1. WANENE YA HALICCE NI?
Wanda ko Wanne Musulmi Ya san Wannan Tambayar Sai dai Na kawota dan Itace ta zama Wajibi ta fara shigowa a Jeren Wayannan Tambayoyin, To tunda kowanne Musulmi Ya san Wanda Ya halicce shi Sai tambaya ta Biyu.
2. DON ME YA HALICCE NI?
Allah (swt) da kansa Ya Bamu Amsar wannan Tambaya Sai dai Wasummu basa ma lura da Amsar ballantana Suyi abinda Allah (swt) Yace.
Allah (swt) Yana Cewa "BAN HALICCI MUTUM DA ALJANI BA SAI DON SU BAUTA MIN".
3. TO YAYA NE AKEYIN BAUTAR?
Kowannen Mu ya kamata Yasan Cewa Bauta dole bata Yuwa Sai da Ilmi kuma Dole ne Sai Da Yin tambaya akan abinda Ya shafi Ilmi Shi kan shi.
Sharuddan Yin Bauta
- Ka samu a cikin Al'qur'ani Ance Ayi.
- Ka dauko Yanda Magabata na Kwarai Suka yi bautar, Ma'ana Yanda Suka Dauko Yanda Manzon Allah (saww) Yake yin bautar.
- kayi Badan Wani ko wata Ya Yaba maka ba.
4. A INA NAKE YANZU?
Ma'ana A ina nake Yanzu? Shin Ina nan In da Allah ke son Ya Ganni? Ko kuma Na saki Hanya?
5. ZUWA INA MAKOMA TA ZATA KASANCE?
Bayan Duk Wayannan Tambayoyin Guda Hudu to tambaya ta Biyar Duka ta fisu Tsoro da Rudani, Amsar tambayar Makomata Wutane ko kuma Aljanna.
Lalle Wayannan Tambayoyin Abin Dubawa Ne Ga Kowanne Musulmi Mai Hankali.
Wallahi Wa sun Mu da Yawa Sun Yarda Da Allah ne Ya Halicce Su Amma basu san Yarda Shi Yake da Ikon Yi musu Komai ba, Basa Neman Taimakonsa Sai Na Bokaye da 'Yan bori.
Wallahi Da Yawan Wasummu Basu Ma Iya Karanta Fatiha Dai dai ba, Amma Idan Zaka Lissafa Wakokin Kafirrai Zakaji Ya Fi hardace Su Fiye da Surorin Al'Qur'ani koma Sunayen Allah.
Wallahi Wasummu Basa Tuna Mutuwa Ko kadan, Kullum Tunanin Su Ya Za'ayi na Samu Kuddi, ko wani abu makamancin haka, Amma basa Tunanin Shin Ana Amsar Ibada ta, Shin Zan Iya Mutuwa Yau, Shin Meye Zunubbai na A gurin Allah (swt).
Wallahi Da Yawa Daga Cikin Mu Har Sun Manta Da Suyi Istigfari Sai Dai Kullum Suna kan Whatsapp, Facebook, Twettr, Istagram, da Sauransu.
Wallahi Mu komawa Allah (swt) ko zamu Samu Rabauta.
Ya Kamata Kana Gama Karatun Wannan Post Din Ka Tashi Kayi Istigfari, Kace " ASTAGFIRULLAHI" ko sau 100, Kada Ka bari Har Ajuma Dan Zaka Iya Mutuwa Yanzu.
ALLAH YA SAMU DACE DUNIYA DA LAHIRA, KUMA ALLAH YA TSARE JIKKUNAN MU DA WUTAR JAHANNAMA.
ahmadmusainc.blogspot.com
Sunday, March 22, 2020
Saturday, March 21, 2020
JINJINA GA IYAYE *****************
Idan mutum ya yi NAZARIN wahalar da IYAYE suka sha wajen tashinsa, da daure ma kurciyarsa har zuwa sadda zai yi hankali shi kadai ya isa ya nuna masa
girman hakkin IYAYE a kan sa.
To, ina ga kuma in mun koma ga alhakin uwa na daukar ciki wata tara tsakanin lafiya da ciwo, laulayi da haraswa, da kyamar abinci da raunin jiki da nauyin ciki har zuwa ga nakuda wadda wata 'yar karamar lahira ce mata suke zuwa a mafi
yawan lokuta!
Annabi (saww) Ya nuna mana Muhimmancin Iyaye a hadisai da dama musamman ita Uwa.
YA DAN UWA/'YAR UWA musulmi/ma
Mu gode wa Allah da ya sa mu cikin inwar addinin musulunci da karantarwarsa.
Daga cikin abinda TURAWA ke fama da shi a yau mai tada hankali shine;
Akwai tanadin da kowane mutum yake yiwa kansa na kuddi don tsufansa.
Dole ne mutum ya tara wasu makudan kudade da zasu amfane shi idan ya tsufa. Don me?
Don babu wanda zai kula da shi idan ya tsufa. In ba haka ba kuwa lalle ne zai kare rayuwarsa a gidan nakasassu da
gajiyayyu wanda gwamnati ta tanada wanda kuma ba shi da banbanci da zaman fursuna a kurkuku.
A lokacin su kuma 'ya'yansa maza da mata na can suna soyayya da abokai da kawayensu ba wanda ya damu da shi.
A kasashen turawa akwai kowace doka har da ta hakkin karnuka amma babu wata doka akan hakkin IYAYE. Don me? Wai don kada a takura wa 'ya'ya! Za
a shiga cikin 'yancinsu!!
Musulunci ya banbantamu da su ta in da ya nuna mana cewa iyaye suna da hakki sosai ga 'ya'yan su koda kuwa bayan sun MUTUNE.
Wata likita ta bada labarin wani mutum mai biyayya mai ban mamaki.
Tace wata Tsohuwa ce wawiya da ba a haife ta ma da hankali ba.
'Dan ta ya zo da ita yana mai tsananin kula da ita. Ba ya son komi ya same ta. Kullum idonsa na kan wannan mahaifiyar tashi.
Saboda mamakin irin yanda yake kula da mahaifiyar tasa, yasa wannan likita ta tambaye shi, kuma ya sanar da ita cewa tun lokacin da aka haifeta (ita mahaifiyar tasa) tana fama da tabuwar hankali kuma bata san abinda take yi ba.
An aurar da ita ga mahaifinsa bayan ta samu cikinsa sai mahaifin ya kasa hakura da zama da ita, ya sauwake mata ta koma hannun iyayenta. wannan abin ba karamin tashin hankali ya saka wannan matar ba.
Akan haka yasa ta kara shiga tsananin tashin hankali.
Tashin hankalin da wannan matar ta shiga shine, yasa ya bar komai baya komai sai kula da ita mahaifiyarsa.
Ku duba fa shi wannan ya kula da uwar da cikinsa kawai ta dauka bata san wahalarsa kowace iri ba yana ta tarainiya da ita haka.. To, mu da iyayenmu suka sha kowace irin wahala a kanmu ya zamu yi kenan?!
A cikin tarihin magabata akwai labarai masu kayatarwa game da bin wannan umurni na ubangiji na kwautaatawa iyaye.
1. Mis'ar bin Kidam (rta) ya taba kawo ma
mahaifiyarsa ruwa bayan ta nemi haka amma ko da ya zo ta yi bacci. Sai ya tsaya har gari ya waye bai tashe ta ba kuma bai tafiyarsa ba.
2. Muhammad bin Al-Munkadir ya ce, na kwana ina murza kafar mahaifiyata don ta ji dadin bacci, kanena kuma ya kwana yana sallah. Bana tunanin a bamu lada daya sai dai ni na fishi samun ladar.
3. Sayyidina Abu Huraira (rta) ya ga wani mutum yana tafiya bayan wani dattijo. Sai ya tambaye shi, wane ne? Ya ce, mahaifina. Sai ya ce: kada ka kira shi
da sunansa, kada ka zauna kafin sa, kuma kada kayi tafiya a gabansa.
Bayan haka ya kai dan uwa musulmi! Ka sani ba wani laifi a wurin Allah wanda yake gaggauta kama mai yinsa, ya debe masa albarka, ya barkata masa rayuwa tun a nan duniya kamar cuta wa iyaye.
Sai ka ga mutum ya damu da matarsa, ya kula da 'ya'yansa amma bai ko san halin da mahaifiyarsa take ciki ba.
Ankarbo daga Abu kahil, cewa Manzon Allah (saww) yace; ku cewa wanda yayi biyayya ga mahaifansa, a halin suna raye ko suna mace, to lalle Allah (SWT) ya yarda da shi a ranar Qiyama, sai muka ce yaya mutum zaiyi biyayya ga mahaifansa Alhali suna mace Ya Rasulillahi? Sai yace; ya nema musu gafara, kar ya zagi mahaifan wani balle a zagi na sa mahaifan.
YA ALLAH KA GAFARTAWA IYAYEN MU, KA YAFE MUSU KURAKURANSU...(AMEEN)
NI DAI KU SHAIDA NA TURO WANNAN BADAN KOMAI BA SAI DON TUNA WA DA MAHAIFANA DA KUMA ROKA MUSU GAFARA.
KACE AMEEN KUMA KA TURA GA 'YAN UWANKA DOMIN ROKAWA IYAYENKA GAFARA.

TAMBAYA AKAN GASHI A CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA.*
✍ Rubutawa: *Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah).*
TUN JIYA AKE BUGO MINI WAYA AKAN WAI WANI YA YI MAFARKI YA GA ANNABI MUHAMMAD SAW, WAI YACE MASA A BUƊE ALKURNANI CIKIN SURATUL BAƘARA, ZA A GA GASHI SAI A JIƘA A SHA YANA MAGANIN CORONA VIRUS.
MANZON ALLAH SAW YACE :DUK WANDA YA YI MINI ƘARYA YA TANADI MASAUKINSA A CIKIN WUTA. BUKHARI DA MUSLIM
WANNAN MAFARKI DA WANNAN MAGANA BA GASKIYA BACE SABODA DALILI GUDA GOMA:
-NA ƊAYA, MAFARKI DA ANNABI SAW GASKIYA NE, AMMA SAI KA GAN SHI YADDA YAKE A KAMANNINSA DA MAGANGANU SA DA HALAYANSA, WANNAN KUWA BAI YI KAMA DA YADDA ANNABI SAW YAKE ISAR DA SAKO BA, GASHI DA ALKUR'ANI.
- NA BIYU, ME YA HAƊA DA ALKUR'ANI MAI GIRMA DA KUMA GASHI?.
- NA UKU, GASHIN NA WAYE, MUTUM KO DABBA? KUMA NA INA NE GASHIN?.
- NA HUƊU, DUK WANI GASHI IDAN BA NA ANNABI SAW BA, TO ZAI ZAMA KO ƘAZANTA KO NAJASA.
- NA BIYAR, ME YASA BA'A YI AMFANI DA ALKUR'ANIN BA SAI GASHIN KAWAI?.
- NA SHIDA, ME YASA SAI A AFRIKA KAWAI AKE SAMUN WAƊANNAN SHIRMAN.
- NA BAKWAI, WAYE YA BUƊE ALKUR'ANIN KUMA YAGA GASHIN?.
- NA TAKWAS, INA WANDA YAGA MAFARKIN YAKE?.
- NA TARA, AN GWADA AKAN MAI CIWAN YA WARKE? KO YA WARKE BA ZAI ZAMA GASKIYA BA, DOMIN ZAI IYA ZAMA JARRABAWA.
- NA GOMA, ANYA BA SHEƊANU BANE DA BOKAYE, DA MASU SIHRI SUKE SON HALAKA MUTANE? DOMIN AYI WASA DA ALKUR'ANI MAI GIRMA DOMIN WATA MUSIFAR TA ƘARA SAUKA, KAMAR YADDA YA FARU A LOKACIN IBOLA DA GISHIRI?.
ALLAH YA TSARE MANA IMANI DA AKIDA YA YAYE MANA DUKKAN BALA'I.

Friday, March 20, 2020
SUBHANALLAH
Tun bayan da Mushirakan Larabawa suka kori Manzon Allah (SAW) daga garin Makkah yayi hijira tare da sahabbansa zuwa Madinah, daga baya Manzon Allah Ya sake dawo wa yaci Makkah da yaki (akayi Fathu Makkah), Musulunci ya kafu, shekaru sama da dubu daya da dari hudu da suka gabata ba'ayi wani lokaci da aka hana musulmai sallah a masallaci ba a fadin Kasar Saudiyyah har da Makkah da Madinah ba sai wannan karon
Jiya mahukuntan Saudiyyah sun bada umarnin rufe Masallacin Manzon Allah (SAW) dake birnin Madina da kuma Masallacin Harami dake birnin Makkah saboda masifar cutar annoba da ta addabi duniya (Coronavirus)
Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo yace:
Mu sani cewa lalle babu wata musifa da ta wuce a jarrabeka a cikin addininka, yau gashi ana ta rufe Masallatai, ana hana fitowa sallar Jam'i, har sallar juma'a da yawa daga kasashe sun bayarda sanarwa a dakata sakamakon wannan cuta, Lalle wannan abun tsoro ne! Kamar Allah Yayi fushi da mutane ne, yace: Ku fita ku bar min dakuna na (Masallatai) tunda barnaarku a bayan kasa tayi yawa.
Babbar musiba ce a rabaka da dakin Allah, a ce babu Umarah, babu Dawafi, babu sallar jam'i, lalle babu musibar da tafi musiba a cikin addini, tabbas Allah Yana fushi da mutane, Ya zama wajibi mu koma mu tuba ga Allah.
Allah Ka yafe mana, Ka kawo mana saukin wannan masifa Amin

Saturday, March 14, 2020
Abubuwa Guda Bakwai Wanda Allah Ya Jarabci Al'ummar Duniya Da A Su Cikin Wannan Shekarar Ta 2020
01. Dubannin mutame sun kamu da cutar KoronaVirus a fadin duniya.
02. A shekaran jiya anyi guguwa mai karfi a kasashen Misra da Sham.
03. Miliyoyin fari da dangwaye sun cika kasar Yamen da wasu kasashe a gabashin Afrika.
04. A shekaran jiya an samu wani bugun iska mai karfi wanda ya rinka tunbuke bishiyoyi a kasashen Palasdin da Urdun da Syria.
05. Birori sun cika tituna kasar Thailand saboda yunwa ya koro su, suna neman abinci.
06. A satin da ya gabata jemagu sun cika kasar Australia
07. Abu mafi muni shine, a wannan shekarar aka tsare mutane daga dawafi a daki mai alfarma saboda cutar KoronaVirus.
Ya Allah ka gafarta muna ka jikan mu amin.
Fityanul Islam Of Nigeria
14/02/2020

Tuesday, March 10, 2020
TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...12..
Lokacin da wannan jakada ya zo wa Annabi sulaiman(A.S) mabiyansa suna tare da shi da hadiya a tare dasu, sai Annabi sulaiman(A.S)Yace shin zaku 'kare ni da dukiya, bayan abin da Allah(S.W.T)ya bani ? Na Annabta da mulki shine mafifici daga abinda ya baku na duniya, kai bari! Ku dai kuna farin ciki ne da kyautarku saboda al'faharin ku da tarkace-tarkacenku, ka koma da abinda ka zo da shi na hadiya, lallai zamu zo musu da runduna wadda ba su da iko da ita, kuma lallai zamu fisshe su daga garinsu birnin saba'i, kuma zamu fisshe su in basu zo min suna masu mi'ka wuyaba.
Lokacin da jakada ya koma musu da wannan kyautar sai ta sanya gadonta cikin 'kofa bakwai7 daga cikin katangar gidanta, gidan nata kuma yana cikin gidaje bakwai7, ta kulle 'kofofin ta sanya masu tsaro, sannan kuma tayi shirin tawowa gurin Annabi sulaiman(A.S)Dan taga abinda zai umarceta da shi, sai ta maraito acikin makwayo dubu goma sha biyu, ko wamne makwayo dubbai suna tare da shi, har izuwa kusa da Annabi sulaiman(A.S)da mil uku (3-m) , sai Annabi sulaiman(A.S)ya yi hashashe da ita , sai yace yaku wad'annan jama'a wanene zai zo min da gadonta tun kafin su zo min suna masu mi'ka wuya, sai wani gwarzo daga Aljanu, wato mai tsananin 'karfi yce ni zan zo maka da shi kafin ka ta shi daga mazaunin shari'arka, (wato daga safiya zuwa rabin yini)ha'ki'ka ni mai 'karfi ne kuma amintacce ne ni ga abinda yake cikin gadon na jauharori da makamantansu, sai Annabi sulaiman(A.S)Yace ina son mafi sauri daga haka, sai wani wanda yasan ilimin littafi ya ce ni zan zo maka da shi kafin idonka ya koma gareka idan kayi duba da shi izuwa wani abu, sai ya subi sama, yana dawo da idon 'kasa sai ya ganshi a gabansa, lokacin da Annabi sulaiman(A.S)ya ga wannan gadon a gabansa sai yace wannan falalar Ubangiji ce don ya jarrabe ni zan gode masa ko zan butulce masa, wanda ya godewa ni'imar Allah, to tabbas ya gode dan kansa, domin sakamakon godiyar nan nasa ne, To tabbas Ubangiji mawadaci ne ga buran godiyar sa, kuma mai karamane da Baiwa a bisa wanda ta butulce masa.
Sai Annabi sulaiman(A.S)yace ku jirkita gadonta, zuwa halin da bazata ganeshi ba, mu gani zata ganeshin? Domin jarraba hankalinta, lokacin da ta zo sai akace, shin kamar haka gadonki yake? Sai tace kai kace shine kamar yadda suka shigar mata da kwatance, sai Annabi sulaiman(A.S)ya lura da cewa lallai tana da sani da basira, an bamu ilmi tun ga banta, mun kasance masu mika wuya, ya fad'i hakane don nuna godiya ga Allah, abinda kuma take bautawa ba Allah ba,ya tare ta ga Bautar Allah(S.W.T) ha'ki'ka ita ta kasance daga mutane kafirai.
Lokacin da ta tsaya gurin Annabi sulaiman(A.S)Sai aka ce da ita wannan rufi , rufine na gilas fari ruwan dad'i yake kwarara a 'kar'kashisa, akwai kifi da kwado da dabbobin ruwa, Annabi sulaiman(A.S)ya zuba su, lokacin da tagani sai ta zaci kunzomeman ruwa ne, sai ta yaye 'kafafuwanta guda biyu domin tsallaka ruwan, Annabi sulaiman(A.S)yana kan gadonsa gana kallonta, sai yaga 'kafafuwanta kyawawa, sai yace mata wannan rufi ne mai santsi na kaskon 'karau, sai ta ce Ubangiji ha'ki'ka na zalinci kaina da bautar waninka na mika wuya tare da Annabi sulaiman ga Allah Ubangijin Talikai.
Sai ta nemi ya aure ta sai ya 'ki saboda gashin 'kafarta, sai shaid'anu sukayi, masa nur wato farar 'kasa, sai ya kawar da gashin, sai ya aure ta ya tabbatar da ita akan mulkinta, ya kasance yana ziyartarta sau d'aya a wata yana zama a wajanta kwana uku.
Mulkinta ya 'kare da 'karewar mulkin Annabi sulaiman(A.S), An ruwaito cewa An khalifantar da shi gana d'an shekara shia uku(13), ya rasu kuma yana d'an shekara hamsin da uku(53).
WAFATIN ANNABI SULAIMAN(A.S)..
.ZANI GABA INSHA ALLAHU..

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...1O..
LABARIN BILKISU DA ALHUDA-HUDA.
Malamai sukace, acikin labarun , Lokacin da Annabi sulaiman(A.S)ya gama ginin Baitul Mu'kaddis, sai yayi nufin fita zuwa harami, sai ya tattara tawagarsa ta mutane da Aljanu da tsuntsaye da 'kwari, sun kai yawan Bataliya d'ari , sai iska ta d'aukesu zuwa harami, sai ya sauka anan yayi kwanaki iya yadda Allah yaso, har yayi aikin HAJJI , da sauran wasu ibadu, kuma ya gayawa mutanansa labarin zuwan Annabi Muhammad(S.A.W)sannan sai yayi nufin tafiya 'kasar yaman, sai ya fita daga makka da safe, ya nufi 'kasar yaman, su kai wani gari da ake SAN'A'A , a dai dai lokacin zawali( Wato lokacin sallar azahar)Tafiyar wata d'aya kenan,amma yayita a d'an wannan lokacin, sai ya ga wannan garin kyakkyawan garine, ga haske ga kuma kayan marmari 'kanshi sai tashi yake, sai ya sauka a wannan garin don yin sallah da kuma cin abincin rana, sai suka nemi ruwa basu samuba, Dama Alhuda-huda shine d'an jagora gurin neman ruwa domin yana ganin ruwa a duk inda yake koda kuwa a 'kar'kashin 'kasane kamar yadda mutum yake kallon ruwa a kofi idan yana gabansa, idan ya hango ruwan sai ya tona, sai su kuma shaid'anu su tona su d'ebo, sai aka nemi Alhuda-huda baya nan.
'Katadata ya rawaito cewa, Manzon Allah(S.A.W)yace, (NA HANEKU DA KASHE HUDAHUDA DOMIN SHINE JAGORA ANNABI SULAIMAN (A.S)GURIN RUWA) sai Annabi sulaiman(A.S)ya nemi Alhuda-huda Bai ganshiba, sai yayi masa wannan Al'kawarin na narko, shi kuma HUDAHUDA lokacin da yaga Annabi sulaiman(A.S)ya shagala da sauka a 'kasar SAN'A 'A, sai ya tashi sama domin ganin tsahon duniya da fad'inta, ya duba gabas da yamma, sai ya hango gonar BILKISU, sai ya sauka a cikinta , sai ya had'u da wani huda hudan wanda ake kiransa da suna (AFIR) shi kuma ALHUDA-HUDAN Annabi sulaiman(A.S)ana kiransa da suna(YA'AFUR)sai Afir yace da Ya'afur ina zaka! Kuma daga ina? Sai Ya'afur yace daga SHAM nake tareda sahibina sulaiman d'an Dauda(A.S)sai Afir yace waye sulaiman? Sai Ya'afur yace sarkin mutane da Aljanu da shaid'anu da 'kwari da dabbobi da iska, sai Ya'afur yace to kai kuma daga ina? Sai Afir yace anan garin nake, sai Ya'afur yace waye sarkin garin? Sai Afir yace wata macece , sai yace ya sunanta? Sai Afir yace BILKISU, Amma fa sulaiman yana da mulki babba, sai dai bai kai na BILKISU ba, domin ita tana mulkin Yaman ne gaba d'aya, A 'k'kashinta akwai jagorori guda Dubu goma sha biyu(12,000)kuma kowa ne jagora yana da maya'ka dubu d'ari(100,000)ko zamu je kaga mulkinta? Sai yace ai kuma ina tsoro kada sulaiman ya nemeni lokacin sallah, idan yana bu'katar ruwa, sai Afir yace, ai Annabi sulaiman(A.S)Zai ji dad'i idan ka bashi labarinta, sai suka tafi domin yaje ya gani bayan ya gani, sai ya koma gurin Annabi sulaiman(A.S)dai dai lokacin sallar la'asar, to Dama wannan lokacin an nemi ruwa an rasa kuma an nemi Alhuda-huda baya nan.
Amma wannan zance marar Tushe ne a malamai.
A ruwayar d'an Abbas kuma cew akayi, wani yanki na rana ya saraya akan Annabi sulaiman(A.S)sai ya duba gurin da Alhuda-huda yake bayanan sai ya yi kiran wannan tsuntsun mai suna Nasir ya tambaye shi cewa ina HUDAHUDA? Sai yace Ranka ya dad'e! Bansan inda yayi ba, kuma ban aike shi ko ina ba dayake shine shugaban tsuntsaye, sai Annabi sulaiman(A.S)yayi fushi sai yace , sai na azabtar da shi azabtarwa ko kuma in yankashi, ko kuma yazo min da wata hujja mai 'karfi, sai ga HUDAHUDA ya dawo, sai Nasir yace dashi ina kashiga yau? Ga shi Annabi sulaiman(A.S)Ya yi rantsuwa sai ya azabtar da kai, sai HUDAHUDA yace kuma bai togace komaiba, sai yace a'a yace sai dai in kazo masa da hujja mai 'karfi, sai ya ce yawwa, sai ya tashi ya tafi gurin Annabi sulaiman(A.S)yana zaune akan kujerarsa, lokacin da ALHUDA-HUDAN ya kusanci Annabi sulaiman(A.S)sai ya d'aga kansa sama ya shin fid'a fuka fukansa a 'kasa da jelarsa yana jansu domin nuna Tawaki'u ga Annabi sulaiman(A.S)Sai Annabi sulaiman yasa hannu akan ALHUDA-HUDAN sai ya funcika yana mai cewa ina kake ina nemanka, to zan azabtar da kai azaba mai tsanani, sai HUDAHUDA yace ya Annabin Allah kaji tsoran tsayiwarka agaban Allah, sai Annabi sulaiman(A.S)ya girgiza, sai ya yi masa rangwame, sannan sai Annabi sulaiman(A.S)yace ina ka tafi? Sai HUDAHUDA yace , kamar yadda Allah yake fad'a ackin Alkur'ani cikin suratun namli ayata 22 cewa:-
Zanci gaba insha Allahu
Musha ruwa lpy.

Subscribe to:
Posts (Atom)