©AJI NA ƊAYA~DARASI NA HUƊU®HANYA TA BIYU DA AKE RUBUTA HARUFFAN LARABCI.
Duk harafin da ya zo a farkon kalma, ya zamana a gabansa akwai haruffan wannan kalmar, sai ya ginu da haruffan gabansa kamar haka. Kalli yanda ake rubuta wadannan Kalmomi masu zuwa:
Mustashfa م س ت ش ف ي asibiti
Nurun ن و ر haske
Mujtaba م ج ت ب ي Mujtaba
Hujratun ح ج ر ة Daki
Da'amun ط ع ا م Abinci
Haruffan Wadannan kalmomi a tsi-tsinke suke Amma idan za a rubutasu a ka'ida sai a hade su da juna kamar haka:
Mustashfa مستشفي. Asibiti.
Nurun نور Haske
Mujtaba. مجتبي Majtaba
Hujratun حجرة Daki
Da'amun. طعام Abinci
A nan za a ga kamar layi ne aka yi aka ɗora haruffan a kai, kamar yanda ya gabata a misalan baya. Haka kuma idan muka lura da kyau za mu gano cewa haruffa masu jela Ana yanke jelar ne lokacin da za a haɗa su da harafin gabansu. Harafin karshe ne ba a yanke masa jelarsa kamar haka:
Mu'allimu. م ع ل م Malami sai ya koma haka معلم
Waɗannan misalai na nuna inda haruffan ke haduwa da junansu. Duk farkon kalma ta fara da ɗaya daga cikin haruffan larabci 28 da muke magana a kai. Saidai a kula a ga yanda kowanne ke canjawa. Ga kuma karin misalai a hoto dake kasa.
Masu bukatar sauran darusa da suka kuɓuce musu sai su Shiga wannan link suyi liking kuma su following domin samun sauran Darsuka ɗin 👇👇👇👇👇👇👇�
Page-https://www.facebook.com/111306253888584?referrer=whatsapp
Allah ya sa agane, kuma ya bamu ilimi mai Amfani. Ãmīn
No comments:
Post a Comment