Thursday, November 11, 2021

FALALAR RANAR JUMA'A

FALALAR RANAR JUMU'AH Idan Allah Ya baka ikon karantawa daure kayi share domin duka mu amfana. An karbo daga Aus ibn Aus (RA) Annabi (Saww) Ya ce, "Wanda ya yi wanki, ya yi wanka, ya matsa kusa, ya yi sammako, ya kusanto liman ya saurari huduba a ranar jumu'a, zai sami ladan tsayuwar shekara daya da azuminta da dukkan tako da ya yi. (Imamu Tirmiziy da Nasa'i suka rawaito shi). Haka Kuma an karbo hadisi daga Anas (RA) ya ce, An bijiro da sallar Juma'a ga Manzon Allah (saww).
Mala'ika Jibrilu ne ya zo masa da ita a tafinsa kamar farin adubi, a tsakiyarsa akwai wani baqin digo, sai ya ce: "Menene wannan ya jibrilu?" Ya ce masa, "Wannan ita ce Juma'a Ubangijinka yake bijiro da ita a gare ka; domin ta kasance idi a gareka da alummarka a bayanka, kuma ku kuna da alheri a cikinta, wanda kai ne za ka zama na farkon samunsa, kuma yahuduwa da nasara su zama a bayanka. Kuma a cikinta akwai wata sa'a babu wani bawa da zai yi addu'a a cikinta ta alheri da yake rabonsa ne, face an ba shi, ko ya nemi tsari daga sharri face an ije masa mafi girma daga abin da ya nema, kuma mu a sama muna ambatonsa ranar qari. (Dabarani ne ya rawaito shi a cikin Al-Ausat da isnadi mai kyau). Hakika wannan falaloli ne masu girma da kyawo, muna rokon Allah ya datar damu wayannan Falalolin.

Wednesday, October 27, 2021

MUTANE MA HAKA SUKE BALLANTAN DABBOBI

MUTANE MA HAKA SUKE BALLANTANA DABBOBI? Wata rana wani daga cikin magabata ya aika dansa kasuwa ya siyo masa hanta. Da ya siyo sai ya samu wuka mai kaifi ya yanyanka hantar. Sai ya bar wukar bai wanke ba, sai magensu ta zo tana lasar jinin da ke jikin wukar. Tana lasa harshenta na tsagewa jini ya biyo wukar. Da yaron nan ya zo ya ga magen tana ji wa kanta ciwo, sai ya daka mata tsawa; ya kore ta. Sai kawai magen nan ta dinga gurnani, tana nuna fushinta, ya hana ta abin da take jin dadi. Da yaron ya ga haka, sai ya ce: "Ikon Allah! Kina cutar da kanki, don na hana ki, sai ki ji haushi na. Sai baban nasa ya jiyo shi yana magana, sai ya ce da shi: "Kai da wa kake magana kai kadai. Sai ya ce: baba ka ji, ka ji... Sai Baban ya ce: ai ba dabbobi ba, mutane ma haka suke. Idan suna aikata abin da zai cutar da su (sabon Allah) idan ka hana su sai su ji haushinka. Sai ya ce: to, baba ba sai a kyale su ba tun da kansu suke cutarwa. Sai ya ce: A'a, ai idan ka kyale su suna aikata barna, ba ka hana su ba, idan azaba ta zo, sai ta hada da kai. Amma idan ka hana su, idan suka hanu, to kai da su duk kun tsira. Idan kuma ba su hanu ba, to kai ka kubuta. Wannan kisar sai ta tuna min hadisin: عن النُّعْمَانَ بْنَ بَشِيرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " مَثَلُ الْقَائِمِ عَلَى حُدُودِ اللَّهِ، وَالْوَاقِعِ فِيهَا، كَمَثَلِ قَوْمٍ اسْتَهَمُوا عَلَى سَفِينَةٍ، فَأَصَابَ بَعْضُهُمْ أَعْلَاهَا، وَبَعْضُهُمْ أَسْفَلَهَا، فَكَانَ الَّذِينَ فِي أَسْفَلِهَا إِذَا اسْتَقَوْا مِنَ الْمَاءِ مَرُّوا عَلَى مَنْ فَوْقَهُمْ، فَقَالُوا : لَوْ أَنَّا خَرَقْنَا فِي نَصِيبِنَا خَرْقًا، وَلَمْ نُؤْذِ مَنْ فَوْقَنَا، فَإِنْ يَتْرُكُوهُمْ وَمَا أَرَادُوا هَلَكُوا جَمِيعًا، وَإِنْ أَخَذُوا عَلَى أَيْدِيهِمْ نَجَوْا وَنَجَوْا جَمِيعًا ". أخرجه البخاري (٢٤٩٣)، والترمذي (٢١٧٣)، وأحمد (١٨٣٦١) TSOKACI: Kada zaton idan ka yi inkarin mummuwan abu, ba za a daina ba ya sa kana ganin munkari ka ki hanawa. ALLAH YA BA MU DACEWA

Sunday, October 17, 2021

Gwamnatin tarayya ta saki sunayen mutum 10,000 da zata baiwa bashin NYIF

Ministan Matasa ya bayyana adadin matasan da za’a baiwa sabon bashin jari Ministan yace za’a basu horo na musamman don tabbatar da sun kashe kudin yadda ya kamata READ ALSO Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari ‘Yan bindiga sun sace tagwayen ‘yan mata, Direba da wasu Dogaran Sarki a Najeriya Wannan shine zango na biyu na shirin NYIF da gwamnatin ta kaddamar Abuja – Gwamnatin tarayya a ranar Talata, ta ce an sake sakin sunayen mutum 10,000 da a’a baiwa tallafin kudin jari karkashin shirin Tallafin matasa a Najeriya (NYIF). Gwamnatin tace wannan ya biyo bayan mutum 5,285 da aka saki sunayensu da farko. Wannan na kunshe cikin jawabin da Kola Daniel, mai magana yawun Ministan wasanni da matasa, Sundaye Dare, ya saki, rahoton Tribune. Ya bayyana cewa za’a horar da wadanda aka zaba kuma za’a raba musu kudaden da akayi alkawari. Jawabin Ministan ya kara da cewa an zabi sunayen matasan ne bayan tantance matasa milyan uku da suka nemi bashin. Yace: “Bayan kammala sahun fari, NIRSAL ya fitar da sunayen mutane 10,000 don horar da su da kuma basu kudin jarin.” “Bashin da za’a bada ya fara daga dubu dari biyu da hamsin 250,000 zuwa milyan uku (N3,000,000) “Wadannan sunaye na kan shafin FMYSD da NOYA.” “Dukkan wadanda aka zaba zasu yi horo don tabbatar da cewa sun yi amfani da bashin yadda ya kamata.” October 16, 2021 Adesina: Buhari ya fi Azikiwe, Awolowo da Aminu Kano farin jini wurin ‘yan Najeriya HAUSA NEWS Adesina: Buhari ya fi Azikiwe, Awolowo da Aminu Kano farin jini wurin ‘yan Najeriya October 15, 2021 Neja: Mafarauta Da Ƴan Sa-Kai Sun Kashe Ƴan Bindiga Da Dama a Harin Kwantar Ɓauna HAUSA NEWS Neja: Mafarauta Da Ƴan Sa-Kai Sun Kashe Ƴan Bindiga Da Dama a Harin Kwantar Ɓauna October 15, 2021 Duk wanda baya Maulidi ba musulmi bane — Farfesa Maƙari HAUSA NEWS Duk wanda baya Maulidi ba musulmi bane — Farfesa Maƙari October 14, 2021 Leave a Reply Your email address will not be published. Required fields are marked * Comment Name * Email * Website Save my name, email, and website in this browser for the next time I comment. POPULAR NEWS An Fara Approve Na Sabon Tsarin Rancen Kuɗi Marar Ruwa Wato “Tcf Covid19 Non Interest Loan. Tallafin Covid-19 in kaga an turo maka wannan sakon to kana cikin wadanda za’a biya September 22, 2021 Yadda Ake Karbar Kudin Tallafin Covid-19 Yadda Ake Karbar Kudin Tallafin Covid-19 October 3, 2021 Yadda Zaka Gane Anturo Maka Da Sakon Covid-19 Loan Ka Kuma Amince Yadda Zaka Gane Anturo Maka Da Sakon Covid-19 Loan Ka Kuma Amince October 7, 2021 Gwamnatin tarayya ta saki sunayen mutum 10,000 da zata baiwa bashin NYIF Gwamnatin tarayya ta saki sunayen mutum 10,000 da zata baiwa bashin NYIF October 13, 2021 Yadda Organization Zasu Amfana da N100,000 a Tsarin Nigeria Jubilee Fellows Programme. Yadda Organization Zasu Amfana da N100,000 a Tsarin Nigeria Jubilee Fellows Programme. October 9, 2021 EDITOR'S PICK Have you Applied for CBN Covid-19 Loan and not yet Approved (Here is what to do) Have you Applied for CBN Covid-19 Loan and not yet Approved (Here is what to do) August 6, 2021 Keep Calm And Curry On: Must-Try Japanese Restaurants in Bali July 9, 2021 Sarkin Kano Aminu Bayero a karkashin bincike kan badakalar filaye na N1.3billion. Sarkin Kano Aminu Bayero a karkashin bincike kan badakalar filaye na N1.3billion. April 4, 2021 Survival Funds Zasu Cigaba Da Biyan Naira Dubu 30,000 Survival Funds Zasu Cigaba Da Biyan Naira Dubu 30,000 May 18, 2021 About We bring you the best Premium WordPress Themes that perfect for news, magazine, personal blog, etc. Check our landing page for details. Follow us Categories Business Entertainment Fashion Food Hausa Hausa News Health Lifestyle National News Opinion Politics Science Tech Travel Uncategorized World Recent Posts Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari ‘Yan bindiga sun sace tagwayen ‘yan mata, Direba da wasu Dogaran Sarki a Najeriya Gwamna El-Rufai ya sanar da dalilin kirkirar hukumar kula da kwaryar birane a Kaduna Adesina: Buhari ya fi Azikiwe, Awolowo da Aminu Kano farin jini wurin ‘yan Najeriya Buy JNews Landing Page Documentation Support Forum © 2021 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme. Search... Homepages News Politics National Business World Entertainment Fashion Food Health Lifestyle Opinion Science Tech Travel © 2021 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

Sunday, August 29, 2021

Labarin wani Sarki mai hikima.

 



*QISSA📓📚📓*

Labarin wani Sarki mai hikima. 

    A zamanin da can akwai wani gari da suke za6ar sarki wanda zai mulkesu na tsawon shekara daya kacal, idan shekara tayi sai su dauki wannan sarkin su dorashi akan giwa sannan su zagaya dashi cikin gari don yayi ban kwana da jama'ar wannan gari.
     Bayan an gama zagayawa da wannan sarki sai azo a dorashi akan jirgin ruwa a kaishi wani jeji mai nisa da wannan gari a ajiyeshi, anan zai gama rayuwarsa har ya mutu su kuma sai su dawo su sake za6ar wani sarkin, wannan itace al'adar wannan gari.
     Wata rana bayan sun kai wani sarki wannan daji suna dawowa sai suka ga wani jirgin ruwa wanda yake dauke da wani saurayi da yayi hatsari har ya nutse a cikin ruwa.
      Da ganin haka sai suka ceto wannan saurayi sannan suka daukeshi suka kaishi garin su, sannan suka rokeshi akan yazama sarkin su bayan sun masa bayani akan wannan al'ada tasu.
      Da farko ya nuna baya son wannan sarauta amma daga baya sai ya amince ya amshi wannan sarauta.
     Bayan kwana uku da nadashi sai ya tambaye wazirin sa da cewa, "Shin zaku iya kaini wannan jeji da kuke kai sarakuna tun kafin watanni sha biyu su cika? Sai wannan waziri nashi yace, " Me zai hana? Sai kuwa suka daukeshi suka kaishi wannan daji sai wannan sarki yayi duba zuwa dajin yaga gawarwakin sarakuna da suka gabata a yashe akan kasa, sannan kuma wannan daji bashi da tsari don kayoyine da miyagun namun daji masu hatsarin gaske a ciki.
     Koda wannan sarki yaga haka sai nan da nan yayi umarni ga mayakansa da subi dukkan namun dajin su kashe, cikin dan kankanin lokaci suka karkashe wasu kuma suka gudu.
       Bayan da sarki ya dawo gida sai ya yasa aka tara masa katti majiya karfi har mutum dari, sai ya dauke su aiki akan suje su tsaftace masa wannan daji sannan su kawar da gawarwakin sarakunan da suka gabata da kuma na wadannan namun daji sannan su sassare bishiyoyin da suke dajin.
     Bayan sun samu watanni biyu sai suka tsaftace daji, sai sarki yayi umarni da a shuka kayan marmari sannan a sanya kananan dabbobi irin su agwagwi, kaji, shanu, tumaki, sai sarki yasa aka gina gida a wannan daji babba, kuma asa jiragen ruwa a gefen gidan.
      Don haka duk lokacin da hakimansa suka yi masa kyutar dukiya to sai yaje ya 6oye ta a wannan gida da aka gina masa a daji.
      Bayan cikarsa wata tara akan wannan mulki sai ya tara hakiman sa sannan yace musu, "Na sani a tsarinku kuna kai sarakunanku ne waccan jejin bayan watanni sha biyu to nidai a halin yanzu nake so a kaini tun yanzu.
    Da jin haka sai suka ce dashi, Bazai yiwuba domin hakan ya sa6awa al'adarsu don haka sai dai ya jira har bayan watanni uku sannan a kaishi.
     Hakan wannan sarki ya hakura har sai da yakai watanni sha biyu sannan suka daurashi akan wata katuwar giwa kuma suka sanya masa kayan alfarma masu tsada suka dinga tsagayawa dashi cikin gari mutane na masa ban kwana.
     Amma abin da yafi basu mamaki yadda wannan sarki yake daga musu hannu yana musu murmushi sa6anin wadancan da suke kuka, suka tambaye shi dalilinsa na yin murmurshi da murna, sai yace musu, " A lokacin da aka haifi jinjiri idan yazo duniya kuka yake yi wadanda ke kusa dashi suna murna, don haka kayi kokari kayi tanadi ta yadda zakabar duniyar kana farin ciki, su kuma wadanda ke gefen ka suna kuka, sarakunan da suka gabata sun shagaltu ne da jin dadi a lokacin mulkinsu ni kuma na shagaltu ne da gyran makomata har sai da wajen ya zama lambu ta yadda zanyi rayuwa ba tare da wata matsala ba.

_Da wannan nake jan hankulan mu da mu gaggauta gyara makomarmu don mu samu kyakkyawan karshe tun kafin lokaci ya kure domin duk wanda yake raye to wata dama ne da Allah ya bashi don ya gyara makomarsa._
     _Allah ya bamu dacewa da kyakkyawar karshe_

Saturday, August 28, 2021

INDA KARYA TA HALATTA A MUSULUNCI

 INDA KARYA TA HALATTA A MUSULUNCI



*TAMBAYA*❓

Aslm Mlm kn lpy Malam tambaya nake da ita 
A musulunci akwai inda karya ta halatta

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Karya dai haramun ne ga musulmi, kuma wajibe ne ya kaurace mata a ko wane irin hali. Karya don gyaran al’umma, aure ko kwato hakki babu laifi a cikinta, hasilima makaryacin da duk wanda ya taimakama karyar yana da lada. Hadisi ya inganta daga Bukhari da Muslim, Ummu Kulsum (R.A) ta ce: Annabi Salallahu Alaihi Wasallama ya ce: mai sulhunta. mutane ba makaryaci ba ne: yana fadin alhairi kuma yana burin alhairi.

Ummu Kulsum (R.A) ta kara da cewa banji Annabi SAW yana sauki da yin karya ba a cikin maganganun mutane, sai dai cikin abu Uku: yaki, sulhunta mutane, da zancen mata da miji.

*INDA KARYA TA HALATTA*

Koda yake Karya haramun ne a asalinta, amma tana iya halatta harma da zamo wajibi mutun yayi karyar. Lura da wannan tambaya, karya ta halatta a gurare kamar haka:

1) Karya ta halatta a lokacin YAKI domin razana da tsorata abokan gaba.
2) Karya ta halatta don sulhunta musulmai da dai-daita tsakanin su.
3) Karya ta halatta don inganta rayuwar ma’aurata.
4) Karya ta halatta domin kwato hakkin mai rauni.
5) Karya ta halatta domin kare fitina da barna a bayan kasa.

*SHARUDDAN HALATTA KARYA*

Lalle karya laifi ce cikin manyan laifuka (Kaba’ir), kuma Allah baya yafe laifin karya sai dai tuba ta gaskiya. Karya na kai mai yin ta zuwa ga fajirci, shi kuma fajirci na kai mutum zuwa wuta. Makaryaci ba zai gushe ba yana karya har sai an rubuta shi a matsayin makaryaci a gurin Allah. Don haka musulmi ya kiyayi karya a rayuwar sa.

Karyar da ta halatta wanda mai ita kan iya samun lada, sai ta cika sharudda kamar haka:

1) Sai lamarin ya kasanci babu mafita a cikin sa idan bakaryar aka yiba.
2) Manufan karyar ya kasance maslaha ne kuma alhairi ne kuma babu cutarwa.
3) Kuma a tuba daga baya a nemi gafarar Allah.

Allah muke roko ya gafarta mana baki daya.

Friday, August 20, 2021

TARIHIN KUNGIYAR TALIBAN

 

TARIHIN KUNGIYAR TALIBAN


KUNGIYAR TALIBAN

Daga Alkalamin wani bawan Allah

Mulkin Kasar Afghanistan dai a yau ya koma hannun Taliban, sai naga ya dace na warware wasu daya cikin al’ummar mu wani abu mai rikitarwa game da su:

(1) Wannn suna Taliban, a harcen su na Pashtun yana nufin jam’in dalibai, kamar Musulman ne, abinda ke nufi jam’in Musulmi, su Dalibai ne wadanda suka gogu a karatun zaure, kamar yadda yake a al’adar Kasar su

(2) Mazhabarsu ta Aqeedah Maturidiyya ce ta Abu Mansur Almaturidi, daya ne daga cikin manyan Malaman Sunnah na zamaninsa, Mazhabarsa tana kusa sosai da Mazhabar Abul Hasanil Ash’ari.
Yadda wasu suke munana zato a garesu, Taliban a gurin ‘yan Boko Haram da ISIS suna musu kallon ‘yan bidi’ah ne wadanda jininsu ya halatta, saboda wai Taliban sun sabawa mazhabar Salafiyya wadanda suke binta

(3) Taliban Mazhabarsu ta Fiqhu Hanafiyya suke bi, don Mazahabarsa ce ta yadu a Kasashen su tun farkon zuwan Musulunci, kuma da ita suke shari’ah, kamar dai mu nan Nigeria muke bin mazhabar Malikiyyah

(4) Taliban basu da dangantaka da wata kungiyar ta’addancin addini ko siyasa, balle kungiyoyi masu yawan kafirta Musulmi

(5) Amurka ta tuhumi Taliban da goyon bayan ta’addanci saboda kin mika musu Usama bin Laden don su hukuntashi a shekarar 2001, su kuwa Taliban sunyi aiki da ilmin da suka sani wanda ya haramta sallama Musulmi ga kafurai, har suka yarda da gushewar mulkinsu akan dabbaka Sunnar Manzon Allah (SAW)

(6) Taliban kwararru ne kuma gogaggu ne a iya mulkin jama’a, ba kamar yadda kafofin yada labaran turai ke bata su ba, ko da yake ba’a rasa su da wata kura-kurai wadanda ba wani ‘dan adam dake iya rabuwa da kuskure, amma alherinsu yafi kuskurensu yawa nesa ba kusa ba.
Kuma mulkinsu a Kasar Afghanistan yafi na Amurkawa masu yada addinin Kiristanci karfi da yaki, kamar yadda yafi na Iran da take kokarin shiga ta yayyaga Kasar, ta yada shi’anci kamar yadda takeyi yanzu haka a Iraqi

(7) Wasu mutane na yi musu hukunci da nau’in tufafinsu, ace wai suna tauye hakkin mata, suna yi musu kulle, wannan ba haka bane, irin tufafinsu na al’ada suke sawa mazansu da matansu, ko zaman Amurka a Kasar na shekara 20 bai canza matansu daga yin lullubi da sanya niqabi ba


(8) Bayyanar kungiyoyi masu da’awar jihadi na duniya irinsu Boko Haram, ISIS da sauransu ya sa wasu Musulmi ba su son jin maganar jihadi, abinda ke sa su jin tsoron Taliban, alhali Taliban ta banbanta da irin wadancan kungiyoyi masu yawan kafirta Musulmi.

Su Taliban mutane ne masu kokarin adalci hatta ga abokan gabar su, kuma kasancewar su jagorori a Kasar Afghanistan yafi alheri akan Amurka (Kafirai) ko Iran ‘yan shi’ah

Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmai a duk inda suke Amin


Thursday, August 19, 2021

TARKON MUTUWA A JOS

 

TARKON MUTUWA A JOS

TARKON MUTUWA A JOS

ABINDA YAKE FARUWA ANA KASHE MUSULMAI MATAFIYA A JOS

Kabilar Birom da Irigwe sun fi shekara 20 suna tare hanya suna yanka Musulmai, har babban soja Janaral sun kashe, kuma har zuwa yau babu wani mataki da aka dauka

Mutanen da aka kashe jiya a Jos mutanen jihar Kwara ne da Ondo, kuma Musulmai ne gaba dayansu, sun fito daga Bauchi bayan kammala taron zikiri da addu’ah karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Sun tashi da sassafe daga Bauchi zasu koma jihohin su, sai suka bi ta Jos, saboda duk wanda ya fito daga Borno, Yobe, Adamawa, Gombe da Bauchi zai je Abuja to sai yabi ta cikin birnin Jos saboda yafi sauki da kusa

Cikin birnin Jos yana da fadi sosai, kuma akwai hanyoyi da yawa, idan mutum ba ya saba bin hanya ba to zai iya 6ata, kuma ko kasan hanya sai ka kai a kalla awa daya kana tafiya a cikin birnin Jos kafin ka dauki hanyar zuwa Abuja

Sakamakon rikicin da akayi a Jos tun bayan shekaru 20 da suka wuce, har yau akwai anguwanni da hanyoyi a cikin Jos wanda Musulmi bai isa ya bi ko ya shiga ba, domin yana shiga za’a kashe shi, gawarsa ma ba za’a gani ba

To a hakane, idan baki wadanda suka shiga Jos zasu wuce zuwa Abuja basu san hanya ba, idan tsautsayi da karan kwana ya zo sai Musulmi yabi hanyar da ba’a bi, shikenan kwanansa ya kare, abinda ya faru da wadannan ‘yan uwa namu kenan da aka kashe jiya

Kuna zuwa a mota zasu tareku, da zaran sunga alamar Musulunci a fuskarka shikenan zasu kwantar su yanka, akwai lokacin da suna kama matan Musulmai akan hanya su tafi dasu unguwannin su, har abada ba’a sake ganinsu, ance suna zuwa su killace matan Musulmai, suna musu fyade har sai sunyi ciki sun haihu, sai su kashe su rike jariran

Haka sukeyi saboda bakar kiyayyar Musulunci, su wai a gurinsu sun kama matan Muuslmai sun musu fyade sunyi ciki sun haihu, sai su kashe matan su rike yaran, saboda wai suci riba a jikin Musulmai, Musulmai sun haifa musu arna

Bakaken arnan Jos suna da sojojin bogi da ‘yan sandan bogi, suna bi har garuruwan Musulmai su kama Musulmai su tafi dasu Jos, daga nan ba’a sake jin labarin makomar Musulmi, babu wanda ya san abinda sukeyi a wannan unguwanni nasu da Musulmai basa shiga sai Allah, kuma babu irin bindigar da basu dashi

Amma menene amfani tsarin dokar Constitution wanda ya bawa duk wani ‘dan Nigeria ‘yanci yayi tafiya duk inda ya ga dama a cikin Nigeria ba tare da tsangwama ba?
Me yasa shekara da shekaru an kasa daukar mataki akan Arnan Jos da suke tare hanya su kashe Musulmai?

Su arnan suna da ‘yanci su bi cikin layukan Musulmai su wuce kalau babu wanda zai tabasu, amma Musulmai basu da ‘yancin su bi layukan bakaken arna sai an taresu an kashe haka siddan ba tare da sun aikata laifin komai ba, arnan da suke wannan ta’addanci a Jos har naman Musulmai sun gasa sun ci, kuma suka dauki bidiyo suka nunawa duniya

Arnan da suke aikata wannan ta’addanci su sani cewa ba jarunta bane, domin matafiyi baya rike da makami, idan suna son tabbatar da cewa su jarumai ne su bari Musulmai su dauki makami a gwabza su gani ko akwai wani bakin arne da zai kai labari

Idan ya tabbata Gwamnatin Nigeria da Gwamnatin jihar Pilato ba zata iya dakile arnan da suke tare hanya a Jos suna kashe Musulmai ba, to ya kamata Musulmai su dana tarko, su dauki matakin kariya da ramuwar gayya, wannan ba laifi bane har a dokar kasa

Daga karshen wannan rabutun, ina bada shawara, duk wanda ya fito daga jihohin Arewa maso gabas zai je Abuja, kuma zai bi ta cikin Jos, matukar bai san hanya ba, to da zaran yazo farkon cikin garin Jos wajen Masallacin ‘Yan taya, ya tsaya yayi tambaya a nuna masa hanya da zai wuce, hakan zai taimaka sosai saboda kada a fada tarkon bakaken arna

Allah Ka kare Musulunci da Musulmai a duk inda suke Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Wednesday, July 28, 2021

©AJI NA ƊAYA~DARASI NA HUƊU®HANYA TA BIYU DA AKE RUBUTA HARUFFAN LARABCI.

 ©AJI NA ƊAYA~DARASI NA HUƊU®HANYA TA BIYU DA AKE RUBUTA HARUFFAN LARABCI. 


Duk harafin da ya zo a farkon kalma,  ya zamana a gabansa akwai haruffan wannan kalmar, sai ya ginu da haruffan gabansa kamar haka. Kalli yanda ake rubuta wadannan Kalmomi masu zuwa: 


Mustashfa م س ت ش ف ي asibiti

Nurun   ن و ر haske 

Mujtaba م ج ت ب ي Mujtaba

Hujratun ح ج ر ة  Daki

Da'amun ط ع ا م Abinci

Haruffan Wadannan kalmomi a tsi-tsinke suke Amma idan za a rubutasu a ka'ida sai a hade su da juna kamar haka:

Mustashfa  مستشفي. Asibiti. 

Nurun  نور  Haske 

Mujtaba. مجتبي Majtaba 

Hujratun حجرة   Daki 

Da'amun.  طعام  Abinci 


A nan za a ga kamar layi ne aka yi aka ɗora haruffan a kai,  kamar yanda ya gabata a misalan baya. Haka kuma idan muka lura da kyau za mu gano cewa haruffa masu jela Ana yanke jelar ne lokacin da za a haɗa su da harafin gabansu. Harafin karshe ne ba a yanke masa jelarsa kamar haka:


Mu'allimu. م ع ل م Malami  sai ya koma haka معلم


Waɗannan misalai na nuna inda haruffan ke haduwa da junansu.  Duk farkon kalma ta fara da ɗaya daga cikin haruffan larabci 28 da muke magana a kai. Saidai a kula a ga yanda kowanne ke canjawa. Ga kuma karin misalai a hoto dake kasa.


Masu bukatar sauran darusa da suka kuɓuce musu sai su Shiga wannan link suyi liking kuma su following domin samun sauran Darsuka ɗin 👇👇👇👇👇👇👇�

Page-https://www.facebook.com/111306253888584?referrer=whatsapp


Allah ya sa agane, kuma ya bamu ilimi mai Amfani. Ãmīn

AJI NA ƊAYA DARASI NA UKU ®JERIN HARUFFA MASU KAMA DAJUNA DA KUMA YANDA AKE RUBUTA HARUFFAN LARABCI.

©AJI NA ƊAYA DARASI NA UKU

®JERIN HARUFFA MASU KAMA DAJUNA DA KUMA YANDA AKE RUBUTA HARUFFAN LARABCI. 


1.   Haruffa masu kama da juna a rubutawa.

2.   Haruffa masu kama da juna a wajan faɗa


1.  Masu kama da juna a rubutawa su ne:


ب  ت ث.     Ba'un Ta'un.  Sa'un     

ج ح خ.    Jimun Ha'un Kha'un      

د ذ.           Dalun.  Zalun 

ر ز.      Ra'un   Zayun    

س ش.      Sinun.  Shinun

ص ض      Sadun. Dadun      

ط ظ.       Ɗa'un   Za'un    

ع غ.         Ainun. Gainun  

ف ق          Fa'un.   Ƙafun


2   Masu kama da juna a wajan faɗa su ne:

ا   . ع.        Alifun. Ainun 

ث  س  ص.   Sa'un  Sinun Sadun   

د   ض.     Dalun   Dadun

 ذ   ز     ظ.    Zalun.   Zayun. Zadun  


Yanda ake rubuta haruffan larabci. 


Haruffan larabci suna da hanyoyi hudu da ake bi don rubuta su. Ma'ana kowane harafi a cikinsu yana iya cangawa gida hudu kenan kamar haka:


1 Hanya ta farko Rubutasu dai-dai.


Ana rubutasu dai-dai ne batare da sun hadu da juna ba a daya daga cikin dalilai biyu:

a) Lokacin da ake karantasu ko rubutasu dai-dai ba a cikin kalma ba. 

b) lokacin da suka zo a karshen kalma ya zama kuma suna bayan harafi daya daga cikin wadannan haruffa shida ( ا د. ذ. ر. ز. و. ) ، a nan ma sai a rubuta su a tsin-tsinke kamar haka :

ا. ب. ت. ث. ج. ح. خ. د. ذ. ر. ز. س. ش. ص. 

ض. ط. ظ. ع. غ. ف. ق. ك. ل. م. ن. ه. و. ي.


Alhamdu lillah wassalatu wassalamu Ala Rasulillah الحمد لله والصلاة والسلام على رسول الله 


Sa'annan masu bukatar sauran darusa da suka ɓuce musu sai su Shiga wannan link kuyi liking kuma ku following domin samun Darsuka akan hakan 👇👇👇👇👇👇👇�

Page-https://www.facebook.com/111306253888584?referrer=whatsapp

Tuesday, July 27, 2021

AJI NA ƊAYA DARASI NA BIYU

©AJI NA ƊAYA~DARASI NA BIYU


® BANBANCI TSAKANIN HARUFFAN BOKO DA NA LARABCI. 


Haruffan larabci sun banbabta da na boko ta waje uku 

1). Ana rubuta Haruffan boko ne daga hagu zuwa dama. Amma na Larabci ana rubutasu ne daga dama zuwa hagu. Kamar haka:

ا ب ت ث ج ح خ د ذ ر ز س ش ص ض ط ظ ع غ ف ق ك 


Amma ba kamar haka:

ك ق ف غ ع ظ ط ض ص ش س ز ر ذ د خ ح ج ث ت ب ا


2). Haruffan boko ana rubuta su dai- dai ne, na Larabci kuwa wani lokacin su so dai- dai, wani lokacin su zo a hade da juna kamar haka : 


INDA SUKE DAI-DAI 


Zara'a. زرع. ya yi shuka. 

Darasa. درس ya karanta 

Adamu. آدم Adamu

Wazana. وزن. Ya auna

Aurar.          زَوِّجْ.       Ya aurar.              زَوَّجَ


INDA SUKE A HADE DA JUNA 


Ku 2 za ku fita.                      سوف تخرجان 

Uhibbu kira'atul Arabiyya أحب قراءة العربية Ina son karanta Larabc.

Fahimtu darsi فهمت درسي. Na fahimci darasina. 

Akalal waldu mauzan أكل الولد موزا Yaron ya ci ayaba. 


3) Haka kuma ana sa wasullan haruffan boko a gaban kowane harafi. Amma wasullan haruffan larabci na zuwa ne a samansu ko a karkashinsu. Kamar yanda zai zo nan gaba. 

Allah ya sa an gane. Amin


Kara kumanta wannan Ajin na ɗaya, ga mai son ya iya karantawa, ko rubutawa, gami da sanin ma'anar duk abin da yake Karantawa na Larabci' Sa'annan kuma Akwai group WhatsApp na MATA DA MAZA Kamar haka:

👇👇👇👇👇👇👇

GROUP WHATSAPP NA MATA ZALLA sai kiyi sallama ta wannan number  09012664164 / 08138550767 amma ta voice message sai kice (Assalamu alaikum, inaso asakani a group WhatsApp na mata zalla aji na.......sai ki kira ajin da kike so) bayan wannan bama bukatar jin wani magana daga gareki.


AMMA GA MAZA wayanda suke son shiga kuma wadda muka buɗe ya cika ga sabuwar, sai dai dan Allah idan kasan kana wancan kar ka shiga wannan damin abinda zamu ɗaura a wancan shi zamu sa a wannan

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/JnSH7suWglND8AKY1u2VwA

Thursday, June 3, 2021

®AJI NA ƊAY ~DARASI NA ƊAYA 01, A~HARUFFAN LARABCI

Larabci kamar kowani yare ne ya ginu a kan Harafai, Harafai da suka gina larabci su ne ake kira da Huruful-Hija'iyyah wasu kuma sukan ce musu Huruful-abjadiyyah, matukar idan kana so ka iya karatun Larabci toh dole ne sai ka san Huruful-Hija'iyyah


Huruful-Hija'iyyah harafaine guda 28, Awani gaulin kuma idan kun duba zaku ga guda 30, kari shi ne, Lam Ali (لا ) da Hamza (ء) Lam Alif da Hamza (لا ء) basa ciki, kari ne a kai, sanin wadannan Harafai (Huruful-Hija'iyyah) da gāne su da Bab-ban ce su da iya rubuta su zai taimaka gurin iya karatu da rubutun Larabci


Huruful-Hija'iyyah kamar yadda kuke gani a kwai Harafai masu Kamada juna bab-ban ci shine gurin digo, Yi kokari ka haddace su kuma ka iya rubuta su , gāsu kamar haka:-

 الدرس الأول الحروف :

ا alifun ب ba'un ت ta'un ث sa'un ج jimun ح ha'un خ kha'un د dalun ذ. zalun ر Ra'un ز zayun س sinun ش shinun ص sadun ض dadun ط da'un. ظ za'un ع ainun. غ gainun ف fa'un ق kafun ك kafun. ل lamun م. Mimun ن nunun ه ha'un و wawun ي ya'un 



Mun ɗaura Video din yadda ake karantawa a YOUTUBE-CHANEL NAMU SAI KUYI SUBSCRIBE TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇

https://www.youtube.com/channel/UCmC9fMpvNGwheErpsSvVZyA

Saturday, April 10, 2021

YANCIN KAI A NIGERIA CI GABA KO CI BAYA?

 

SHEKARU 61 DA SAMUN ‘

Tura Wannan Zuwa
sharethis sharing button
Sir James Willson Robertson, shi ne Gwamna janar na ƙarshe a tarihin mulkin mallaka a Najeriya. Ya soma mulki ne a ranar 15 ga watan Yuni na shekarar 1955, sannan ya miqa mulki a hannun Dr. Nnamdi Azikwe, wanda yake shi ne baƙar fata na farko ɗan Najeriya daya fara mulkin ƙasar, a ranar 16 ga watan Nuwamba na shekarar 1960.

Makomar Nijeriya Bayan Samun 'Yancin Kai

MarubuciMohammed Bala Garba,Maiduguri.

Sir Robertson, bayan komawar sa gida, ya shiga damuwa da takaici bisa yadda ‘yan Afirka suka rushe duk wani asasin gina ƙasa da Turawa suka kafa musu a iya zaman su a ƙasashen Afirka, suka shiga yake-yake da juna tare da neman yancin kai a tsakanin su. Ya faɗi hakan karara a littafin sa mai suna ‘Africa in Transition. From direct rule to Independence, wanda aka buga a shekarar 1974. Ya kuma faɗi cewar ‘yan Afirka sun yi kuskuren neman ‘yanci tun da farko, domin abin da suka sani yanzu (na yake-yake da almundahna) basu san shi ba a baya, shi yasa tun a lokacin suka rinka matsa lambar korar Turawa tare da karbar yancin kai, wannan yasa muka yanke shawarar basu abin da suke so.

Kafin samun ‘yancin kai, an shafe shekara da shekaru ‘yan kishin ƙasa suna gwagwarmayar kwato wa ƙasar nan 'yancin daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, a ƙarshe haƙarsu ta cimma ruwa, inda a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, Sir Abubakar Tafawa Balewa wanda ya zamo Firaministan Najeriya na farko ya karɓi tutar 'yancin kai daga hannun Gwamna Janar Sir James Willson Robertson, inda aka ɗaga tutar da Micheal Taiwo Akinkunmi ya zana mai launin Kore da Fari da Kore, yayin da aka sauke tutar Ingila.

Najeriya ƙasa ce mai al'adu da addinai da ma ƙabilu daban-daban da suka haura 200. Manya a cikinsu, su ne, Hausa da Ibo da kuma Yoruba, sannan kowannensu na da tsarin yadda yake tafiyar da mulkin jama'arsa.

Bayan da aka raba ƙasar zuwa yankuna uku, wato Hausa da Fulani a yankin Arewa, Ibo a yankin gabashi, Yarabawa kuma a yankin yamma, Arewa ta fi kowanne yankin yawa da kuma girma, abinda sauran yankunan suka yi ta kokawa a kai.

A shekarun 1940 zuwa 1950, jam'iyyun da aka kafa domin yakin kwatarwa Najeriya 'yancin kai su ne, NPC (Northern People’s Congress) a Arewa, NCNC (Nigerian National Democratic Party) ta ƙabilar Ibo, da AG (Action Group) ta Yarabawa, sun yi ta gwagwarmaya musamman ma dai NCNC da AG waɗanda ke neman a basu yancin cin gashin kai, abinda suka ga zai yi wuya ba tare da haɗa kai da Arewa ba.

Hakan ne yasa jam'iyyun uku suka yi ta gwagwarmayar tare.

A ranar da za a baiwa Najeriya ‘yancin kai, wato ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, turawan mulkin mallaka na Ingila sun miƙa tutar ‘yancin kai ga firaiminista Sir. Abubakar Tafawa Balewa wanda ɗan Arewa ne kuma musulmi, yayin da Dr. Nnamdi Azikiwe wanda Kirista ne ɗan kabilar Ibo ke matsayin shugaban ƙasa.

Tun daga wannan lokacin sauran ƙabilun musamman Ibo basu ji daɗin lamarin ba na cewa 'yan Arewa ne ke mulkarsu, wanda wannan ne ya haifar da juyin mulki na farko da sojojin yawancinsu 'yan ƙabilar Ibo suka yi a shekarar 1966, karkashin jagorancin Laftanal Chukwuma Nzeogwu Kaduna, inda aka kashe manyan shugabannin Arewa.

Waɗannan ƙananan hafsoshin sojan, sun yi ikirarin cewa sun shirya juyin mulkin ne a saboda a cewarsu, shugabannin dake jagorancin ƙasar sun nuna zarmiya, inda suka ce ministocin gwamnati suna sace kuɗaɗen baitul-mali domin amfaninsu.

Sai dai kuma a wani ɓangare, akwai masu ikirarin cewa wannan juyin mulki na ƙabilanci ne, saboda daga cikin sojoji 8 da suka kulla wannan juyin mulkin, 7 'yan ƙabilar Igbo ne, ɗaya ne kawai Bayarbe. A wani gefen kuwa, dukkan manyan shugabannin farar hular da aka kashe, harma da manyan hafsoshin soja, kusan duk 'yan Arewacin Najeriya ne.

Waɗanda aka kashe a juyin mulkin sun haɗa da Sir. Abubakar Tafawa Balewa Firimiyan Arewa da Sir. Ahmadu Bello Firimiyan Yamma da Samuel Akintola Ministan kuɗi da Festus Okotie-Eboh (Shi kaɗai ne ɗan yankin gabas a cikin gwamnatin tarayya da aka kashe) da Ahmed Ben Musa da Birgediya Zakariya Maimalari da Birgediya Samuel Ademulegun da Kanar Kur Mohammed da Kanar Shodeinde da Laftanal-kanar Abogo largema da Laftanal-kanar James Pam da leftana-kanar Arthur Unegbe. Shi ma Saje Daramola Oyegoke, ya taimakawa Nzeogwu wajen kai hari a kan gidan Sardauna, amma a cewar 'yan sanda, daga baya Nzeogwu ya kashe shi.

A ranar 28 ga watan Yulin 1966, watanni shida bayan wannan juyin mulki, hafsoshin soja daga Arewacin Najeriya suka shirya nasu juyin mulkin, wanda ya kai ga kashe Janar Aguiyi-Ironsi tare da laftanal-kanar Adekunle Fajuyi.

Waɗanda suka shirya wannan juyin mulki su ne, Laftanal-kanar Murtala Mohammed da laftanal-kanar Joseph Akahan da Manjo T.Y. Danjuma da dai sauran ƙananan hafsoshin sojan Arewacin Najeriya, cikinsu har da Laftanal Ibrahim Badamasi Babangida da Laftanal Muhammadu Buhari. Daga nan ne Najeriya tahau turbar rikice rikicen addini da na ƙabilanci har ma da na siyasa.

Rikicin Maitatsine shi ne rikicin addini na farko mafi muni da Najeriya ta fuskanta a jamhuriya ta biyu ƙarƙashin mulkin marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Tun daga wancan lokacin da aka yi rikicin Maitatsine, an yi ta samun rikice rikicen addini da na ƙabilanci daban-daban, kamar daga Arewacin zuwa Kudanci zuwa Gabashin ƙasar.

A farkon shekarar 1980 ne aka yi rikicin Maitatsine a jihar Kano, wanda daga bisani ya bazu zuwa Yola da Maiduguri da Bauchi da Gombe, inda aka yi asarar rayukan dubban dubatan mutane da suka haɗa da Musulmai da Kirista. Bayan wannan, rikice-rikicen da suka fi muni sun haɗa da rikicin Zangon Kataf na jihar Kaduna a shekarar 1992 tsakanin Hausawa da Katafawa, wanda daga bisani ya rikiɗe ya koma na addini.

A wannan rikicin shi ma an yi asarar rayuka da dukiyoyi masu ɗimbin yawa. Sai kuma rikicin Shagamu na jihar Ogun, wanda ya auku a watan Yulin shekarar 1999 tsakanin Yarabawa da Hausawa, biyo bayan kisan wata mata Bahaushiya da wata ƙungiya mai suna (Oro) ta yi, inda suka ce ta keta ƙa’idarsu. Kashe-kashen da aka yi wa Hausawa a Shagamu ya sa a Kano ma matasa sun ɗauki fansa kan Yarabawan dake zaune a can.

Ɗalibai suna farin ciki da zagayowar ranar samun 'yancin Kai

Sai kuma a watan Nuwamban shekarar 1999, inda wani rikicin ƙabilanci ya sake ɓarkewa a unguwar Ajegunle ta jihar Legas tsakanin ƙungiyar OPC (Oodua People’s Congress) da ta matasan ƙabilar Ijaw.

Bayan kwantar da wannan rikicin a watan Disambar wannan shekarar, an sake samun wani ɓarkewar rikicin ƙabilancin a kasuwar Mile 12, tsakanin kungiyar OPC da Hausawa, bisa dalilan shugabancin ƙungiyar masu sayar da doya a kasuwar, wato Shukura Yam Sellers Association, wanda kusan Hausawa ne ke riƙe da shugabancinta, inda aka yi asarar rayuka sama da ɗari biyu tare da ƙone kasuwar kurmus.

Ɓullo da tsarin shari’ar Musulunci a wasu jahohin Arewacin ƙasar shi ne ya yi sanadiyar rikicin addini a jihar Kaduna cikin watan Fabrairun 2000, inda nan ma aka yi rikici tsakanin Musulmai da mabiya addinin Kirista, waɗanda suka nuna rashin amincewarsu ga amfani da shari’ar Musulunci a jihar. Rikicin wanda ya bazu zuwa garuruwan Kachiya da Zariya da sauransu, shi ma ya haddasa asarar daruruwan rayuka da dukiyoyi masu ɗimbin yawa.

Bayan wannan rikicin na Kaduna, an samu makamancinsa a jahohin Sokoto da Barno musamman ma a garin Damboa na jihar Barno.

An fara samun rikici a Jos tun daga shekara ta 2001, wanda asalin sa na siyasa ne tsakanin ‘yan asalin yankin Pilato da kuma Hausa/Fulani dake zaune a can, kafin daga bisani ya rikiɗe ya koma na addini da ƙabilanci, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan rikice-rikicen da aka samu a Najeriya. Rikincin Jos na faruwa ne tsakanin Hausa/Fulani Musulmai da kuma ‘yan yankin na Pilato waɗanda akasarinsu mabiya addinin Kirista ne. Bangarorin biyu sunyi taƙaddama ne kan ko suwaye ‘yan asalin jihar da kuma waɗanda za su yi shugabanci. Kan haka ne wasu ke ganin bayan ga ƙabilanci na addini, rikicin Jos na da alaƙa da siyasa. An samu asarar rayuka da ma dukiyoyi masu ɗimbin yawa tun daga lokacin da aka fara zaman doya da manja a garin, wato daga shekara ta 2001 zuwa 2010. Rikice-rikicen da aka yi ta yi a Jos a shekarun baya kan bazu zuwa jahohin dake makwabtaka da ita kamar Gombe da Bauchi.

Ana cikin wannan yanayi muka tsinci kanmu a halin da muke ciki ayau, wato rikicin Boko Haram, wanda ya auku a watan Yulin shekara ta 2009, inda waɗansu matasa ƙarƙashin jagorancin Muhammad Yusuf dake adawa da ilimin Boko da aikin gwamnati suka ƙaddamar da yaƙi kan jami’an tsaro da ofisoshinsu a birnin Maiduguri a jihar Barno.

Irin kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankulan da tun farko ake ganinsu a yankin Arewa maso gabas, daga baya ya bazu zuwa sassan Najeriya da wajenta. Yau kimanin shekaru goma kenan muna fama da tashe-tashen hankulan da zub da jini a dalilin ƙungiyar Boko Haram, sai ga wata fitinar ma ta sake ɓarkewa tsakanin Makiyaya (masu kiwo) da Manoma, inda aka zub da jini tare da rasa rayuka masu yawa.

Bayan lafawar wannan, sai ga jihohin Zamfara da Katsina da Taraba da Kaduna sun rikice, inda kullum cikin kashe-kashe da zub da jinin al’umma ake. Garkuwa da mutune kuwa ya zamo ruwan dare a waɗannan jahohin, kai kace babu gwamnati a ƙasar.

Abubuwan dake faruwa tsakanin mabiya mazhaban Shi’a da gwamnatin Najeriya na sake barazana ga zaman lafiyar ƙasar, musamman ma ga Arewancin ƙasar.

Abin da mafi yawan mutane basu sani ba wasu kuma suka mance, shi ne, Mohammed Yusuf (shugaban ƙungiyar Boko Haram) wasu ‘yan tsirarin matasa ya mallaka, inda suka ƙaddamar da yaƙi kan jami’an tsaro da ofisoshinsu a cikin birnin Maiduguri, daga nan kuma kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankula suka zamo ruwan dare a yankin Arewa.

A yayin da wannan tashe-tashen hankali ke bazuwa zuwa wasu sassan na Najeriya har ma da makwabtanta.

MAKALOLI MASU ALAKA:

SHIN DA GASKE NE NIGERIA TA KUBUTA DAGA MULKIN MALLAKA?

Kalli Kayatattun Hotunan Tunawa da Ranar Samun 'Yancin Kan Nigeria a Shekaru 59 daga Turawan Mulkin Mallaka

KARANTA TARIHIN YADDA TURAWA SUKA AZABTAR DA AL'UMMAR YANKIN AREWACIN NIGERIA

Yau kimanin shekaru goma ke nan amma gwamnatin Najeriya ta kasa murƙushe Boko Haram, to yaya kuma ƙungiyar Shi’a wacce take da mabiya a dukkan ƙananan hukumomin ƙasar?

Duk mu ajiye wannan gefe guda, a tsawon wannan shekaru 59 da samun ‘yancin kai, shin ta ɓangaren ci gaban ƙasa da tattalin arziki, ci gaba muka samu ko ci baya?

Tuesday, April 6, 2021

YADDA ALLAH (SWT) YA TSARA ALJANNAH FIRDAUSI DA NI'IMOMI MASU TARIN YAWA

 YADDA ALLAH (SWT) YA TSARA ALJANNAH FIRDAUSI DA NI'IMOMI MASU TARIN YAWA


https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

 

An gina Aljannah ne da tubali (blocks) na Zinare da Azurfa

tatacciya. Simintin cikinta anyi shine da Almiski mai mutukar

Qamshi.


An cike tsakanin tubalanta da kayan ado ba Zubarjadi da

Yaaqootu.


An halicci Qasar cikinta ne daga Za'afaran.



Tana da Qofofi guda takwas kamar haka:


1. Jannatul Ma'awa.

2. Daarul Maqaam.

3. Daarus Salaam.

4. Daarul Khuld.

5. Jannatul 'Adni.

6. Jannatun Na'eem.

7. Jannatul Khaseef.

8. Jannatul Firdaus.


•JANNATUL MA'AWA ita ce daga Qasa,


•JANNATUL ADNI kuma ita ce matsakaiciya


•JANNATUL FIRDAUSI kuma ita ce Qololuwa.


Acikin Aljannah akwai Gonaki da lambuna wanda tsawon

kowacce gona da fadinta ya kai tsawon tafiyar shekara 100

ko fiye da haka.


Akwai bishiyoyi masu inuwa masu Ni'ima da tsirrai marassa

Qaya.


An Halicci bishiyoyim cikinta ne daga madaukakin Zinare da

tatacciyar Azurfa.


Suna da manyan ganye kamar girman kunnen giwa, kuma

'ya'yan itacen bassu Qarewa. Suna nan nau'i-nau'i.


Wadanda suke Qaunar juna domin Allah zasu samu shiga

Aljannah kuma acikinta za'a basu wasu Al'amudai na Yaqootu.


Akan Al'amudan akwai Dakuna (rooms) guda dubu saba'in

(70,000) masu haske.


Kuma hasken Wadannan dakunan ne zai haske 'Yan Aljannah

kamar yadda hasken rana yake haske mutanen duniya.


Akwai dakunan cin abinci yalwatattu ta yadda acikin dakin

cin abinci guda za'a samu shimfidu (dining sheet) guda dubu

saba'in (70,00).


Akwai Qananan yara masu hidima, suna zagayawa ko ina cikin

gidan Aljannah. Sunci ado da kaya iri-iri. Kuma Su kansu

suna haske kamar Lu'u.


Bishiyoyin dabinai da inabi wadanda 'ya'yansu ko yaushe

nunannu suke. Kuma suna daf da Qasa. Girman kowanne

nonon dabono yakai kamar Zira'i 12. Kuma kowanne kwayan

dabino guda ya kai girman Tulu, Kuma fari ne tas kamar

madara, Kuma babu Kwallo acikinsa. Zakinsa kuma wane

Zuma!!


Kuma girman kowanne Inabi guda daya yakai girman tulu.


Sai wani Sahabi yace "Ya Rasulallahi guda daya zai isheni

dani da iyalaina?"


Sai ANNABI (S.A.W) yace masa "AI GUDA DAYA ZAI ISHEKA

DAKAI DA KABILARKA MA BAKI DAYA"


TUFAFIN 'YAN ALJANNAH:


Kowanne Dan Aljannah za'a sanya masa riguna guda 70 na

haske. Masu taushi, masu kyalli, Kuma marassa nauyi ko

kadan.


Wadannan rigunan kowacce kalarta daban, nau'inta daban.

Kuma ba irin tufafin duniya bane, domin kuwa babu wacce

take rufe 'yar uwarta.


Saboda tsananin haskensu da kyawunsu, ana iya ganin Siffar

jikin mutum har Zuciyarsa da irin Qarfin soyayyar da take

dauke dashi.


Wadannan Tufafin bassu tsufa ko datti, kuma bassu yagewa.


QORAMUN ALJANNAH


Acikin Aljannah akwai Qoramu (Kogi) guda bakwai:


1. Kogin ruwa.

2. Kogin Madara.

3. Kogin ruwan Zuma .

4. Kogin ruwan giya (Sharabun Tahoorun).

5. Kogin Kafoor.

6. Kogin Zanjabeel.

7. Kogin Tasneem.


Ya Allah muna tawassuli da fiyayyen bayinka wato ANNABI

(S.A.W) domin alfarmarsa ka gafarta mana kasa muna cikin

'Yan Sahun gaba wajen shiga Aljannah Albarkan ANNABI

S.A.W Amin.


Tuesday, March 2, 2021

SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI ********************************* Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro.

 


SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI

*********************************
Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro.

SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI
******************************
***
Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro.
 1. Yana da kyau Macce me ciki ta siffantu da halaye na kwarai tare kuma da gujewa munanen halaye.
2. Saurarar karatun Alqur'ani na mintuna 30 kullum ga macce mai ciki kan taimaka wajen samun natsatstsen yaro.
3. Kauracewa duk wani magani da ba likita ne ya bada umurnin a sha ba, kan taimaka wajen samun lafiyayen jariri.
4. Macce mai ciki ta guji rashin yin bacci da wuri, samun bacci na awa 8 kan taimaka wa kwakwalwar jaririn da za'a haifa.
5. Macce mai ciki ta guji aikin wahala ko kuma wani abu wanda yayi kama da shi domin samun lafiyar jikinta da ta jariri.




6. Mai ciki ta rika kula da abinci kafin taci, ta tabbatar baku tsakuwa ko datti a cikin abinda zata sha.
7. Yawaita cin kayan lambu irinsu, Zogale, Cucumber, kankana, lettuce, alayyahu da sauransu.
8. A karshe yana da kyau mai ciki ta rika cin dabino hudu a rana biyu da safe biyu da dare koma fiye da su.
Allah ya baku ikon saukewa, masu nema Allah ya basu, wayanda ke da Allah ya basu abin ciyarwa da ikon tarbiyantarwa.

SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI *********************************

 

SHAWARORI TAKWAS GA MASU CIKI

SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI
******************************
***
Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro.
 1. Yana da kyau Macce me ciki ta siffantu da halaye na kwarai tare kuma da gujewa munanen halaye.
2. Saurarar karatun Alqur'ani na mintuna 30 kullum ga macce mai ciki kan taimaka wajen samun natsatstsen yaro.
3. Kauracewa duk wani magani da ba likita ne ya bada umurnin a sha ba, kan taimaka wajen samun lafiyayen jariri.




4. Macce mai ciki ta guji rashin yin bacci da wuri, samun bacci na awa 8 kan taimaka wa kwakwalwar jaririn da za'a haifa.
5. Macce mai ciki ta guji aikin wahala ko kuma wani abu wanda yayi kama da shi domin samun lafiyar jikinta da ta jariri.
6. Mai ciki ta rika kula da abinci kafin taci, ta tabbatar baku tsakuwa ko datti a cikin abinda zata sha.
7. Yawaita cin kayan lambu irinsu, Zogale, Cucumber, kankana, lettuce, alayyahu da sauransu.
8. A karshe yana da kyau mai ciki ta rika cin dabino hudu a rana biyu da safe biyu da dare koma fiye da su.
Allah ya baku ikon saukewa, masu nema Allah ya basu, wayanda ke da Allah ya basu abin ciyarwa da ikon tarbiyantarwa.

YA KAMATA MUSAN WANNAN KAFIN AURE SABODA LAFIYAR IYALI DA KWANCIYAR HANKALIN MU

 YA KAMATA MUSAN WANNAN KAFIN AURE SABODA LAFIYAR IYALI DA KWANCIYAR HANKALIN MU


Akwai cutuka da ya kamata a yi gwajin jini akansu a tsarin Musulunci bisa koyarwar Manzon Allah (S.A.Ws), kamar yadda yace "Babu cuta babu cutarwa a komai"

Mu sani idan har bincike a tsakanin ma'aurata ya halatta, to a yi bincike akan lafiyar ma'aurata shi ne ya fi cancanta domin sai da lafiya ne zaman auren zai inganta.


Jikin kowane 'dan adam yana dauke da wani abu da ake kira Genotype a turance. To wannan Genotype din idan har ya kasance na miji da mace su zo ɗaya to kuwa 'ya'yansu duka zasu kasance ba masu cikakkiyar lafiya ba.


Akwai → AA wannan shine lafiyayye

Akwai → AS wannan  shine ke da rabin cutar (ma'ana bai munana ba).

Akwai → SS To wannan shine mai cikakkiyar cutar ta amosanin jini.


A lokacin duk lokacin da akayi aure tsakanin mai SS da SS to duka ’ya’yansu su gaji wannan nakasu (ma'ana zasu kasance masu dauke da ɗaya daga cikin cutar Gado kamar Sikila, kansar Jini, Hauka ko Gaula, cutar kuturta, da cutar Haka-Haka ). Su dukansu da ’ya’yan nasu kuma kullum sukan kasance a cikin rashin lafiya, kenan rabin zaman auren za'a iya yinsa a jinyace.


A lokacin da mai ciwon (SS) ya auri mai rabin ciwon (AS), zai iya kasancewa wasu a cikin ’ya’yansu su gaji wannan ciwo.


Amma idan mai rabin ciwon (AS) ya auri wata mai rabin ciwon (AS), to rabin ’ya’yansu ne za su iya kasancewa masu amosanin jini, sauran kuma

lafiyayyu.


Duk lokacin da mai AA ya auri mai SS Ko AS to za'a iya samun sauqi kwarai da gaske.

Amma Idan Mai (AA) ya auri mai (AA) to fa shikenan babu zance haduwa da 'ya'ya masu dauke da cutar ta Amosanin jini (Gado).


Wannan cutar Gado ( kamar Sikila, kansar Jini, Hauka ko Gaula, cutar kuturta, da cutar Haka-Haka ) suna rayuwa ne a cikin jinin mutum bil adama, cutar ana haihuwar mutum da ita ne, ma'ana cutace da ke zaune a cikin jinin jikin dan Adam.

Saboda cuta ce da ke kama jajayen kwayoyin halittu na jini. Wannan ciwo ba kwayoyin cuta ke kawo shi ba, gadonsa ake yi daga wajen iyaye, waɗan da ke da wannan nakasar a kwayoyin jini.

Wasu mutanen, nakasar tasu rabi ce, waɗanda ake wa lakabi da AS; wasu kuma duk kwayoyin a nakashe suke, waɗanda su ne a ke kira da SS.


Misali kamar cutar Sikila na daga cikin jerin ciwukan da sai dole an gada daga wurin mahaifiya da mahaifi sa’annan yake nunawa.


Insha Allahu rubutu nagaba zanyi akan YADDA AKE GANE CUTAR GADO (kamar Sikila, kansar Jini, Hauka ko Gaula, cutar kuturta, da cutar Haka-Haka )


Muna rokon ALLAH ya bamu lafiya da zama lafiya da abinda lafiya zata ci. Āmin

✍️

Ahmad Musa

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Tuesday, February 23, 2021

TAMBAYOYIN BIYAR DA KOWANNE MUSULMI YA KAMATA YA SAN AMSAR SU.

 TAMBAYOYIN BIYAR DA KOWANNE MUSULMI YA KAMATA YA SAN AMSAR SU.


1. WANENE YA HALICCE NI?

Wanda ko  Wanne Musulmi Ya san Wannan Tambayar Sai dai Na kawota dan Itace ta zama Wajibi ta fara shigowa a Jeren Wayannan Tambayoyin, To tunda kowanne Musulmi Ya san Wanda Ya halicce shi Sai tambaya ta Biyu.


2. DON ME YA HALICCE NI?

Allah (swt) da kansa Ya Bamu Amsar wannan Tambaya Sai dai Wasummu basa ma lura da Amsar ballantana Suyi abinda Allah (swt) Yace.



Allah (swt) Yana Cewa "BAN HALICCI MUTUM DA ALJANI BA SAI DON SU BAUTA MIN".


3. TO YAYA NE AKEYIN BAUTAR?

Kowannen Mu ya kamata Yasan Cewa Bauta dole bata Yuwa Sai da Ilmi kuma Dole ne Sai Da Yin tambaya akan abinda Ya shafi Ilmi Shi kan shi.


Sharuddan Yin Bauta

- Ka samu a cikin Al'qur'ani Ance Ayi.

- Ka dauko Yanda Magabata na Kwarai Suka yi bautar, Ma'ana Yanda Suka Dauko Yanda Manzon Allah (saww) Yake yin bautar.

- kayi Badan Wani ko wata Ya Yaba maka ba.


4. A INA NAKE YANZU?

Ma'ana A ina nake Yanzu? Shin Ina nan In da Allah ke son Ya Ganni? Ko kuma Na saki Hanya?


5. ZUWA INA MAKOMA TA ZATA KASANCE?

Bayan Duk Wayannan Tambayoyin Guda Hudu to tambaya ta Biyar Duka ta fisu Tsoro da Rudani, Amsar tambayar Makomata Wutane ko kuma Aljanna.


Lalle Wayannan Tambayoyin Abin Dubawa Ne Ga Kowanne Musulmi Mai Hankali.


Wallahi Wa sun Mu da Yawa Sun Yarda Da Allah ne Ya Halicce Su Amma basu san Yarda Shi Yake da Ikon Yi musu Komai ba, Basa Neman Taimakonsa Sai Na Bokaye da 'Yan bori.


Wallahi Da Yawan Wasummu Basu Ma Iya Karanta Fatiha Dai dai ba, Amma Idan Zaka Lissafa Wakokin Kafirrai Zakaji Ya Fi hardace Su Fiye da Surorin Al'Qur'ani koma Sunayen Allah.


Wallahi Wasummu Basa Tuna Mutuwa Ko kadan, Kullum Tunanin Su Ya Za'ayi na Samu Kuddi, ko wani abu makamancin haka, Amma basa Tunanin Shin Ana Amsar Ibada ta, Shin Zan Iya Mutuwa Yau, Shin Meye Zunubbai na A gurin Allah (swt).


Wallahi Da Yawa Daga Cikin Mu Har Sun Manta Da Suyi Istigfari Sai Dai Kullum Suna kan Whatsapp, Facebook, Twettr, Istagram, da Sauransu.


Wallahi Mu komawa Allah (swt) ko zamu Samu Rabauta.


Ya Kamata Kana Gama Karatun Wannan Post Din Ka Tashi Kayi Istigfari, Kace " ASTAGFIRULLAHI" ko sau 100, Kada Ka bari Har Ajuma Dan Zaka Iya Mutuwa Yanzu.


ALLAH YA SAMU DACE DUNIYA DA LAHIRA, KUMA ALLAH YA TSARE JIKKUNAN MU DA WUTAR JAHANNAMA.


ahmadmusainc.blogspot.com

Sunday, February 7, 2021

TARIHIN KAFUWAR JERUSALEM

 Jerusalem Ko Birnin Kudus,Ya Kafu Shekaru 3000 Kafin Haihuwar Annabi Isa ( AS ) Amma Inji Malaman Tarihi, Ya Taba Zama Birnin Annabi Daood, Shekaru 1000 Kafin Haihuwar Annabi Isa ( AS ) Shima Inji Malaman Tarihi. 



Birnin Yana Da Yawan Mutane ( 936,425 ) A Lissafin Shekarar 2019, Garin An Sha Kai Masa Hare-Hare Domin Kwace Shi A Tarihi Har Sau 52,

SARKIN KASAR MASAR

 Giza ( the Great Pyramid ) Duk Wannan Tarin Kabarin Sarkin Masar ( Egypt ) Ne ( King Khufu’s ). 



Wanda Yayi Mulki Shekaru 2600 Kafin Haihuwar Annabi Isa ( Amma) Inji Malaman Tarihi 



Giza Wani Yanki Ne Kudu Maso Yamma Na ALKAHIRA Ta Zamanin, Wanda Yayi Aiki A Matsayin Necropolis Don Masarautar Tsohon Masarautar Misira. Mafi Shahara Ga Pyramids Na Khufu (An Kammala Shi A Cikin Shekarar 2560 Kafin 



HaihuwarbAnnabi Isa) Gizah ko Jizah ; Da Larabci : الجيزة Al-Jizah, Furucin larabci Na Masar:  [el ˈgiːze] ) Shine Gari Na Biyu Mafi Girma A Misira,

JERIN SUNAYEN SARAKUNAN KANO

 JERIN SUNAYEN SARAKUNAN KANO 

GIDAN BAGAUDA 

Bagauda (ruled 999-1063)

Warisi dan Bagauda (ruled 1063-1095)

Gijimasu dan Warisi (ruled 1095-1134)

Nawata & Gawata (ruled 1134-1136)

Yusa (ruled 1136-1194)

Naguji (ruled 1194-1247)

Guguwa (ruled 1247-1290)

Shekarau (ruled 1290-1307)

Tsamiya (ruled 1307-1343)

Usman Zamnagawa (ruled 1343-1349)

Yaji I dan Tsamiya (ruled 1349-1385)

 

BAYAN ZUWAN MUSULUNCI 


Yaji I (ruled 1349-1385)

Bugaya (ruled 1385-1390)

Kanajeji (ruled 1390-1410)

Umaru (ruled 1410-1421)

Daud (ruled 1421-1438)

Abdullahi Burja (ruled 1438-1452)

Dakauta (ruled 1452)

Atuma (ruled 1452)

Yakubu Na 2  (1452-1463)

Muhammadu Rumfa (ruled 1463-1499)

Abdullahi dan Rumfa (ruled 1499-1509)

Muhammad Kisoki (ruled 1509-1565)

Yakubu (ruled 1565)

Abu-Bakr Kado (ruled 1565-1573)

Muhammad Shashere (ruled 1573-1582)

Muhammad Zaki (ruled 1582-1618)

Muhammad Nazaki (ruled 1618-1623)


GIDAN KUTUNBI 

El Kutumbi (ruled 1623-1648)

al-Hajj (ruled 1648-1649)

Shekarau (emir) (ruled 1649-1651)

Muhammad Kukuna (ruled 1651-1652)

Soyaki (ruled 1652 he ruled Kano in those days)

Muhammad Kukuna (restored) (ruled 1652-1660)

Bawa (ruled 1660-1670)

Dadi (ruled 1670-1703)

Muhammad Sharefa (ruled 1703-1731)

Kumbari (ruled 1731-1743)

Alhaji Kabe (ruled 1743-1753)

Yaji II (ruled 1753-1768)

Baba Zaki (ruled 1768-1776)

Daud Abasama II (ruled 1776-1781)

Muhammad Alwali II (ruled 1781-1805)


BAYAN JIHADI 


Suleimanu dan AbaHama(emir) (ruled 1805-1819)

Ibrahim Dabo dan Mahmudu (ruled 1819-1846)

Usman I Maje Ringim dan Dabo (ruled 1846-1855)

Abdullahi Maje Karofi dan Dabo (ruled 1855-1883)

Muhammadu Bello dan Dabo (ruled 1883-1893)

Muhammadu Tukur dan Bello (ruled 1893-1894)

Aliyu Babba dan Maje Karofi (ruled 1894-1903)



BAYAN ZUWAN TURAWA 


Muhammad Abbass Dan Maje Karofi (ruled 1903-1919)

Usman II dan Maje Karofi (ruled 1919-1926)

Abdullahi Bayero (ruled 1926-1953)

Muhammadu Sanusi I Dan Bayero (ruled 1954-1963)

Muhammad Inuwa Dan Abbas (ruled 1963 - he served for 3 months only)

Ado Bayero Dan Abdu Bayero (ruled 1963-2014)

Muhammadu Sanusi II (2014-2020)

Aminu Ado Bayero Na Yanzu


INA BUKATAR TAIMAKO A WAJEN GYARA