Wednesday, October 27, 2021

MUTANE MA HAKA SUKE BALLANTAN DABBOBI

MUTANE MA HAKA SUKE BALLANTANA DABBOBI? Wata rana wani daga cikin magabata ya aika dansa kasuwa ya siyo masa hanta. Da ya siyo sai ya samu wuka mai kaifi ya yanyanka hantar. Sai ya bar wukar bai wanke ba, sai magensu ta zo tana lasar jinin da ke jikin wukar. Tana lasa harshenta na tsagewa jini ya biyo wukar. Da yaron nan ya zo ya ga magen tana ji wa kanta ciwo, sai ya daka mata tsawa; ya kore ta. Sai kawai magen nan ta dinga gurnani, tana nuna fushinta, ya hana ta abin da take jin dadi. Da yaron ya ga haka, sai ya ce: "Ikon Allah! Kina cutar da kanki, don na hana ki, sai ki ji haushi na. Sai baban nasa ya jiyo shi yana magana, sai ya ce da shi: "Kai da wa kake magana kai kadai. Sai ya ce: baba ka ji, ka ji... Sai Baban ya ce: ai ba dabbobi ba, mutane ma haka suke. Idan suna aikata abin da zai cutar da su (sabon Allah) idan ka hana su sai su ji haushinka. Sai ya ce: to, baba ba sai a kyale su ba tun da kansu suke cutarwa. Sai ya ce: A'a, ai idan ka kyale su suna aikata barna, ba ka hana su ba, idan azaba ta zo, sai ta hada da kai. Amma idan ka hana su, idan suka hanu, to kai da su duk kun tsira. Idan kuma ba su hanu ba, to kai ka kubuta. Wannan kisar sai ta tuna min hadisin: عن النُّعْمَانَ بْنَ بَشِيرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " مَثَلُ الْقَائِمِ عَلَى حُدُودِ اللَّهِ، وَالْوَاقِعِ فِيهَا، كَمَثَلِ قَوْمٍ اسْتَهَمُوا عَلَى سَفِينَةٍ، فَأَصَابَ بَعْضُهُمْ أَعْلَاهَا، وَبَعْضُهُمْ أَسْفَلَهَا، فَكَانَ الَّذِينَ فِي أَسْفَلِهَا إِذَا اسْتَقَوْا مِنَ الْمَاءِ مَرُّوا عَلَى مَنْ فَوْقَهُمْ، فَقَالُوا : لَوْ أَنَّا خَرَقْنَا فِي نَصِيبِنَا خَرْقًا، وَلَمْ نُؤْذِ مَنْ فَوْقَنَا، فَإِنْ يَتْرُكُوهُمْ وَمَا أَرَادُوا هَلَكُوا جَمِيعًا، وَإِنْ أَخَذُوا عَلَى أَيْدِيهِمْ نَجَوْا وَنَجَوْا جَمِيعًا ". أخرجه البخاري (٢٤٩٣)، والترمذي (٢١٧٣)، وأحمد (١٨٣٦١) TSOKACI: Kada zaton idan ka yi inkarin mummuwan abu, ba za a daina ba ya sa kana ganin munkari ka ki hanawa. ALLAH YA BA MU DACEWA

No comments:

Post a Comment