Tuesday, March 10, 2020

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...6

 Sai Allah(S.W.T)Ya umarci Annabi sulaiman(A.S)da ya sauka yayi sallah acikinsa, kuma ya kusance shi da wani abin kusanta, sai Annabi sulaiman(A.S)ya aikata haka, ance Annabi sulaiman(A.S)ya yanka ra'kuma dubi biyar, da Bajimayan shanu dubu biyar,da akuyoyi dubu ashirin, a daf da ka'aba ,sai Annabi sulaiman(A.S)ya gaya wa wasu manya daga cikin mutanansa cewa, wannan gurin wani Annabi Balarabe zai fito daga gareshi, za'a bashi taimako da nasara ga duk wanda yayi taurin kai agareshi, kuma takobi zata kasance a wuyan duk wanda ya sa'ba masa, kuma kwarjininsa zai kai musalin tafiyar wata guda, wanda yake a kusa da wanda yake   a nesa duk d'aya ne a gurinsa, baya jin tsoran zargin mai zargi acikin bin Ubangiji, Aljanna ta tabbataga wanda ya riskeshi kuma ya gasgatashi, sai suka ce tsakaninmu da shi zai shekara nawa ya kai Annabin Allah? sai yace zai kusa shekara dubu(1000).
        Sai Annabi sulaiman(A.S)ya cigaba da tafiya har ya isa wani kwari da ake kira (WADIS-SADID)sannan kuma ya 'karasa kwarin wannan tururuwar wanda shima ake kiransa(WADIN NAMLI)sai wannan tururuwa ta tashi tana tafiya tana d'an rangaji, ya kasance girmanta kamar girman kura , ma'abociyar fukafukai guda biyu.
    Malamai sunyi sa'bani a kan sunanta wasu suka ce  sunanta  (DAKHIYA)wasu kuma sukace sunanta(KHIRMA), sai tayi kiran 'yan uwanta tururuwai saboda rundunar Annabi sukaiman(A.S)da ta gani, shine fad'in Ubangiji(S.W.T)cewa:-" YA KU JAMA'AR TURURUWAI! KU SHIGA GIDAJANKU KADA SULAIMAN DA RUNDUNONINSA SU KARKARYA KU, A HALIN SU BA SU SANI BA." suratun namli.
      Dama kamar yadda muka fad'a cewa babu wata halitta da zatayi magana face sai iska ta dakkota ta kawo wa Annabi sulaiman(A.S), aka ce Annabi sulaiman(A.S)yaji maganar wanann tururuwar misalin tsawon mil uku(3-m), sai Annabi sulaiman(A.S)yayi murmushi saboda jin maganar wannan Tururuwar, sai yace Ubangijina ka cusa min in godewa ni'imarki wacce ka ni'imta ta gareni da kuma mahaifana guda biyu, kuma in aikata aiki na 'kwarai, wanda kake yarda da shi kuma ka shigar dani rahamarka acikin bayinka managarta.
       Haka tsarin maganarsa tazo acikin Alkur'ani mai girma cikin suratun Namli aya ta 19. Awasu sauran 'kissa kuma akace, Annabi sulaiman(A.S)lokacin da yaji zancen wannan tururuwar sai ya sakko zuwa gareta, sai yace; azo da ita, sai aka zo da ita, sai yace da ita, saboda me wad'annan Tururuwan suka tsorata sunji ance ni azzalimine? Saboda me kikace kada sulaiman da rundunarsa su karkaryaku? Sai Tururuwar tace ya Annabin Allah bakaji a cikin maganata nace, "A HALIN BAKU SANI BA." Kuma duk da cewa na san banyi nufin karkaryawa na jikiba ina nufin karkaryawa na rai, saboda naji tsoro kada suyi burin abinda Allah yabaka, sai su fitinu su kuma shagala da kallonka akan TASBIHIN DA SUKEYI.
     Sai Annabi sulaiman(A.S)yace wa'azantar dani yake Tururuwa, sai Tururuwa tace kasan ko saboda me ake kiran sunan mahaifinka da DAUDA? Sai yace a'a sai tace da shi ana kiransa da Dauda saboda yayi maganin raunin da zuciyarsa take dashi, sai ta kuma cewa, Shin kasan ko saboda me ake kiranka da sulaiman? Sai yace a'a sai tace saboda kai ku'butaccene acikin abin da aka baka, saboda ku'butar zuciyarka, kuma ha'k'kine a gareka ka had'u da mahaifinka Dauda, sannan sai ta kuma cewa kasan ko saboda me Allah (S.W.T)ya hore maka iska? Sai yace a'a sai tace domin duniya iskace, sai Annabi sulaiman(A.S)yayi murmushi saboda maganarta, yana mai mamaki, shine wannan addu'ar wacce muka fad'a abaya.
        Nana Maimuna(R.A)ta bada labarin cewa Manzon Allah(S.A.W)ya hana a kashe masu tafiya akan 'kasa guda hud'u 4 daga cikin kwari da tsuntsaye, acikinsu akwai Tururuwa.
    Yana daga cikin abinda Allah(S.W.T)ya hore wa Annabi sulaiman(A.S)Horewa dayayi masa ta mutane da Aljanu da Tsuntsaye da 'kwari da shaid'anu sunayi masa aiki na duk abinda yaga dama, shine fadin Ubangiji(S.W.T)cewa:-
        "KUMA DAGA ALJANNU(MUKA HORE MASA)WANDA DA SUKE AIKI NAN GAMA GARESHI DA IZNIN UBANGIJI WANDA YA KARKATA DAGA CIKINSU, DAGA UMARNINMU SAI MU 'DAN'DANA MASA DAGA AZABAR SA'IRA"suratun saba'i aya ta (12).
      Haka Allah (S.W.T)ya wakilta wani mala'ika, wanda a hannunsa akwai wata bulala ta wuta, duk wanda Ya'ki bin umarnin Anmabi sulaiman(A.S)daga acikin Aljanu, sai ya dokeshi da ita nan da nan ya'kone.
        Daga cikin Aljanu akwai wad'anda suke nutso cikin ruwa, suke fito masa da nau'i nau'i na ma'adanai kamar lu'u lu'u da zubarjadi da ya'kutai, wad'annan Aljanu sune farkon wad'anda suka fara irin wannan aikin.

Zanci gaba insha Allahu

Musha ruwa lpy.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...5

 Abdullahi d'an Hamisu ya bada labari da isnadinsa, daga d'an mas'ud daga mahaifinsa, yace mun kasance tare da Manzon Allah(S.A.W)halin wata tafiya sai muka wuce ta wajan wata bishiya akanta akwai wasu 'ya'yan Kurciya guda 2 sai muka d'aukesu, sai wannan Kurciyar ta kawo 'kara gurin ma'aiki(S.A.W)sai manzon Allah(S.A.W)yace :-waye ya afkawa 'ya'yan wannan Kurciyar? sai mu kace mu ne, sai Manzon Allah(S.A.W)ya ce ku maida su gurbinsu.
        Ance Annabi sulaiman(A.S)ya ta'ba wuce wata turuwa akan hanyarsa ta zuwa mukibi, sai tururuwar take cewa, tsarki ya tabbata ga Ubangiji maigirma, mai yafi girma daga abinda ya bawa iyalan Annabi Dauda(A.S), sai Annabi sulaiman(A.S)yayi murmushi saboda maganar da wannan tururuwa ta fad'a, sai ya gayawa rundunarsa wannan magana, sai sukayi mamaki, sai Annabi sulaiman(A.S)Ya ce:-in baku labarin abinda yafi wannan ban mamaki? sai sukace na'am, sai yace:-wannan tururuwa ta kasance tana cewa, Kuji tsoron Allah a fili da 'boye, da kuma kyakkyawan nufi a gareshi ahalin wadata da Takauci, da kuma adalci lokacin fushi da lokacin yarda.
       An rawaito cewa, Annabi sulaiman(A.S) ya fita ro'kon ruwa a tare da shi akwai mutane da Aljanu, sai suka wuce ta gurin wata Tururuwa ta bud'e fuka fukanta ta d'aga hannayanta tana cewa, Ya Ubangiji mu halittace daga cikin halittunka ba mu da wadatuwa ga arzikinka, kuma kada ka kamamu da zunuban 'yan Adam ka shayar da mu, sai Annabi sulaiman(A.S)yace wa wad'anda suke tare dashi ku koma Ha'ki'ka   za'a shayar da ku da addu'ar wanin ku.
        Akwai kuma wata 'Kissa ta wadin Namli, wacce Allah Ubangiji(S.W.T)yace :- "KUMA AKA TATTARA, DOMIN SULAIMAN, RUNDUNONINSA, DAGA ALJANU DA MUTANE DA TSUNTSAYE, TO SU ANA KANGE SU(GA TAFIYA) "suratun Namli.
      HAR A LOKACIN DA SUKAJE KAN RAFIN TURURUWA WATA TURURUWA, TACE, YA KU JAMA'AR TURURUWAI ! KU SHIGA GIDAJANKU,KADA SULAIMAN DA RUNDUNONINSA SU KARKARYA KU, A HALIN BASU SANI BA"suratun Namli.
        Sha'abi da ka'ab sukace, Annabi sulaiman(A.S)ya kasance idan zai yi tafiya yana d'ora Ahlinsa da masu yi masa hidimada sakatarorinsa akan abin hawansa, su kuma dabbobi suna tafiya a gabansa tsakanin sama da 'kasa iska tana ri'ke da su,sun tafi zuwa yaman, sai suka bi ta madina wato birnin Manzon Allah(S.A.W)a yanzu, sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce, wannan shine gidan hijirar manzon Allah(S.A.W)wanda za'a aiko a 'karshen zamani, Aljanna ta tabbata ga wanda ya bishi kuma yayi imani da shi, sannan sai suka isa harami sai suka ga gumakan da ake bautawa, wad'anda ba Allah(S.W.T)ba, sun kewaye d'akin Allah, lokacin da Annabi sulaiman(A.S)ya wuce d'akin ka'aba, sai d'akin ka'aba ya kama kuka, sai Allah(S.W.T)yayi wahayi izuwa d'akin ka'aba da cewa, me yasa kake kuka,? sai d'akin ka'aba yace, ya Ubangiji wani Annabi ne daga cikin Annabakawanka, kuma tare da mutane daga cikin masoyanka, sun wuce ta kaina ba su sakko gareni ba, kuma ba suyi sallah a guri na ba, kuma ba su ambace ka a da'irata ba, kuma wad'annan gumakane a kewaye dani ake bauta musu bayan kai, sai Allah(S.W.T)yayi wahayi a gareshi da cewa kada kayi kuka da sannu zan cikaka da fuskoki masu sujjada a gareni, kuma zan saukar da Alkur'ani a cikinka,kuma zan aiko wani Annabi daga cikin Annabawa a 'karshen zamani daga gareka. mafi soyuwa a gare ni,kuma zan sanya wasu bayi a cikinka daga cikin halittuna masu yin bauta, kuma zan wajabtawa bayina wani abin wajabtawa wanda za suyi ta kwad'ayin tahowa zuwa gareka, kuma zan tsarkake ka daga masu bautar gumaka da shaid'an........
zanci gaba insha Allahu.

Asha ruwa lpy.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...4..


     Sannan Dan Futuhawaihi ya bada labari da isnadinsa daga Muhammad
d'an ka'ab cewa, Annabi sulaiman(A.S)yana da askarawa sun kai farsakhi d'ari 100,ishirin da biyar daga cikin na mutane ne, ishirin da biyar kuma na aljanu ne, ishirin da biyar kuma na 'kwari ne, ishirin da biyar kuma na tsuntsaye ne, yana kuma da gidage guda dubu 1000 na 'kawahir, acikin gidajan akwai gado d'ari uku 300 da mata d'ari bakwai 700, yana umar tar iska ta d'auke shi tayi yawo dashi, sai rannan yana yawo a tsakanin sama da 'kasa, sai Allah(S.W.T)ya yi masa wahayi da cewa:-
           HA'KI'KA NA 'KARA MAKA ACIKIN MULKINKA DA CEWA BABU WANDA ZAI YI MAGANA DAGA HALITTU DA WANI ABU FACE SAI ISKA TA ZO MAKA DA SHI TA BAKA LABARI.
       Yana daga cikin horewar da Allah(S.W.T)ya yiwa Annabi sulaiman(A.S) sanar da shi zancen tsuntsaye, kamar yadda Allah yake fad'a cewa:-
       DA FAD'AN ANNABI SULAIMAN(A.S) "YA KU MUTANE AN SANAR DA MU NAGANAR TSUNTSAYE." suratun namli.
         Dan Futuhawaihi yace da isnadinsa daga d'an ka'ab, idan DAWISU yayi kuka a gaban Annabi sulaiman(A.S)sai yace kun san abinda yake cewa? sai suka ce a'a yace ai cewa yake , kamar yadda kayi haka za'ayi maka.
      Alhuda-huda ma dayayi kuka sai Annabi sulaiman(A.S)yace kun san abinda yake fad'a?sai sukace a'a sai yace da su cewa yake yi, duk wanda bai jin 'kai ba, to shima ba za'a ji 'kan saba.
    kurciya ma tayi kuka sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce kun san abinda take cewa? sai sukace a'a, sai yace ai cewa take yi, tsarki ya tabbata ga Ubangiji mad'aukaki cikin samansa, da kuma cikin'kasan sa.
      kwado shi ma cewa yake yi SUBHANA RABBIYAL 'KUDDUSU, tsarki ya tabbata ga Ubangiji mai tsarki.
       Manzon Allah(S.A.W) ya ce :-idan zakara yayi cara cewa yake yi(UZKURULLAHA YA GAFILUN)ma'ana ku ambaci Ubangiji ya ku marafkana.
      Annabi sulaiman(A.S)yaci gaba da gaya musu cewa idan DAI'DAWI yayi kuka to cewa yake yi, ko wane rayayye matacce ne, kuma ko wane sabo tsoho ne.
     Annabi sulaiman(A.S)yaci gaba da fassara musu kukan tsuntsaye kala-kala, daga ciki akwai wanda yake cewa ku nemi gafara ya ku masu zunubi, akwai mai cewa ku gabatar da Alkhairi domin zaku sameshi, akwai mai cewa, kaicon wanda duniya ta zama abar bakin cikinsa, akwai mai cewa Mulkin Ubangiji ya daidaita, akwai mai cewa tsarki ua tabbata ga abin ambato a kowane guri, da dai sauransu domin kowace irin hakitta ka gani to akwai manufar halittar ta a wajan Ubangiji, kuma zamu iya lura da cewa duk sauran hilittun Ubangiji ashe suna yiwa 'Dan Adam gargad'ine da kuma tunatarwa akan MAHALICCI ALLAH.
zanci gaba insha Allahu..

asha ruwa lpy.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)....3..

 Allah Ubangiji(S.W.T)ya ce:-(KUMA SULAIMAN YA GAJI DAUDA)suratun namli.
    Abin nufi anan shine ya gaji Annabtar sa, da hikimar sa, da ilmin sa, Duk da cewa Annabi Dauda(A.S)yana da 'ya'ya goma sha tara(19).
      MU'KATIL yace:- Annabi sulaiman(A.S)ya kasance akan mulki mafi girma ga na mahaifinsa Annabi Dauda(A.S)da kuma iya hukunci, shi dai Annabi Dauda(A.S)ya kasance mai yawan ibada ne akan d'ansa Annabi sulaiman(A.S), kuma Allah (S.W.T)ya bashi mulki da hikima yana 'Dan shekara goma sha uku(13),Shima yana daga cikin mutum hud'u wad'anda suka mulki duniya gaba d'aya.
     Annabi sulaiman(A.S)ya kasance fari kuma mai jiki mai haske,kuma kyakkyawa, mai yawan gashi,yana sa fararen tufafi, kuma ya kasance mai yawan tsoran Allah(S.W.T) kuma mai tawadhi'u yana cud'anya da miskinai, kuma yana zama dasu, yana cewa miskini ya zauna da maikinai.
       Mahaifinsa Annabi Dauda(A.S)ya kasance yana shawara da shi a lokacin mulkinsa akan al'amura masu yawa, duk da cewa 'karami mai 'kananan shekaru, amma yana da cikakkyan hankali da ilmi.
          Allah Ubangiji(S.W.T)ya ke'benci Annabin sa Annabi sulaiman(A.S)da wasu darajoji da kuma kyaututtuka na baiwa, Ubangiji yana cewa:-
(HAKIKA MUN BAI WA DAUDA DA SULAIMAN ILMI, KUMA SUKA CE GODIYA TA TABBATA GA ALLAH,WANDA YA FIFI TA MU AKAN MAFI YAWA DAGA BAYINSA MUMINAI.)suratun namli;
     Kuma Ubangiji ya fad'a acikin Al'kur'ani mai girma tana mai bada labari akan Annabi sulaiman(A.S):-
YACE"YA UBANGIJI:KA GAFARTA MINI, KUMA KA BANI MULKI WANDA BAI KAMATA GA KOWA BA BAYANA".
"LALLAI KAI NE MAI YAWUN KYAUTA".
      Annabi sulaiman(A.S)yayi wannan addu'a ne Domin kada wani yayi alfahari da sarauta a bayansa, Ya halaka kuma ya halakar da wani,saboda sarauta itace asalin girman kai da alfahari.
      sai Allah ya amsa addu'ar sa ya kuma girmamashi da wasu abubuwa wanda Allah bai ta'ba horewa wani su ba, daga cikin hakittar sa ba kafin Annabi sulaiman(A.S)daga cikin hotewar da Allah(S.W.T)yayi masa daga iska, Ubangiji mad'aukakin sarki yana cewa:-
"SABODA HAKA MUKA HORE MASA ISKA TANA GUDU DA UMARNINSA, TANA TASHI DA SAUKI,INDA YA NUFA."Suratu..
       Malamai suka ce an hore masa iska a matsayin dawakan da ya yanka domin Allah, Saboda Annabi sulaiman(A.S)ya yanka dawakan ne saboda kallonsu ya hana shi sallah, wacce ita sallar farillace ta dole a kansa, amma tattalin kayan ya'ki farillace ta wani zai iya d'aukewa wani.
    sannan kuma an hore masa Aljanu domin niyyarsa ta samun 'ya'ya masu jihadi domin Allah.
     Malam muhammad Dan Is'hak yace, Annabi sulaiman(A.S)ya kasance mutum ne mai yawan ya'ki Baya iya zama ba tare da ana gwabza ya'ki ba,dan baya iya jin d'uriyar wani sarki a sassan duniya,face sai ya ya'ke shi, kuma ya nuna masa karfin mulki sa, Ya kasance idan yayi nufin ya'ki yana sa askarawansa su 'kera masa wani abu kamar girji na katako sannan sai a d'ora masa gadonsa akai sannan duk sauran jama'a da dabbobi su hau a kuma zuba kayan ya'ki kala-kala akai, bayan an gama shirya komai sai ya umarci iska ta d'aukeshi zuwa inda ya nufa,  an ce suna yin tafiyar wata a yammaci d'aya, kuma suna yin tafiyar wata a safiya d'aya, tana tana tafiya da shi duk inda ya so, shine fad'in Ubangiji(S.W.T):-
"KUMA GA SULAIMAN, MUN HORE MASA ISKA,TAFIYARTA TA SAFIYA DAIDAI DA WATA,KUMA TA YAMMA DAIDAI DA WATA."Suratu sabi'i.

......Zanci gaba insha Allahu

JUMA@ KAREEM..
 RAMADHAN KAREEM..

MUNSHA RUWA LAFIYA.

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...2

Sai Annabi Dauda(A.S)ya tashi ya hau kan mumbari ya yiwa Allah(S.W.T)godiya yayi yabo agareshi, sannan yace Allah(S.W.T)ya umarce ni da in khakifantar muku da Annabi sulaiman(A.S), sai Banu isra'ila suka fusata suka ce wannan yaron mai 'Karancin shekaru za'a khakifantar mana al hali a cikinmu akwai wad'anda suka fishi d'aukaka da ilmi?
        sai Annabi Dauda(A.S)yaji abinda suke fad'a sai ya kirawo manya-manyansu yace dasu naji abinda kuke fad'a, To amma kowa ya zo min da sandar sa duk wanda sandar sa tayi tsiro to shine zai zama khakifa a bayana, sai sukace sun yadda, sai kowa yaje ya kawo sandar sa, sai Annabi Dauda(A.S)yace kowa ya rubuta sunan sa a jikin sandar sa, sai duk suka rubuta sunayansa.
     sai Annabi sulaiman(A,S)ya zo da sandar sa ya rubuta sunansa shima a jikin ta, sai aka sa sandunan ackin wani d'aki aka kulle 'kofar aka datse da mukulli, aka kuma sa masu dagi daga cikin manyan shuwagaban nin su.
      Bayan asuba tayi Annabi Dauda(A,S)yayi sallar Asuba da su, Gari kuma ya waye, sai aka bud'e wannan d'akin aka fito da wad'annan sanduna kamar yadda suke, Amma sandar Annabi sulaiman(A,S)sai  akaga tuni tayi ganye kuma tayi 'ya'ya.
     sai sukace kai mun mi'kawa Annabi Dauda(A,S) wannan al'amarin, Da Annabi Dauda(A,S)sai ya godewa Allah(S.W.T,) sai ya d'ora Annabi sulaiman(A.S)a kusa da shi, sai yace da Bani isra'ila wannan shine khalifanku a baya na.
     Wahabu d'an munabbahu yace:- lokacin da Annabi Dauda(A.S)ya khalifantar da d'ansa Annabi sulaiman(A.S)ya yi masa wa'azi da cewa:-
            Ya kai 'karamin 'Da na kashedinka da fushi, domin fushi yana wulakanta ma'abocin sa, sannan kaji tsoran Allah(S.W.T)da kuma biyayya a gareshi,domin suna rinjayar ko wane irin abu ne, kada kuma ka yawaita kishi ga mutananka ba tare da wani abu ba,Domin hakan yana gadar da mummunan zato ga mutane koda kuwa ku'butattune, ka yanke kwad'ayi ga abin hannun mutane , Domin hakan wadata ce, kuma kada ka yi kwad'ayi domin shi talauci ne mahalarci, kuma kashedinka da fad'ar abinda zai yi maka wahalar cikawa da kuma abinda zai yi maka wahalar aikatawa, ka kuma tsaida kanka da harshen ka akan gaskiya, ka kuma lazamci kyautatawa, idan kuma kana da ikon Alkhairinka na yau zaifi na yau zaifi na jiya to ka aikata, ka kuma yi sallah irin sallar mai ban kwana, kamar bazaka kai gobe ba, kada kuma ka zauna da wawaye,kada kuma ka gayawa malami mummunar magana, kada kuma kayi jayayya da shi akan addani,idan kuma kayi fushi to ka zauna, kuma ka canja guri, ka 'kaunaci rahamar Ubangiji, domin rahamar Ubangiji ta yalwaci komai.
        sannan ance lokacin da aka khalifantar da Annabi sulaiman(A.S)sai ya 'Boye al'amuran sa, ya kuma auri wata mace, ya kuma 'Buya ga mutane, ya fuskanci ilmi da kuma ibada, wata rana wannan matar tasa take cewa bata taba ganin mutum mai kyawun d'abi'u irin saba, kuma mai dad'in 'kamshi ba........

zanci gaba insha Allah

musha ruwa lpy..

TARIHIN ANNABI SULAIMAN (A.S)..1..

  Annabi sulaiman(A.S)shine 'dan Annabi Dauda(A.S)Abu Huraira(R.A)ya ce Allah ya saukarwa da Annabi Dauda(A.S)littafi wanda yake dauke da Tambayoyi guda goma sha uku(13),sai Allah(S.W.T)yayiwa Annabi Dauda(A.S)wahayi akan ya Tambayi 'dan sa Annabi sulaiman(A.S)wannan Tambayoyi guda goma sha uku(13), in ya amsa su to shine Khalifa a bayan sa.

     Sai Annabi Dauda(A.S)ya kirawo malaman Bani Isra'ila guda (70)da kuma masu yawan Bauta a cikinsu, suma guda saba'in(70) sai ya zaunar da Annabi Sulaiman(A.S) a gabansu, sai yace:-ya kai 'karamin dana ha'ki'ka Ubangiji ya saukar min da wani littafi daga sama acikinsa akwai Tambayoyi , ya kuma Umarce ni da in yi maka Tambaya akansu, idan ka amsa su to kaine khalifa a baya na, sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce:-To! Annabi zai yi min Tambaya akan abinda aka bayyana masa , amma Dogarona yana ga Allah (S.W.T).
       Sai Annabi Dauda(A.S)yace ya kai d'an 'karamin 'dana:-
menene yafi ko wane abu kusanci kuma
menene yafi kowane abu nisa?
menene  kuma yafi  'debe kewa ga Al'amura
menene kuma yafi muni ga Al'amura?
menene yafi kyau ga sauran abubuwa
menene kuma yafi muni ga sauran abubuwa?
menene yafi 'kankanta ga abubuwa
kuma menene yafi yawa ga sauran abubuwa?
kuma wanne abubuwa ne guda biyu a tsaye
wanne abubuwa ne guda biyu suke kai kawo?
kuma wanne abubuwane guda biyu sukayi Tarayya kuma wane abubuwa ne guda biyu ma'kiyan juna?
kuma wane abune idan mutum ya haushi za'a gode masa 'karshen sa, kuma wane abune idan mutum ya haushi za'a zarge shi a 'karshen sa?

   Sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce:-Abin da yafi kowa ne abu kusanci itace lahira, Abinda yafi kuma kowanne abu nisa kuwa shine abinda ya tsere maka daga duniya.
  Abun kuma da yafi 'debe kewa ga Al'amura abin da yake sujjada a tare da shi akwai rai, abin da yafi kowane abu muni shine abinda yayi sujjada babu rai a tare da shi.
    Abu mafi kyawun sauran bubuwa kuwa shine imani bayan kafirci, mafi munin abubuwa kuma shine kafirci bayan imani.Abu mafi 'kankanta kuwa shine ya'kini.
   Abu mafi yawa ga sauran abubuwa kuma shine kokwanto.
   Abubuwa biyu da suke tsaye sune kasa da sama, wadanda suke kaikawo sune rana da wata.
    Abubuwan da sukayi tarayya ga juna sune dare da rana, ma'kiya ga juna kuma sune mutuwa da rayuwa.
   Al'amarin da idan ka haushi kuma za'a gode maka a 'karshen sa shine Ha'kuri lokacin fushi, wanda kuma za'a zarge ka a 'karshen sa shine Hukunci lokacin fushi.

   Sai Annabi sulaiman(A.S)yace wannan shine jawabin wannan Tambayoyi dai dai yadda aka saukar daga sama.
   Sai wad'annan malaman Bani Isra'ila da kuma masu yawan Bautar a cikin su suka ce Basu yadda ba har sai suma sunyi masa wata Tambaya, idan ya amsa sun yadda da shine khalifa, sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce:-ku tambaye ni ni dai dogarona shine Allah(S.W.T).
   Sai sukace da shi, wane abune idan ya gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ya 'Baci dukkan jiki ya 'Baci? sai yace Zuciya..........zanci gaba. insha Allahu.

  Allah ya gyara mana zuciyarmu.
Asha ruwa lpy.

Monday, March 9, 2020

KABARI LAMBUNE DAGA ALJANNAH KO KUMA RAMI DAGA JAHANNAMA

Ba wani yini da zai shude,face kabari ya yi shela, ya ce, 'Ni ne gida na daji, ni ne gidan kadaici, ni ne gidan tsutsotsi da ƙwari.'

Yayin da aka binne mumini a cikin ƙabari, ƙabarin zai yi misa maraba, yana cewa, 'Maraba da zuwan ka nan, ka kyauta da ka zo nan. A cikin dukkan masu tafiya bisa bayan ƙasa, kai ne na fi so. A yanzu da aka kawo ka zuwa gare ni. za ka ga mafi kyawun hali na'

Daga nan sai ƙabari ya yi fadi, kwatankwacin iyakar ganin mutum, sai a bude kofar Aljannah a cikin sa. Ta cikin wannan kofar, iska mai kanshin turaren Aljannah za ta dinga zuwa gareshi.'

Amma idan aka binne kafiri ko mai ƙetare iyakokin Allah Ta'ala, ƙabari zai ce, 'Ba na maraba da zuwan ka nan, kuma zuwan ka abin kyama ne. Da ba ka zo nan ba, da ya fi maka. Daga cikin dukkan masu tafiya a bisa doron ƙasa, kai ne na fi ƙi. A halin yanzu an kawo ka zuwa gare ni, kuma za ka ga irin aiki na'

Daga nan sai ya matse shi da tsakanin gaske, har sai hakarƙarinsa sun sarke da juna kamar yadda yatsun hannuwa biyu suke kurɗawa a tsakanin juna. Daga nan sai a sako masa kumurci casa'in ko casa'in da tara, za su ci gaba da yagar sa har zuwa tashin Alkiyamah.

Da daya daga cikin kumurcin zai huro dafin sa a bisa doron ƙasa, da ba wata ciyawa da za ta sake tsiro wa a kanta, har tashin Alkiyamah. Daga nan sai Manzon Allah (S.A.Ws) ya ci gaba da cewa, 'Ƙabari lambu ne daga Aljannah ko kuma rami daga Jhannama.

Ya Allah ka kare mu daga azabtar Kabari kasa Aljannar Firdausi itace makomarmu. Ãmīn ya Qādiyal Hājah~ ahmadmusainc.blogspot.com