Saturday, December 2, 2023

TAMBAYA NA (0007) MECECE HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BUKATA A BANDAKI ?

TAMBAYA NA (0007) MECECE HUKUNCIN FUSKANTAR ALKIBLA YAYIN BIYAN BUKATA A BANDAKI ? To Malamai sun yi saɓani akan wannan hukuncin, Abu- hanifa ya hana hakan, Malik ya tafi akan cewa mutukar a gida ne to babu laifi, saboda hadisin Abdullahi dan Umar wanda yake cewa: "Na hau ɗakin Hafsa sai na ga Annabi (S.A.Ws) yana biyan bukatarsa, yana fuskantar Sham ya kuma juyawa alkibla baya", kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (145). Saidai abin da ya fi shi ne kar mutum ya fuskanci Alkibla, ko da a gida ne, saboda hadisin Abu-ayyub wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa: "Idan kuka zo yin bahaya to kada ku fuskanci alkibla kada kuma ku bata baya" Bukhari a hadisi mai lamba ta: (394) d aMuslim a hadisi lamba ta: (264), Tabbas barin kallon alkibla yayin biyan bukata shi ne ya fi, saboda hadisin da ya gabata da kuma fita daga sabanin Malamai, don haka idan mutum zai gina masai a gidansa zai yi kyau ya kautar da ita daga alkibla. Don neman karin bayani duba: Bidayatul-mujtahid 1\115. Allah ne Mafi sani

TAMBAYA NA SHIDA (0006) YAYA IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA?

TAMBAYA NA SHIDA (0006) YAYA IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA? To yan'uwa dole ne, sai ta yi jini uku kamar yadda Hanafiyya suka fada, ko kuma tsarki uku kamar yadda Malikiyya suka tafi akai, ko da kuwa duk shekara take yin haila sau daya, saboda Allah Madaukaki ya rataya idda ne da samuwar jini, kamar yadda yake cewa a cikin suratul Bakara aya ta : (228) "Kuma matan da aka saka, to za su jira tsawon jinane uku" Don haka duk tsawon lokacin da za ta zauna to dole sai ta jira su, kamar yadda ayar take nunawa. Allah ne Mafi sani.

TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA?

TAMBAYA NA BIYAR (0005) MECECE SIFFAR WANKAN JANABA? Yan'uwa janaba wani hukunci ne da yake faruwa saboda ɗaya daga cikin abubuwa guda biyu : 1. Ko dai mutum ya yi mafarki kuma ya ga maniyyi, 2. Ko kuma mutum ya sadu da matarsa, duka waɗannan suna wajabta wanka, wankan janaba tana da siffofi guda biyu, duk wacce ka ɗauka ta yi: I/. Siffar da ta fi kamala ita ce wacce ta zo a hadisin A'isha cewa Manzon Allah (S.A.Ws) idan ya zo wankan janaba yana farawa ne da wanke hannunsa, sannan sai ya wanke farjinsa da hannun hagu, sai kuma ya yi alwala amma ban da wanke kafa, sannan sai ya ɗebi ruwa sau uku ya zuba a gashinsa, bayan haka sai ya zuba a ragowar jikinsa, sannan sai ya wanke kafarsa. Bukari da Muslim.
II/. Akwai kuma siffa ta biyu wacce ta zo a hadisin Ummu-salama lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake siffanta mata wankan janaba, inda yake ce mata: "Ya isar miki ki zuba ruwa sau uku a kanki, sannan ki zuba a duka jikinki, mutukar kin yi haka to kin tsarkaka" Muslim ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (330). Allah ne Mafi sani.

SHAHADAR ANAS BIN NADR (Radhiyallahu anhu) KASHI NA ƊAYA

SHAHADAR ANAS BIN NADR (Radhiyallahu anhu) KASHI NA ƊAYA Anas bin Nadr (R.A) yana daya daga cikin Sahabban da basu samu sukunin shiga yakin Badar ba. Ya yi matukar bakin cikin rashin samun wannan babbar dama, wadda kuma ita ce irinta ta farko, kuma mafi ɗaukaka daga dukkan jihadin da aka yi a cikin tarihın Addinin Musulunci. Ya yi ta tunanin Allah Ta'ala Ya kawo wani yakin da zai samu damar bayar da tasa gudunmuwar, Tun da yake Allah Ta'ala bai sa ya samu sukunin shiga na Badar ba. Ai kuwa ba a dade ba, sai ga yakin Uhudu, watau shekara guda bayan na Badar. Ya shiga sahun jerin gwanon askarawan Islama, tare da zuciya guda. Duk da cewar kafirai sun fi yawa wajen wannan yaki, amma duk da haka, Allah Ta'ala Yana taimakon Musulmi har zuwa bayan lokacin da wasu mutane suka yi katoɓara, sa'annan reshe ya juye da mujiya, Musulmi suka daina cin galaba.
A wannan lokaci dai, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya umurci wasu maharba 'yan baka su hamsin, da su rika lura da baya, domin kada abokan gaba da ke kan doki, su ɓullo masu kwatsam. An dai riga an ja kunnensu cewar, lallai kada su kuskura su motsa daga inda suke, har sai sun samu umurnin yin haka daga wajensa. To amma a lokacin da suka ga Musulmi suna samun nasara, kana kafirai suna ta ranta a na kare, sai suka bar inda suke, da tsammanin cewar an gama yakin. Don haka suna ganin kamar wannan lokaci ne, na kwasar ganima. Shi jagoran 'yan bakan, ya yi iya matukar bakin kokarinsa don hana su wannan abu, don haka ya roke su da su ci gaba da tsayuwa wurin da suke, amma wadanda ma suka saurare shi basu fi mutane goma ba, inda suke ta jayayyar cewar, wannan umurni dai na Manzon Allah (S.A.Ws) kurum har zuwa lokacin da ake yin faɗa ne. MU HAƊU A KASHI NA BIYU Allah ya sa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️Ahmad Musa

BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU

BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU A kashi na ɗaya mun tsaya a dai-dai inda "Mai makon ma su amsa wannan gayyata da ya yi musu", sai ma suka ki ko saurarensa. Kuma duk da cewar an san larabawa da karimci, maimakon gwada wannan karimci nasu sai suka shiga yi masa abin da bai kamata ace ya fito daga bakinsu ba, a matsayinsu na shugabanni. In gajarce muku labari, fitowa ma fili suka yi ɓaro-ɓaro suka ce da shi, basa son ganinsa a wannan garin nasu. Da dai a kalla kamata ya yi ace Manzon Allah (S.A.Ws) ya samu kyakkyawan tarbo da kuma jawabi mai daɗaɗawa daga gare su Tun da yake sune shugabannin kabilarsu.
To amma maimakon haka, kurum sai ɗaya daga cikinsu ya kaɗa baki ya ce, 'Kai ne Allah Ya zaɓa a matsayin Annabi!' Wani kuma da ba'a ya ce: 'Duk yanzu Allah Ya rasa wanda zai zaɓa ya zama Annabinsa sai kai? Shi kuma na uku sai ya ce: 'Kai ni ba na ma son yin magana da kai, domin idan kai Annabi ne, yin gardama da kai jawo wa kai rigima ne, idan kuma kana kwaikwayon Annabawa ne, to don me zan ɓata lokaci na, ina magana da Annabin karya?" Manzon Allah (S.A.Ws) wanda yake kamar dutse ne wajen dauriya da hakuri, bai ɓata rai ba, kan irin abin da waɗannan shugabannin suka yi masa. Maimakon haka, sai ya shiga ƙoƙarin saduwa da talakawan garin. Amma duk cikinsu, babu wanda ya tsaya ya saurare shi. Maimakon haka ma sai suka nuna gara ma ya san inda dare ya yi masa, ya bar musu, garinsu. Lokacin da ya fahimci cewar duk irin abin da yake son nuna musu, ba za su fahimce shi ba, don haka sai ya yanke shawarar barin garin. To, amma su ma kyale shi ya fita lami lafiya, basu yi haka ba. Maimakon haka, sai suka tara fitinannun yaran garin, inda suka fito titi suna yi masa ature, kana suna (faɗa masa rashin kunya da bakaken maganganu), wasu kuma na jifansa. Allah Sarki! An yi ta jifansa da duwatsu, ko ina jikinsa yayi jina-jina, yadda har takai, takalmansa suka manne da kafafunsa saboda jinin da ke zuba. Ya bar garin cikin wannnan zullumi na bakin ciki. MU HAƊU A KASHI NA UKU Allah yasa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️*Ahmad Musa*

TAMBAYA NA HUƊU (0004) MENE NE ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA

TAMBAYA NA HUƊU (0004) MENE NE ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA To yan'uwa akwai abubuwan da malamai suka yi bayani cewa, suna kawo nutsuwa a zuciya, ga su kamar haka: 1. Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar duk wata shirka da bidi'a da abin da yake kaiwa zuwa gare su.
2. Shiriya da hasken da Allah Yake jefawa a zuciyar bawa, wanda duk lokacin da aka rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci. 3. Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da ilimin mutum ya yalwata, zai samu jindadi a zuciyarsa. 4. Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin Allah "Wadanda suka yi imani, zuciyoyinsu suna nutsuwa da zikirin Allah" Suratu Arra'ad aya ta (28). 5. Kyautatawa bayin Allah, saboda duk mutumin da yake yin kyauta zai kasance cikin kwanciyar hankali, kamar yadda marowaci yake kasancewa cikin kunci. 6. Fitar da kyashi da hassada daga zuciya. 7. Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida. 8. Barin baccin da ba shi da amfani. 9. Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin karawa akan haka. 10. Rashin cakuduwa da mutane sai gwargwadon bukata. Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke jawo bakin ciki da damuwa da kuma kunci. Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad 2\22. Allah Ne Mafi sani.

Wednesday, November 29, 2023

TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI?

TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI? Malam, menene bambanci tsakanin nifakul amali da i'itikaadi? To Malam: Nifaqul i'itikadi (wanda ake kudurcewa a zuciya) shi ne boye kafurci da kuma bayyana Musulunci, kamar yadda wasu mutane suka yi a zamanin Manzon Allah (S.A.Ws), duk wanda ya siffantu da wannan to ba musulmi ba ne, kamar yadda Allah ya yi bayani a suratul Munafikun. Amma nifakul-amali (munafuncin aiki) kuwa to shi ne wanda ya zo a cikin hadisin Abdullahi dan Amr inda Annabi (S.A.Ws) yake cewa: "Dabi'u guda hudu duk wanda suka kasance tare da shi, to ya zama cikakken munafiki, wanda kuma ya ke da daya daga cikinsu to yana da dabi'ar munafukai har sai ya bar ta: idan ya yi zance ya yi karya, idan aka amince masa ya ci amana, idan ya yi alkawari ya yi yaudara, idan ya yi husuma sai ya yi fajirci". Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: (34) da Muslim a hadisi mai lamba ta: (106). In mutum ya siffantu da daya daga cikin wadannan dabi'u guda hudu, to bai fita daga Musulunci ba, saidai yana da tawayar imani. Allah Ne Mafi sani.