Tuesday, March 10, 2020

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...9..

 Sai Annabi Dauda(A.S)ya fara shirin gina masallaci.
   Sai ga  wani mutum salihi talaka ta zo masa domin ya jarrabe shi akan cewa shin da IKLASI za suyi wannan ginin? Sai wannan mutumin yace wa Bani Isra'ila ina da ha'k'ki a wannan gurin kuma ina da bu'katarsa, don haka bazai yiwu ku karemin ha'k'ki  naba, sai suka ce ya  kai wannan bawan Allah ai duk wani mutumin bani Isra'ila yana da ha'k'ki a wannan gurin kamar yadda kake da ha'k'ki kada kayi mana rowa kuma kada ka matsanta mana, sai yace ai ni na san ha'k'kina Amma ku baku san naku ba, sai sukace yanzu ka yadda ta dad'in rai ko sai mun 'kwata da 'karfi? Sai yace da su kunga irin wannan Hukuncin a ckin Hukuncin Allah ko Hukuncin Annabi Dauda(A.S)? Sai yace to zan daukaka 'kara zuwa wajan Annabi Dauda(A.S)ai kun yadda dashi, sai ya daukaka 'kara, sai Annabi Dauda(A.S)yace 'kasar sace , sai sukace To nawa zamu bashi mu amsa ya Annabin Allah? Sai yace ku bashi akuya 100, sai mutumin yace s karamin Ya Annabin Allah, sai Annabi Dauda yace ku bashi shanu 100, sai yace A 'karamin, sai yace ku bashi dawaki 100, sai yace a 'karamin , Domin zaku saye shine saboda Allah(S.W.T), Allah(S.W.T)kuma baya rowa, sai Annabi Dauda(A.S)yace Tunda ka fad'i haka, to ka yanke duk abinda za'a baka, sai mutumin yace zaka sayeshi misalin girmansa na zaitun da Dabino da inibi? Sai Annabi Dauda(A.S)ya ce Na'am, sai mutumin yace lallai ka saya don Allah(S.W.T)bakayi rowa ba, sai Annabi Dauda(A.S)yace  masa ro'ki duk abinda kake so, sai mutumin yace a gina min wani kango sannan a cikashi da zinare, ko azurfa, sai Annabi Dauda(A.S)yace shikenan, wannan ai mai sau'kine, sai mutumin ya juya gurin Bani Isra'ila yace dasu wannan shine mutumin da ya tuba, tacaccan tuba, sannan kuma ya cewa Annabi Dauda(A.S)ya Annabin Allah Wallahi Allah ya gafartamin zunubi d'aya shi yafi soyiwa a gareni akan komai, ni dai kurumna jarrabakane akan gina BAITUL MU'KADDIS.
    sai suka fara gina BAITUL MU'KADDIS, Annabi Dauda(A.S)ya kasance yana d'akko duwatsu a bayansa don yin ginin, suka yi aiki sosai har suka d'aga ginin sosai, sannan sai suka tsaya da aikin don gajiyawa, sai Allah(S.W.T) yayi masa wahayi sa cewa , wannan shine BAITUL MU'KADDIS, Amma bakai zaka 'karasa ginin shiba, d'an ka sulaiman zamu bashi mulki bayanka shine zai 'kara sa gininsa, amma ladan zai wanzu a gareka, sai Allah ya d'auki ran Annabi Dauda(A.S)sai Annabi sulaiman(A.S)ya hau milki ya 'karasa ginin.
     Annabi sulaiman(A.S)ya Tara mutane da Aljanu da shaid'anu , ya rarraba musu aikin ginin.
     Lokacin da suka gama ginin sai Annabi sulaiman(A.S)ya kusanci Ubangiji kusanta ta da cewa:-YA UBANGIJI KAINE KA BANI WANNAN MULKI BAIWACE AGARENI DAGA GAREKA, KUMA KA SANYANI KHALIFANKA A BAYAN 'KASA , KA GIRMAMANI DA SHI kAFIN IN ZAMA KOMAI, GODIYA TANA GAREKA , ALLAH INA RO'KONKA DUK WANDA YA SHIGA WANNAN MASALLACI YAYI SALLAH RAKA'A BIYU ACIKINSA YANA MAI IKHLASI GA ALLAH, KADA YA FITO FACE SAI KA GAFARTA MASA ZUNUBANSA GABA 'DAYA, YA UBANGIJI KADA WANI MAI ZUNUBI YA SHIGESHI FACE SAI KA GAFARTA MASA, KO WANI MAI TSORO FACE SAI AMINTA KO WANI MARAR KAFIYA FACE SAI YA WARKE, KO WANI TALAKA FACE SAI WADATA.
      ya kuma ce YA UBANGIJI IDAN KA AMSHI ADDU'ATA KUMA KA BANI ABINDA NA RO'KA KA SANYA MIN WATA ALAMA TA KAR'BAR KUSANCIN DA NAYI ZUWA GAREKA,
   sai wuta ta sakko daga sama ta cinye abinda yayi kusancin da shi, sannan ta koma sama.
      BAITUL MU'KADDIS ya kasance akan irin ginin da Annabi sulaiman(A.S)yayi, tsahon lokaci har sai da Lokacin da BUKTANASAR ya ya'ki   Bani Isra'ila aka jefamasa wata majaujawa ta rusashi aka d'auke duk kayan adon da akasa a jikinsa zuwa 'kasar Babila , Ba'a gyaraba har sai lokacin sayyadina umar d'an khad'd'ab (R.A)aka gyarashi da umarninsa, Allah(S.W.T)shine masani.

Zanci gaba insha Allahu.

Musha ruwa lpy.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)....8

GININ ANNABI SULAIMAN(A.S)

   ALLAH UBANGIJI(S.W.T)YA CE:-
TSARKI YA TABBATARWA WANDA YAYI TAFIYAR DARE DA BAWANSA(Annabi mai tsira da amincin Allah) a d'an yanki na dare, cikin mudda 'kan'ka nuwa daga masallaci mai Alfarma (MAKKA)izuwa masallaci mafi nisa(BAITUL MU'KADDAS),  "An ambaceshi mafi nisa saboda nisansa daga gareshi" wanda mukayi Albarka Daura da shi "duk Annabawa masu tsira da Amincin Allah(S.W.T)ya yarda dasu, da 'koramu da 'ya'yan itatuwa don mu nuna masa mamakin ikonmu.
      Ance Allah(S.W.T)ya yiwa Al'karyar da Baitul Mu'kaddas yake acikinta Albarka ta ruwan dad'i da 'ya'yan itatuwa da bishiyoyi iri-iri.
     An rawaito cewa, Manzon Allah(S.A.W)Ya ce:-FAN BAITUL MU'KADDAS TA KASANCE AKAN WATA BASHIYAR DABINO DAGA CIKIN BISHIYOYIN BADINON ALJANNA, ITA KUMA WANNAN BISHIYAR DABINON TAKASANCE AKAN WATA KORAMA, DAGA CIKIN KORAMUN ALJANNA, A WAJAN WANNAN 'KORAMUN ANAN ASIYA "YAR MAZAHIM DA MARYAM  "YAR IMRANA (R.T.A)SUKE TSARA KAYAN ADO NA MUTANE 'YAN ALJANNA RANAR ALKIYAMA" daga khakil  d'an ma'adan daga ubaidata d'an samit.
     Farkon ginin Baitul Mu'kaddas da kuma siffar ginin kamar yadda aka ambata.
Shine:-
   Allah UBANGIJI(S.W.T)yayi albarka ga tsatson Annabi Ibrahim(A.S)ta wajen yawa har sun kasance basa 'kirguwa, a zamanin Annabi Dauda(A.S), Annabi Dauda(A.S)ya zauna acikinsu lokaci mai tsaho a 'kasar falasd'in, sai yaga suna 'karuwa adadinsu yana yawaita a kowace rana sai abin ya bashi mamaki, sai yayi nufin yasan yawansu,sai  yayi unarni da a 'kidayasu, amma hakan bai yuwuba, sai Allah(S.W.T)yayi masa wahayi da cewa:- KASAN CEWA NA YIWA MAHAIFINKA IBRAHIM (A.S)AL'KAWARIN RANAR DANA UMARCE SHI DA YA YANKA 'DANSA, YAYJ HAKURI YA CIKA UMARNI NA , AKAN CEWA ZAN SA ALBARKA ACIKIN ZURIYYARSA, HAR SAI SUN KAI YAWAN ADADIN TAURARI, TA YADDA BAZA'A IYA 'KIDAYA ADADIN SUBA, SAI KAI KUMA KAYI NUFIN SANIN ADADINSU, TO KASANI BABU WANDA ZAI SAN ADADINSU SAI NI, AMMA ZAN JARRABESU DA 'KARANCIN YAWA DOMIN WANNAN MAMAKIN DA KAKE NA YAWANSU YA FAKU DAGA GAREKA.
        Sai ALLAH(S.W.T)ya bawa bani Isra'ila za'bi ,akan ya jarrebesu da yinwa ko da fari na shekara uku, ko kuma ya sallad'a ma'kitansu akansu har tsahon wata uku, ko kuma ya sa musu mutuwa ta kwana uku, sai Annabi Dauda(A.S)ya basu labari da abinda Allah(S.W.T)yayi masa wahayi da kuma za'bin da ya basu, sai sukace ai kai ne mafi sani daga garemu, kaza'bar mana abinda yafi sau'ki, kayi duba sosai, amma kasan cewa bamu da ha'kuri wajen yunwa, kuma sallad'a ma'kiya Al'amarine mabayyani a garemu, idan dai babu makawa sai an jarrebemu to mutuwar tafi, domin a hannunsa take ba a hannun wanin saba, sai aka umarci Annabi Dauda(A.S)da ya gaya musu suyi shirin mutuwa, suyi wanka susa turare su kuma sa likkafani su warwatsu a gurin Baitul Mu'kaddas kafina gina shi, sai ya umarce su dasuyi kan-kan da kai ga Allah(S.W.T)ko ya ji'kansu, sai Allah(S.W.T)ya aiko musu da Annoba, sai kaga mutane dubunnai sun mutu a dare d'aya, wanda ba'asan adadin suba, ba'a daina binne wad'anda suka mutuba saboda yawansu sai bayan wata d'aya.
      Lokacin da rana ta biyu ta kewayo sai Annabi Dauda(A.S)ya fad'i yana mai sujjada yana rokon Allah(S.W.T)akan ya yaye wa Bani Isra'ila wannan musibar, sai Allah (S.W.T)ya amshi addu'ansa, ya d'auke musu wannan Annobar suka daina mutuwa,sai Annabi Dauda(A.S)ya umarci Bani Isra'ila dasu godewa Allah saboda Baiwar da yayi musu, sai sukace dame zamu gode masa?sai yace ku gina masallaci a gurin da yayi muku Rahmarsa, saboda wad'anda za su zo bayanku su ringa tuna Ubangiji da ambatonsa, sai Annabi Dauda(A.S)ya fara shirin gina masallaci sai ga wani mutum Salihi talaka ya zo masa domin ya jarrebe shi akan cewa shin da IKHLASI za suyi wannan ginin?

ZANCI GABA INSHA ALLAHU.

JUMA@KAREEM

RAMADHAN MUBARAK.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)....7.

 BIRNIN DA ANNABI SULAIMAN(A.S)YAKE TAFIYA DA SHI ACIKIN ISKA.

   Annabi sulaiman(A.S)yana da birni(gari)wanda yake tafiya a kansa an ginashi da 'kwarir girmansa kamu DUBU GOMA(10,000)acikinsa akwai tarago guda biyu, acikin kowane tarago akwai duk abinda miskinai suke bu'kata,tarago na 'kasa yafi 'karfe kauri da 'karfi karago na sama kuma yafi ruwa garai-garai da sirantaka, wanda yake cikinsa yana ganina abinda yake wajen taragon saboda garai-garai d'insa, acikinsa akwai wata 'kubba fara, akansa akwai wata tuta fara wacce take haskakawa askarawansa haske idan dare yayi.

KUJERAR ANNABI SULAIMAN(A.S)

     Allah Ubangiji(S.W.T)yana cewa:-"MUNJEFA JIKI KAN GADONSA,"suratun sad aya ta 33.
      An ruwaito cewa Annabi sulaiman(A.S)ya umarci shaid'anu da suyi masa kujera wacce zai ringa zama akai don yin hukunci wato Al'kalanci, ya umarcesu da suyi mata 'kira wacce idan wani mai 'Barna ko wani mai shaidar zur ya ganta za ta yi masa kwarjini, ya kuma tsorata.
      Sai suka 'kera masa kujera da Hauran Giwa suka kuma kewaye ta da lu'u-lu'u da zubardaji da dai nau'i-nau'i na jauhari, suka kuma kewayeta da bishiyoyin dabino na zinare ganyanta na ya'kutai koraye, akan bishiyar dabino guda biyu akwai da'wisu na zinare, akan sauran bishiyoyin kuma akwai wani tsuntsu da ake kira Nasran shima anyishi da zinare sashinsu na kallon sashi suka kuma sanya wasu zakuna guda biyu agefen kujerar na zinare, akan kowane d'aya daga cikinsu akwai wani ginshi'ki na zubardaju kore, sun kuma yiwa wannan bishiyoyin ado da filawoyi na alfarma, sai suka sanyawa kowace fulawa narkakkun ya'kutu wanda zai ringa yiwa wannan gadon inuwa da kuma sauran bishiyoyin wannan kujera, sannan kuma akayi matattakala wacce idan Annabi sulaiman(A.S)yayi niyyar hawa sai ya d'ora 'kafarsa akan matattakalar ta 'kasa sai kurum tayi sama dashi har kan kujerar, kuma sai ya d'ora 'kafarsa akan matattakalar ta ringa juyawa da shi idan yayi nufin hutawa, su kuma wad'annan d'awisan da Nasran d'innan su ringa bud'e fuka fukansu, su kuma wad'annan zakuna guda biyu suna shimfida hannayensu suna dukan 'kasa da kunnuwansu, haka suke tayi akowace matattakala har sai Annabi sulaiman(A.S)ya zauna daidai akan kujerarsa ta mulki, sannan kuma sai wad'annan tsuntsaye guda biyu nakan dabino sai su fara zuba turaren muski da ambar agareshi, sannan Sai wata Kurciya ta zinare ta miko masa littafi daga cikin wasu ginshi'kai najikin kujerar sai ta bud'e masa littafin, sai ga fara karantawa mutane don yin hukunci a tsakaninsu, su kuma manya manyan mutanen bani isra'ila suna zaune akan wasu kujeru na zinare da azurfa a hagun sa, su dubu(1000)suna kewaye dashi, tsuntsaye sunyi musu inuwa, su kuma mutane suna zuwa gurinsa domin yayi musu hukunci, idan wani mai yin shaida yazo sai wannan kujera ta rabe biyu sai zakunan nan su fara dukan  'kasa sa kunnuwansu, su kuma tsuntsaye subud'e fuka fukansu, sai wanda ya zo shaidannan ya tsorat tsoro mai tsanani bazai shaida ba sai akan abinda ya tabbatar, babu zancen shaidar zur.

     Wannan shine kad'an daga cikin abubuwan mamaki na kujerar Annabi sulaiman(A.S).
    Lokacin da Allah(S.W.T)ya d'auki ran Annabi sulaiman(A.S)sai sarki BUKHUNASAR ya aika da a d'akko wanann kujerar to da aka d'akkota, sai yayi nufin ya ringa hawanta, amma sai dai bashi da ilmin sanin yanda take, lokacin da yayi niyyar ya hauta ya d'ora 'kafarsa akan matattakala ta farko sai wannan zakin ya daga hannunsa na dama yadaki 'kafarsa duka mai tsanani, sannan ya jefashi sama, bai gushe yana ta yin sama ba , har sai da ya mutu, ita kuma kujerar aka barta anan har saida wani sarki daga cikin sarakuna da ake kira ('Kaddashi 'Dan Saddad)ya   ya'ki  garin da wannan kujera take, ya kuma rusa mulki MUKHTANASAR d'in, sai ya maida kujerar Baitul Mukaddas, babu wani sarki da ya ta'ba zama akanta, sai kuma aka sata a 'kar'karshin wani fan dutse , sai ta 'buya, har yanzu babu wanda yasan inda take sai Allah, ALLAH SHINE MASANI.

ZANCI GABA INSHA ALLAHU.

RAMADHAN MUBARAK.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...6

 Sai Allah(S.W.T)Ya umarci Annabi sulaiman(A.S)da ya sauka yayi sallah acikinsa, kuma ya kusance shi da wani abin kusanta, sai Annabi sulaiman(A.S)ya aikata haka, ance Annabi sulaiman(A.S)ya yanka ra'kuma dubi biyar, da Bajimayan shanu dubu biyar,da akuyoyi dubu ashirin, a daf da ka'aba ,sai Annabi sulaiman(A.S)ya gaya wa wasu manya daga cikin mutanansa cewa, wannan gurin wani Annabi Balarabe zai fito daga gareshi, za'a bashi taimako da nasara ga duk wanda yayi taurin kai agareshi, kuma takobi zata kasance a wuyan duk wanda ya sa'ba masa, kuma kwarjininsa zai kai musalin tafiyar wata guda, wanda yake a kusa da wanda yake   a nesa duk d'aya ne a gurinsa, baya jin tsoran zargin mai zargi acikin bin Ubangiji, Aljanna ta tabbataga wanda ya riskeshi kuma ya gasgatashi, sai suka ce tsakaninmu da shi zai shekara nawa ya kai Annabin Allah? sai yace zai kusa shekara dubu(1000).
        Sai Annabi sulaiman(A.S)ya cigaba da tafiya har ya isa wani kwari da ake kira (WADIS-SADID)sannan kuma ya 'karasa kwarin wannan tururuwar wanda shima ake kiransa(WADIN NAMLI)sai wannan tururuwa ta tashi tana tafiya tana d'an rangaji, ya kasance girmanta kamar girman kura , ma'abociyar fukafukai guda biyu.
    Malamai sunyi sa'bani a kan sunanta wasu suka ce  sunanta  (DAKHIYA)wasu kuma sukace sunanta(KHIRMA), sai tayi kiran 'yan uwanta tururuwai saboda rundunar Annabi sukaiman(A.S)da ta gani, shine fad'in Ubangiji(S.W.T)cewa:-" YA KU JAMA'AR TURURUWAI! KU SHIGA GIDAJANKU KADA SULAIMAN DA RUNDUNONINSA SU KARKARYA KU, A HALIN SU BA SU SANI BA." suratun namli.
      Dama kamar yadda muka fad'a cewa babu wata halitta da zatayi magana face sai iska ta dakkota ta kawo wa Annabi sulaiman(A.S), aka ce Annabi sulaiman(A.S)yaji maganar wanann tururuwar misalin tsawon mil uku(3-m), sai Annabi sulaiman(A.S)yayi murmushi saboda jin maganar wannan Tururuwar, sai yace Ubangijina ka cusa min in godewa ni'imarki wacce ka ni'imta ta gareni da kuma mahaifana guda biyu, kuma in aikata aiki na 'kwarai, wanda kake yarda da shi kuma ka shigar dani rahamarka acikin bayinka managarta.
       Haka tsarin maganarsa tazo acikin Alkur'ani mai girma cikin suratun Namli aya ta 19. Awasu sauran 'kissa kuma akace, Annabi sulaiman(A.S)lokacin da yaji zancen wannan tururuwar sai ya sakko zuwa gareta, sai yace; azo da ita, sai aka zo da ita, sai yace da ita, saboda me wad'annan Tururuwan suka tsorata sunji ance ni azzalimine? Saboda me kikace kada sulaiman da rundunarsa su karkaryaku? Sai Tururuwar tace ya Annabin Allah bakaji a cikin maganata nace, "A HALIN BAKU SANI BA." Kuma duk da cewa na san banyi nufin karkaryawa na jikiba ina nufin karkaryawa na rai, saboda naji tsoro kada suyi burin abinda Allah yabaka, sai su fitinu su kuma shagala da kallonka akan TASBIHIN DA SUKEYI.
     Sai Annabi sulaiman(A.S)yace wa'azantar dani yake Tururuwa, sai Tururuwa tace kasan ko saboda me ake kiran sunan mahaifinka da DAUDA? Sai yace a'a sai tace da shi ana kiransa da Dauda saboda yayi maganin raunin da zuciyarsa take dashi, sai ta kuma cewa, Shin kasan ko saboda me ake kiranka da sulaiman? Sai yace a'a sai tace saboda kai ku'butaccene acikin abin da aka baka, saboda ku'butar zuciyarka, kuma ha'k'kine a gareka ka had'u da mahaifinka Dauda, sannan sai ta kuma cewa kasan ko saboda me Allah (S.W.T)ya hore maka iska? Sai yace a'a sai tace domin duniya iskace, sai Annabi sulaiman(A.S)yayi murmushi saboda maganarta, yana mai mamaki, shine wannan addu'ar wacce muka fad'a abaya.
        Nana Maimuna(R.A)ta bada labarin cewa Manzon Allah(S.A.W)ya hana a kashe masu tafiya akan 'kasa guda hud'u 4 daga cikin kwari da tsuntsaye, acikinsu akwai Tururuwa.
    Yana daga cikin abinda Allah(S.W.T)ya hore wa Annabi sulaiman(A.S)Horewa dayayi masa ta mutane da Aljanu da Tsuntsaye da 'kwari da shaid'anu sunayi masa aiki na duk abinda yaga dama, shine fadin Ubangiji(S.W.T)cewa:-
        "KUMA DAGA ALJANNU(MUKA HORE MASA)WANDA DA SUKE AIKI NAN GAMA GARESHI DA IZNIN UBANGIJI WANDA YA KARKATA DAGA CIKINSU, DAGA UMARNINMU SAI MU 'DAN'DANA MASA DAGA AZABAR SA'IRA"suratun saba'i aya ta (12).
      Haka Allah (S.W.T)ya wakilta wani mala'ika, wanda a hannunsa akwai wata bulala ta wuta, duk wanda Ya'ki bin umarnin Anmabi sulaiman(A.S)daga acikin Aljanu, sai ya dokeshi da ita nan da nan ya'kone.
        Daga cikin Aljanu akwai wad'anda suke nutso cikin ruwa, suke fito masa da nau'i nau'i na ma'adanai kamar lu'u lu'u da zubarjadi da ya'kutai, wad'annan Aljanu sune farkon wad'anda suka fara irin wannan aikin.

Zanci gaba insha Allahu

Musha ruwa lpy.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...5

 Abdullahi d'an Hamisu ya bada labari da isnadinsa, daga d'an mas'ud daga mahaifinsa, yace mun kasance tare da Manzon Allah(S.A.W)halin wata tafiya sai muka wuce ta wajan wata bishiya akanta akwai wasu 'ya'yan Kurciya guda 2 sai muka d'aukesu, sai wannan Kurciyar ta kawo 'kara gurin ma'aiki(S.A.W)sai manzon Allah(S.A.W)yace :-waye ya afkawa 'ya'yan wannan Kurciyar? sai mu kace mu ne, sai Manzon Allah(S.A.W)ya ce ku maida su gurbinsu.
        Ance Annabi sulaiman(A.S)ya ta'ba wuce wata turuwa akan hanyarsa ta zuwa mukibi, sai tururuwar take cewa, tsarki ya tabbata ga Ubangiji maigirma, mai yafi girma daga abinda ya bawa iyalan Annabi Dauda(A.S), sai Annabi sulaiman(A.S)yayi murmushi saboda maganar da wannan tururuwa ta fad'a, sai ya gayawa rundunarsa wannan magana, sai sukayi mamaki, sai Annabi sulaiman(A.S)Ya ce:-in baku labarin abinda yafi wannan ban mamaki? sai sukace na'am, sai yace:-wannan tururuwa ta kasance tana cewa, Kuji tsoron Allah a fili da 'boye, da kuma kyakkyawan nufi a gareshi ahalin wadata da Takauci, da kuma adalci lokacin fushi da lokacin yarda.
       An rawaito cewa, Annabi sulaiman(A.S) ya fita ro'kon ruwa a tare da shi akwai mutane da Aljanu, sai suka wuce ta gurin wata Tururuwa ta bud'e fuka fukanta ta d'aga hannayanta tana cewa, Ya Ubangiji mu halittace daga cikin halittunka ba mu da wadatuwa ga arzikinka, kuma kada ka kamamu da zunuban 'yan Adam ka shayar da mu, sai Annabi sulaiman(A.S)yace wa wad'anda suke tare dashi ku koma Ha'ki'ka   za'a shayar da ku da addu'ar wanin ku.
        Akwai kuma wata 'Kissa ta wadin Namli, wacce Allah Ubangiji(S.W.T)yace :- "KUMA AKA TATTARA, DOMIN SULAIMAN, RUNDUNONINSA, DAGA ALJANU DA MUTANE DA TSUNTSAYE, TO SU ANA KANGE SU(GA TAFIYA) "suratun Namli.
      HAR A LOKACIN DA SUKAJE KAN RAFIN TURURUWA WATA TURURUWA, TACE, YA KU JAMA'AR TURURUWAI ! KU SHIGA GIDAJANKU,KADA SULAIMAN DA RUNDUNONINSA SU KARKARYA KU, A HALIN BASU SANI BA"suratun Namli.
        Sha'abi da ka'ab sukace, Annabi sulaiman(A.S)ya kasance idan zai yi tafiya yana d'ora Ahlinsa da masu yi masa hidimada sakatarorinsa akan abin hawansa, su kuma dabbobi suna tafiya a gabansa tsakanin sama da 'kasa iska tana ri'ke da su,sun tafi zuwa yaman, sai suka bi ta madina wato birnin Manzon Allah(S.A.W)a yanzu, sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce, wannan shine gidan hijirar manzon Allah(S.A.W)wanda za'a aiko a 'karshen zamani, Aljanna ta tabbata ga wanda ya bishi kuma yayi imani da shi, sannan sai suka isa harami sai suka ga gumakan da ake bautawa, wad'anda ba Allah(S.W.T)ba, sun kewaye d'akin Allah, lokacin da Annabi sulaiman(A.S)ya wuce d'akin ka'aba, sai d'akin ka'aba ya kama kuka, sai Allah(S.W.T)yayi wahayi izuwa d'akin ka'aba da cewa, me yasa kake kuka,? sai d'akin ka'aba yace, ya Ubangiji wani Annabi ne daga cikin Annabakawanka, kuma tare da mutane daga cikin masoyanka, sun wuce ta kaina ba su sakko gareni ba, kuma ba suyi sallah a guri na ba, kuma ba su ambace ka a da'irata ba, kuma wad'annan gumakane a kewaye dani ake bauta musu bayan kai, sai Allah(S.W.T)yayi wahayi a gareshi da cewa kada kayi kuka da sannu zan cikaka da fuskoki masu sujjada a gareni, kuma zan saukar da Alkur'ani a cikinka,kuma zan aiko wani Annabi daga cikin Annabawa a 'karshen zamani daga gareka. mafi soyuwa a gare ni,kuma zan sanya wasu bayi a cikinka daga cikin halittuna masu yin bauta, kuma zan wajabtawa bayina wani abin wajabtawa wanda za suyi ta kwad'ayin tahowa zuwa gareka, kuma zan tsarkake ka daga masu bautar gumaka da shaid'an........
zanci gaba insha Allahu.

Asha ruwa lpy.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...4..


     Sannan Dan Futuhawaihi ya bada labari da isnadinsa daga Muhammad
d'an ka'ab cewa, Annabi sulaiman(A.S)yana da askarawa sun kai farsakhi d'ari 100,ishirin da biyar daga cikin na mutane ne, ishirin da biyar kuma na aljanu ne, ishirin da biyar kuma na 'kwari ne, ishirin da biyar kuma na tsuntsaye ne, yana kuma da gidage guda dubu 1000 na 'kawahir, acikin gidajan akwai gado d'ari uku 300 da mata d'ari bakwai 700, yana umar tar iska ta d'auke shi tayi yawo dashi, sai rannan yana yawo a tsakanin sama da 'kasa, sai Allah(S.W.T)ya yi masa wahayi da cewa:-
           HA'KI'KA NA 'KARA MAKA ACIKIN MULKINKA DA CEWA BABU WANDA ZAI YI MAGANA DAGA HALITTU DA WANI ABU FACE SAI ISKA TA ZO MAKA DA SHI TA BAKA LABARI.
       Yana daga cikin horewar da Allah(S.W.T)ya yiwa Annabi sulaiman(A.S) sanar da shi zancen tsuntsaye, kamar yadda Allah yake fad'a cewa:-
       DA FAD'AN ANNABI SULAIMAN(A.S) "YA KU MUTANE AN SANAR DA MU NAGANAR TSUNTSAYE." suratun namli.
         Dan Futuhawaihi yace da isnadinsa daga d'an ka'ab, idan DAWISU yayi kuka a gaban Annabi sulaiman(A.S)sai yace kun san abinda yake cewa? sai suka ce a'a yace ai cewa yake , kamar yadda kayi haka za'ayi maka.
      Alhuda-huda ma dayayi kuka sai Annabi sulaiman(A.S)yace kun san abinda yake fad'a?sai sukace a'a sai yace da su cewa yake yi, duk wanda bai jin 'kai ba, to shima ba za'a ji 'kan saba.
    kurciya ma tayi kuka sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce kun san abinda take cewa? sai sukace a'a, sai yace ai cewa take yi, tsarki ya tabbata ga Ubangiji mad'aukaki cikin samansa, da kuma cikin'kasan sa.
      kwado shi ma cewa yake yi SUBHANA RABBIYAL 'KUDDUSU, tsarki ya tabbata ga Ubangiji mai tsarki.
       Manzon Allah(S.A.W) ya ce :-idan zakara yayi cara cewa yake yi(UZKURULLAHA YA GAFILUN)ma'ana ku ambaci Ubangiji ya ku marafkana.
      Annabi sulaiman(A.S)yaci gaba da gaya musu cewa idan DAI'DAWI yayi kuka to cewa yake yi, ko wane rayayye matacce ne, kuma ko wane sabo tsoho ne.
     Annabi sulaiman(A.S)yaci gaba da fassara musu kukan tsuntsaye kala-kala, daga ciki akwai wanda yake cewa ku nemi gafara ya ku masu zunubi, akwai mai cewa ku gabatar da Alkhairi domin zaku sameshi, akwai mai cewa, kaicon wanda duniya ta zama abar bakin cikinsa, akwai mai cewa Mulkin Ubangiji ya daidaita, akwai mai cewa tsarki ua tabbata ga abin ambato a kowane guri, da dai sauransu domin kowace irin hakitta ka gani to akwai manufar halittar ta a wajan Ubangiji, kuma zamu iya lura da cewa duk sauran hilittun Ubangiji ashe suna yiwa 'Dan Adam gargad'ine da kuma tunatarwa akan MAHALICCI ALLAH.
zanci gaba insha Allahu..

asha ruwa lpy.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)....3..

 Allah Ubangiji(S.W.T)ya ce:-(KUMA SULAIMAN YA GAJI DAUDA)suratun namli.
    Abin nufi anan shine ya gaji Annabtar sa, da hikimar sa, da ilmin sa, Duk da cewa Annabi Dauda(A.S)yana da 'ya'ya goma sha tara(19).
      MU'KATIL yace:- Annabi sulaiman(A.S)ya kasance akan mulki mafi girma ga na mahaifinsa Annabi Dauda(A.S)da kuma iya hukunci, shi dai Annabi Dauda(A.S)ya kasance mai yawan ibada ne akan d'ansa Annabi sulaiman(A.S), kuma Allah (S.W.T)ya bashi mulki da hikima yana 'Dan shekara goma sha uku(13),Shima yana daga cikin mutum hud'u wad'anda suka mulki duniya gaba d'aya.
     Annabi sulaiman(A.S)ya kasance fari kuma mai jiki mai haske,kuma kyakkyawa, mai yawan gashi,yana sa fararen tufafi, kuma ya kasance mai yawan tsoran Allah(S.W.T) kuma mai tawadhi'u yana cud'anya da miskinai, kuma yana zama dasu, yana cewa miskini ya zauna da maikinai.
       Mahaifinsa Annabi Dauda(A.S)ya kasance yana shawara da shi a lokacin mulkinsa akan al'amura masu yawa, duk da cewa 'karami mai 'kananan shekaru, amma yana da cikakkyan hankali da ilmi.
          Allah Ubangiji(S.W.T)ya ke'benci Annabin sa Annabi sulaiman(A.S)da wasu darajoji da kuma kyaututtuka na baiwa, Ubangiji yana cewa:-
(HAKIKA MUN BAI WA DAUDA DA SULAIMAN ILMI, KUMA SUKA CE GODIYA TA TABBATA GA ALLAH,WANDA YA FIFI TA MU AKAN MAFI YAWA DAGA BAYINSA MUMINAI.)suratun namli;
     Kuma Ubangiji ya fad'a acikin Al'kur'ani mai girma tana mai bada labari akan Annabi sulaiman(A.S):-
YACE"YA UBANGIJI:KA GAFARTA MINI, KUMA KA BANI MULKI WANDA BAI KAMATA GA KOWA BA BAYANA".
"LALLAI KAI NE MAI YAWUN KYAUTA".
      Annabi sulaiman(A.S)yayi wannan addu'a ne Domin kada wani yayi alfahari da sarauta a bayansa, Ya halaka kuma ya halakar da wani,saboda sarauta itace asalin girman kai da alfahari.
      sai Allah ya amsa addu'ar sa ya kuma girmamashi da wasu abubuwa wanda Allah bai ta'ba horewa wani su ba, daga cikin hakittar sa ba kafin Annabi sulaiman(A.S)daga cikin hotewar da Allah(S.W.T)yayi masa daga iska, Ubangiji mad'aukakin sarki yana cewa:-
"SABODA HAKA MUKA HORE MASA ISKA TANA GUDU DA UMARNINSA, TANA TASHI DA SAUKI,INDA YA NUFA."Suratu..
       Malamai suka ce an hore masa iska a matsayin dawakan da ya yanka domin Allah, Saboda Annabi sulaiman(A.S)ya yanka dawakan ne saboda kallonsu ya hana shi sallah, wacce ita sallar farillace ta dole a kansa, amma tattalin kayan ya'ki farillace ta wani zai iya d'aukewa wani.
    sannan kuma an hore masa Aljanu domin niyyarsa ta samun 'ya'ya masu jihadi domin Allah.
     Malam muhammad Dan Is'hak yace, Annabi sulaiman(A.S)ya kasance mutum ne mai yawan ya'ki Baya iya zama ba tare da ana gwabza ya'ki ba,dan baya iya jin d'uriyar wani sarki a sassan duniya,face sai ya ya'ke shi, kuma ya nuna masa karfin mulki sa, Ya kasance idan yayi nufin ya'ki yana sa askarawansa su 'kera masa wani abu kamar girji na katako sannan sai a d'ora masa gadonsa akai sannan duk sauran jama'a da dabbobi su hau a kuma zuba kayan ya'ki kala-kala akai, bayan an gama shirya komai sai ya umarci iska ta d'aukeshi zuwa inda ya nufa,  an ce suna yin tafiyar wata a yammaci d'aya, kuma suna yin tafiyar wata a safiya d'aya, tana tana tafiya da shi duk inda ya so, shine fad'in Ubangiji(S.W.T):-
"KUMA GA SULAIMAN, MUN HORE MASA ISKA,TAFIYARTA TA SAFIYA DAIDAI DA WATA,KUMA TA YAMMA DAIDAI DA WATA."Suratu sabi'i.

......Zanci gaba insha Allahu

JUMA@ KAREEM..
 RAMADHAN KAREEM..

MUNSHA RUWA LAFIYA.