Monday, December 4, 2023

SHAHADAR ANAS BIN NADR (R.A) KASHI NA BIYU

SHAHADAR ANAS BIN NADR (R.A) KASHI NA BIYU A kashi na ɗaya mun tsaya a dai-dai inda "Wannan umurni dai na Manzon Allah (S.A.Ws) kurum har zuwa lokacin da ake yin fada ne". Don haka masu dawakai da suka hango babu wanda ke lura da baya, sai suka yunkuro a guje, inda suka samu suka kutsa, kana suka shammaci Musulmi ta baya, waɗanda suka dukufa wajen kwasar ganima. Ana cikin wannan hali ne fa, Anas (R.A) ya hango Sa'ad bin Ma'az (R.A) yana kokarin wucewa ta gabansa. Nan take ya yi masa tsawa, inda ya jawo hankalinsa yana mai cewa; 'Ya Sa'ad! Ina ka ke shirin zuwa? Na rantse da Allah Ta'ala, na jiyo kamshin Aljannah ya na kunnowa daga Dutsen Uhudu Ai kuwa faɗın haka keda wuya, sai ya yi kururuwa, inda ya yi tsalle, ya kutsa tsakiyar filin daga, aka yi ta ɗauki ba daɗi tare da shi, har sai da ya yi Shahadah. Bayan kammala yakin an yi daga-daga da jikinsa.
Inda aka yi ɗai-ɗai da shi. Wanda ta kai, sam babu wanda zai iya gane shi, sai kurum kanwarsa ce ta shaida shi, shima bayan da ta dubi yan yatsunsa. Irin rauninkan da aka yi masa wanda ya kama daga na kibbau zuwa na takubba, sun fi tamanin. Don haka dai waɗanda suka yi jihadi fi sabilillah, tsakani da Allah, tare da juriya da hakuri, har kamshin Aljannah suke jiyowa tun daga nan duniya, kamar yadda wannan bawan Allah Anas (Radhiyallahu anhu) ya jiyo kamshin Aljannah MU HAƊU A RUBUTU NA GABA AKAN Yarjejeniyar Hudaibiyyah Da Kuma Labarin Abu Jandal Da Kuma Abu Basir (R.A). Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️ Ahmad Musa

Sunday, December 3, 2023

TAMBAYA NA TAKWAS (0008) A WANI SHEKARU NE MATA SUKE FARA YIN HAILA DAKUMA SHEKARUN DA SUKE DAINAWA

TAMBAYA NA TAKWAS (0008) A WANI SHEKARU NE MATA SUKE FARA YIN HAILA DAKUMA SHEKARUN DA SUKE DAINAWA Yawancin mata suna fara yin haila ne daga shekara 12-50 amma wani lokacin mace tana iya yin haila kafin shekara 12 ko kuma bayan shekara 50, wannan ya danganci yanayinta da kuma wurin da take zaune, da abincin da take ci. Malamai sun yi saɓani: shin akwai wata shekara ta musamman da mace take fara haila ko kuma take dainawa, ta yadda jinin da ya sameta kafin wannan ko bayan wannan shekarun ba za'a kira shi jinin haila ba? Darimi -Allah Ya yi masa rahama-ya ce bayan ya ambaci saɓanin da aka yi: "Wannan duk kuskure ne a wajena, domin abin lura shi ne samuwar jinin, don baka duk lokacin da aka samu jinin a cikin kowacce shekara ne ya wajaba a sanya shi ya žarna haila", abin da Darimi ya faɗa shi ne daidai saboda Allah da ManzonSa sun rataya hukunce hukuncen jinin haila ne da samuwarsa, ba su kuma iyakance wasu shekaru na müsamman ba, kamar yadda aya ta (222) a suratul bakara take nuni zuwa hakan, wannan yake nuna mana iyakance shi da lokaci na musamman yana bukatar dalili ne daga litttafi Allah ko daga Sunnar ManzonSa, ba'a kuma samu ba. Don neman karin bayani duba: Dima'uɗɗabi'iyya shafi na :6 Allah ne Mafi sani Kushiga nan domin samun amsar tambaya na 0007 👉👇 https://ahmadmusainc.blogspot.com/2023/12/tambaya-na-0007-mecece-hukuncin.html

Saturday, December 2, 2023

TAMBAYA NA (0007) MECECE HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BUKATA A BANDAKI ?

TAMBAYA NA (0007) MECECE HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BUKATA A BANDAKI ? To Malamai sun yi saɓani akan wannan hukuncin, Abu- hanifa ya hana hakan, Malik ya tafi akan cewa mutukar a gida ne to babu laifi, saboda hadisin Abdullahi dan Umar wanda yake cewa: "Na hau ɗakin Hafsa sai na ga Annabi (S.A.Ws) yana biyan bukatarsa, yana fuskantar Sham ya kuma juyawa alkibla baya", kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (145). Saidai abin da ya fi shi ne kar mutum ya fuskanci Alkibla, ko da a gida ne, saboda hadisin Abu-ayyub wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa: "Idan kuka zo yin bahaya to kada ku fuskanci alkibla kada kuma ku bata baya" Bukhari a hadisi mai lamba ta: (394) d aMuslim a hadisi lamba ta: (264), Tabbas barin kallon alkibla yayin biyan bukata shi ne ya fi, saboda hadisin da ya gabata da kuma fita daga sabanin Malamai, don haka idan mutum zai gina masai a gidansa zai yi kyau ya kautar da ita daga alkibla. Don neman karin bayani duba: Bidayatul-mujtahid 1\115. Allah ne Mafi sani

TAMBAYA NA SHIDA (0006) YAYA IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA?

TAMBAYA NA SHIDA (0006) YAYA IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA? To yan'uwa dole ne, sai ta yi jini uku kamar yadda Hanafiyya suka fada, ko kuma tsarki uku kamar yadda Malikiyya suka tafi akai, ko da kuwa duk shekara take yin haila sau daya, saboda Allah Madaukaki ya rataya idda ne da samuwar jini, kamar yadda yake cewa a cikin suratul Bakara aya ta : (228) "Kuma matan da aka saka, to za su jira tsawon jinane uku" Don haka duk tsawon lokacin da za ta zauna to dole sai ta jira su, kamar yadda ayar take nunawa. Allah ne Mafi sani.

TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA?

TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA? Yan'uwa janaba wani hukunci ne da yake faruwa saboda ɗaya daga cikin abubuwa guda biyu : 1. Ko dai mutum ya yi mafarki kuma ya ga maniyyi, 2. Ko kuma mutum ya sadu da matarsa, duka waɗannan suna wajabta wanka, wankan janaba tana da siffofi guda biyu, duk wacce ka ɗauka ta yi: I/. Siffar da ta fi kamala ita ce wacce ta zo a hadisin A'isha cewa Manzon Allah (S.A.Ws) idan ya zo wankan janaba yana farawa ne da wanke hannunsa, sannan sai ya wanke farjinsa da hannun hagu, sai kuma ya yi alwala amma ban da wanke kafa, sannan sai ya ɗebi ruwa sau uku ya zuba a gashinsa, bayan haka sai ya zuba a ragowar jikinsa, sannan sai ya wanke kafarsa. Bukari da Muslim.
II/. Akwai kuma siffa ta biyu wacce ta zo a hadisin Ummu-salama lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake siffanta mata wankan janaba, inda yake ce mata: "Ya isar miki ki zuba ruwa sau uku a kanki, sannan ki zuba a duka jikinki, mutukar kin yi haka to kin tsarkaka" Muslim ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (330). Allah ne Mafi sani.

SHAHADAR ANAS BIN NADR (Radhiyallahu anhu) KASHI NA ƊAYA

SHAHADAR ANAS BIN NADR (Radhiyallahu anhu) KASHI NA ƊAYA Anas bin Nadr (R.A) yana daya daga cikin Sahabban da basu samu sukunin shiga yakin Badar ba. Ya yi matukar bakin cikin rashin samun wannan babbar dama, wadda kuma ita ce irinta ta farko, kuma mafi ɗaukaka daga dukkan jihadin da aka yi a cikin tarihın Addinin Musulunci. Ya yi ta tunanin Allah Ta'ala Ya kawo wani yakin da zai samu damar bayar da tasa gudunmuwar, Tun da yake Allah Ta'ala bai sa ya samu sukunin shiga na Badar ba. Ai kuwa ba a dade ba, sai ga yakin Uhudu, watau shekara guda bayan na Badar. Ya shiga sahun jerin gwanon askarawan Islama, tare da zuciya guda. Duk da cewar kafirai sun fi yawa wajen wannan yaki, amma duk da haka, Allah Ta'ala Yana taimakon Musulmi har zuwa bayan lokacin da wasu mutane suka yi katoɓara, sa'annan reshe ya juye da mujiya, Musulmi suka daina cin galaba.
A wannan lokaci dai, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya umurci wasu maharba 'yan baka su hamsin, da su rika lura da baya, domin kada abokan gaba da ke kan doki, su ɓullo masu kwatsam. An dai riga an ja kunnensu cewar, lallai kada su kuskura su motsa daga inda suke, har sai sun samu umurnin yin haka daga wajensa. To amma a lokacin da suka ga Musulmi suna samun nasara, kana kafirai suna ta ranta a na kare, sai suka bar inda suke, da tsammanin cewar an gama yakin. Don haka suna ganin kamar wannan lokaci ne, na kwasar ganima. Shi jagoran 'yan bakan, ya yi iya matukar bakin kokarinsa don hana su wannan abu, don haka ya roke su da su ci gaba da tsayuwa wurin da suke, amma wadanda ma suka saurare shi basu fi mutane goma ba, inda suke ta jayayyar cewar, wannan umurni dai na Manzon Allah (S.A.Ws) kurum har zuwa lokacin da ake yin faɗa ne. MU HAƊU A KASHI NA BIYU Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️Ahmad Musa

BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU

BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU A kashi na ɗaya mun tsaya a dai-dai inda "Mai makon ma su amsa wannan gayyata da ya yi musu", sai ma suka ki ko saurarensa. Kuma duk da cewar an san larabawa da karimci, maimakon gwada wannan karimci nasu sai suka shiga yi masa abin da bai kamata ace ya fito daga bakinsu ba, a matsayinsu na shugabanni. In gajarce muku labari, fitowa ma fili suka yi ɓaro-ɓaro suka ce da shi, basa son ganinsa a wannan garin nasu. Da dai a kalla kamata ya yi ace Manzon Allah (S.A.Ws) ya samu kyakkyawan tarbo da kuma jawabi mai daɗaɗawa daga gare su Tun da yake sune shugabannin kabilarsu.
To amma maimakon haka, kurum sai ɗaya daga cikinsu ya kaɗa baki ya ce, 'Kai ne Allah Ya zaɓa a matsayin Annabi!' Wani kuma da ba'a ya ce: 'Duk yanzu Allah Ya rasa wanda zai zaɓa ya zama Annabinsa sai kai? Shi kuma na uku sai ya ce: 'Kai ni ba na ma son yin magana da kai, domin idan kai Annabi ne, yin gardama da kai jawo wa kai rigima ne, idan kuma kana kwaikwayon Annabawa ne, to don me zan ɓata lokaci na, ina magana da Annabin karya?" Manzon Allah (S.A.Ws) wanda yake kamar dutse ne wajen dauriya da hakuri, bai ɓata rai ba, kan irin abin da waɗannan shugabannin suka yi masa. Maimakon haka, sai ya shiga ƙoƙarin saduwa da talakawan garin. Amma duk cikinsu, babu wanda ya tsaya ya saurare shi. Maimakon haka ma sai suka nuna gara ma ya san inda dare ya yi masa, ya bar musu, garinsu. Lokacin da ya fahimci cewar duk irin abin da yake son nuna musu, ba za su fahimce shi ba, don haka sai ya yanke shawarar barin garin. To, amma su ma kyale shi ya fita lami lafiya, basu yi haka ba. Maimakon haka, sai suka tara fitinannun yaran garin, inda suka fito titi suna yi masa ature, kana suna (faɗa masa rashin kunya da bakaken maganganu), wasu kuma na jifansa. Allah Sarki! An yi ta jifansa da duwatsu, ko ina jikinsa yayi jina-jina, yadda har takai, takalmansa suka manne da kafafunsa saboda jinin da ke zuba. Ya bar garin cikin wannnan zullumi na bakin ciki. MU HAƊU A KASHI NA UKU Allah yasa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️*Ahmad Musa*