rubutu na gaba akan Fatimah (R.Ah) yar Annabi (S.A.Ws) amma kafinnan zan dan yi rubutu akan wani al'amari da yake so ya haifar da barazana ga tsaron Nigeria. Muna kuma rokon Allah Ta'ala Ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen ya Qadiyal Haajah.
No comments:
Post a Comment