Friday, December 4, 2020

KASHI NA BIYU, TATTAUNAWAR HUZAIFAH (R.A) DA MANZON ALLAH (S.A.Ws) GAMEDA FITINUN DA ZASU AUKU

Akashi na ɗaya mun tsaya a daidai inda Huzaifah (R.A) yaji amsar Annabi (S.A.Ws), sa'annan ya ƙara nuna damuwarsa ƙwarai da gaske, don haka sai ya ci gaba da irin tambayoyi na irin bala'in da za su aukamma Musulmi.


Huzaifah:  'Ya Rasulallah! Wai shin yaya za mu samu wani alherin bayan wannan masifa?'


Annabi:  'Ih, alheri zai sauka bayan wannan, toh amma sai dai cibiyoyin jama'a ba za su kai irin na da ba (ta fuskar fahimtar abubuwa na addini).


Huzaifah:  'Wata masifar kuma za ta auku bayan wannan alheri?'

Annabi:  'Ih, sai dai a wannan lokaci akwai mutanen da za su ɓatar da jama'a su jefa su wuta.'


Huzaifah:  'Me ka ga ya kamata in yi idan na iske wannan lokaci?'


Annabi:  'Idan ka taras da wata ƙungiyar Musulmi sun haɗe karkashin Amir guda to ka bi su. Idan ko ba haka ba, toh ka guji bin duk wasu 'yan ƙungiyoyi, gwamna ka koma ƙurya ko kuma ka koma gindin bishiya (watau daji) kayi ta zama a can, har mutuwa ta zo maka.'


A lokacin da Huzaifah (R.A) ke shirin barin duniya, ya yi ta kuka saboda damuwa da kuma turarradi. Jama'a suka ce da shi


    Kana kuka ne don za ka bar wannan funiyar?


Ya ce: 'A'a ba wai ina kuka ba ne saboda haka, Ina ƙaunar in mutu. Ina kuka ne saboda a halin yanzu lokacin da nake shirin ƙaura daga nan duniya ban sani ba ko Allah Ta'ala Yana farin ciki da ni ko kuma a'a.'

              Daga nan sai ya yi addu'a:

'Ya Allah! Wannan shi ne lokaci na ƙarshe a rayuwata (ta duniya). Ka san cewa a ko da yaushe ina ƙaunarka. Don haka ka albarkaci saduwa ta da kai.'


Ya Allah muma ka albarkaci saduwar mu da kai Kasa aljannar Firdausi itace mskomarmu.


*✍️Ahmad Musa

TATTAUNAWAR HUZAIFA (R.A) DA MANZON ALLAH (S.A.Ws) GAMEDA FITINTUNU DA ZASU AUKU KASHI ƊAYA

*Ahmad Musa*

Huzaifa (R.A) yana ɗaya daga cikin Sahabban da suka yi suna. Ana yi masa laƙabi da 'Mai Sanin Asiri.' Manzon Allah (S.A.Ws) ya bayyana masa dukkan sunayen munafukai, sa'annan ya shaida masa irin dukkan fitinun da za su samu Musulmi a jere tun daga lokacin har zuwa tashin ƙiyama.


Ya bayyana masa cikakken (sunan mai tada fitinar, iyayensa da kuma wurin da ya fito da sauransu) da irin abin da zai faru wanda zai shafi kusan mutane ɗari uku ko fiye da haka. Huzaifa (R.A) yana mai cewa: 'Duk sauran mutane, Kowa yakan tambayi Manzon Allah (S.A.Ws) kyawawan abubuwa, amma ni nakan yi masa tambayoyi akan abubuwa marasa kyau, yadda zan iya kare kaina daga gare su.'


Daga nan sai ya ambaci irin abin da ya gudana tsakaninsu da Manzon Allah (S.A.Ws)


Huzaifah:  'Ya Rasulallah! shin za mu koma ga sharri bayan abubuwan da ka zo mana da shi na alheri?'


Annabi:  'Ih, wani sharrin na zuwa.'


Huzaifah:  'Za mu sake samun wani alherin bayan wannan sharri?'


Annabi:  'Huzaifah! Maza tafi ka yi ta karanta Alƙur'ani, kana tunani akan ma'anarsa, sa'annan ka bi dokokin da ke cikinsa.


Wannan abu ya sa Huzaifah ya ƙara nuna damuwarsa ƙwarai da gaske, don haka sai yaci gaba da irin tambayoyi na irin bala'in da za su aukumma Musulmi.


A dakace mu zamu cigaba da bayani akan tambayoyi daya masa gameda fitintunu dazasu auku akashi na biyu insha Allahu.


Muna rokon Allah Maɗaukakin sarki ya datar damu dukkan alkhairi ya kuma kare daga dukkan sharri.


https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Wednesday, November 11, 2020

JAHILCI BASHI DA MADOGARA A ADDININ GASKIYA

 

Idan dai rubutun Larabci a jikin ƙuɗi yana nufin Musulunci ne, mai yasa ake fassara littafin Bible da yaren Larabci? Sa'annan kutambayi jahilan da suka kai ƙarar CBN cewa Kasar Israel ma Musulunci sukewa aiki? tunda ga rubutun Arabic a jikin Kuɗinsu


Batun cire rubutun Arabic akan Naira:

Idan rikicin ne muma fa mun iya, kuma muna da abin cewa, sai muce:

1. A cire hoton Cross + daga jikin motocin Ambulance na Asibitocin Nigeria, dan Nigeria ba kasar Kiristoci bane.

2. Sai muce a soke hutun ranar Asabar domin 'yan Nigeria ba Yahudawa bane.

3. Sai muce a soke hutun ranar Lahadi, domin Nigeria ba kasar Kiristoci bane.

4. Sai muce a cire kalmar "Minister" daga sunan masu taimakawa shugaban kasa, domin Ministoci ba an dana su suyi aiki ma coci bane.

Domin kalmar mukami ne a Coci.

.

5. In ba haka ba sai muce dole a saka ranar Juma'a daga cikin ranakun hutu a Nigeria, dan akwai Musulmi a kasar.

6. Indai za'a cire rubutun Arabic a jikin Naira sai muce dole a cire rubutun Hausa da Yarbanci da Igbo a jikin Naira, domin kasar ba ta Hausawa da Yarbawa da Inyamurai bane.

7. Idan ance lallai za'a cire Arabic, sai muce don me aka dauko yare biyu daga kudu (Igbo da Yoruba) aka yi rubutu dasu a jikin kudin kasar mu.

Amma aka dauko yare daya tak (Hausa) daga Arewa.

Muma Arewa dole a saka yare biyu daga Arewa.

.

8. Su an basu hutun har guda biyar:

New year.

Hutun Easter.

Hutun good Friday.

Hutun Christmas.

Hutun Boxing day.

Mu kuma an bamu guda uku rak:

Hutun babbar sallah.

Karamar sallah.

Hutun Maulidi.

.

9. Muma dole a bamu hutu har guda biyar a Nigeria.

Kuma a kara da hutun New Islamic year.


.

Ba dai tone tone suke so ba? muma fa mun iya tone tonen da yafi nasu ma.


https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1


Crédit to Abdul-Hadi Isa Abdul-Hadi Isah Ibrahim

Thursday, October 22, 2020

MABIYA JAGORAN ZAMAN LAFIYA NA DUNIYA SUNYI ABIN AYABA MUSU

Ibnul kayyim Yana cewa addini gaba dayansa kyawawan dabi'u ne, don haka duk wanda ya fika kyawawan dabi'u to ya fi ka addini.


Kyawawan dabi'u suna tsayuwa ne akan turaku guda hudu;


1. HAKURI; Wanda shi ne yake sanya mutum ya zama mai juriya da hadiye fushi, kamar yadda yake sanya tafiya sannu-a-hankali,

da rashin harzuka da kuma rashin gaggawa cikin lamura, kuma yana sanya kamewa daga cutar da wani. Kamar yadda mu yan arewa mukayi a wannan lokaci da aka gona dukiyar yan'uwanmu kuma aka ma wasu kisan gilla



2. KAMEWA: Wacce ita ce take kai mutum ga barin kaskantattun lamura, da abubuwan da ba su dace ba, ta kuma sanya shi ya zama mai kunya, wanda hakan zai sanya shi ya guji karya da rowa da annamimanci da cin naman mutane, da duk wani abu mara kyau. Kamar dai yadda aka harzuka mu domin mufita zanga-zanga amma muka kame


3. GWARZANTAKA : Wacce ita ce take kai mutum zuwa ga kare mutuncin kansa, da aikata abin da zai bashi kima, da yin kyauta ta yadda zai iya rabuwa da abin da yake so,


KUMA gwarzantaka wani abu ne da mutum zai iya rinjayar abokin gabarsa da shi, ta hanyar mallake zuciyarsa yayin fushi, kamar yadda ya zo a hadisi. Hakika mun nuna gwarzontaka a lokacin da ake cin zarafin yan'uwanmu a yankin kudu


4. Adalci; Wanda shi ne zai sanya shi ya daidaita dabi'unsa ta yadda za su zama tsaka-tsaki tsakanin ko-in-kula da wuce gona-da-iri. Kamar dai yadda muka tabbatar da ɗabianmu ta son zaman lafiya


Duk wasu dabi'u masu kyau da ka gani suna faruwa ne daga wadannan turakun guda hudu.


YA ALLAH KA BAMU KYAWAWAN DABI'U KUMA KAYI MANA MAGANIN ABINDA BAMA IYA YIWA KANMU.


https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

HANYA MAFI SAUKI DOMIN MAGANCE KO WACE IRIN FITINA

A Zamanin Manzon Allah (S.A.Ws) Kafirai Sun Takurawa Sahabannsa da Cin zarafi da kuma kuntatawa Da Yaga Irin Halin Kunci Da Takurawar da Makiya Kafirai Da Munafukan Sukeyi Musu, Sai Yayi Musu Huduba Yace Dasu Ya Ku Jama'ar Musulmi Kuyisani Cewa Wannan Halin Da Kuke Ciki Na Musifa Bakome Bane, kuma duk abubuwan nan da suke yi muku, na karshen zamani zasu fi Muni.


Ku sani Fitina Da Bala'i Suna Nan Tafe Akarshen Zamani Idan Zamanin Yazo Zakuga Fitina Da Musifu Da Bala'o'i Sun Kunno Kai Sai Ayi Ta Addu'a Sai Bala'in Da Musifa Sunyi Kamar Sun tafi Sai Wata Musifar Da Bala'in Su Kunno Kai Wanda Sukafi Nabaya hadari.



Manzon Allah (saww) Yaci gaba da cewa Awannan Lokacin Mutane Sunrude Kai Kace Bazasu Mutuba Sun Rasa Ya Zasuyi.


Sai Yace Shawarar Da Zan bawa Al'ummata Na Wannan Zamanin Itace Su rika tunanin Ya Zanyi In cika Da Imani, Yace Duk Wanda Yariki Ya Zanyi Incika Da Imani Shine Yayi Maganin Wannan Musifar Shine Ya Kaucewa Wannan Bala'in.


Amma ba ka tsaya kana tunanin Ya wannan Musibar zata kare ba.


Abin Nufi anan shine, ka rika tunanin cewa;


Yaya Zanyi In daina Giba (Idan har kana yi).


Yaya Zanyi in daina zina (Idan har kana yi).


Yaya Zanyi In daina Sata (Idan har kanayi).


Yaya Zanyi In daina Luwadi (Idan har kana yi).


Yaya Zanyi In daina Madigo (Idan har kina yi).


Wannan Shine Tunanin da Ya kamata Mutum ya tsaya yi ba Yaya wannan Bala'in Zai kwanta ba.


Ya Allah Ina Rokon ka dan Sunayen ka Tsalkakakku Masu daraja Wayanda Muka sani da Wayanda Bamu sani ba, Ya Allah kasa Mu cika da Imani, Ya Allah ka Tsare Mu da Azabar kabari, Ya Allah kasa Aljanna ta zamo makomarmu.


https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Thursday, October 8, 2020

2. TAKATACCEN TARIHIN RUKAYYAH (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)

 2. TAKATACCEN TARIHIN RUKAYYAH (R.Ah) YAR ANNABI (S.A.Ws)


An haife ta shekaru uku bayan haihuwar Zainab (R.Ah), a lokacin da Manzon (S.A.Ws) yake da shekaru 33. Ta auri Uthbah dan Abu Lahab, Baffan Annabi (S.A.Ws). To amma a lokacin tun ba su fara zama tare ba aka saukar da Surah, Al-Lahab. Abu-Lahab ya kira 'ya'yansa Uthbah da Utaibah (wanda shi ne ya auri Ummu Kulthum), har wayau, wata ' yar ta Annabi (S.A.Ws), inda ya ce da su:

Idan ba sakin 'ya'yan Muhammadu ku ka yi ba, ba zan sake kallon fuskokin ku ba.


Sun saki matan nasu. Daga baya aka ci Makkah da yaki, Uthbah ya kar6i Musulunci. RUKAYYAH (R.Ah) bayan wannan saki ta auri Sayyadina Uthman (R.A). Mijin da matar sun yi Hijirah zuwa Habasha har sau biyu.


Tun lokacin da Annabi (S.A.Ws) ya shaida wa Sahabai cewar yana sa ran ya samu umarni daga wajen Allah Ta'ala na yin Hijirah zuwa Madinah, sai suka fara matsawa zuwa can tun kafin Annabi (S.A.Ws) ya yi Hijirasa. Uthman (R.A) da Rukayyah (R.Ah) sun kuma yi Hijirah zuwa Madinah kafin Annabi (S.A.Ws) ya isa garin.


A lokacin yakin Badr, Rukayyah ba ta da Lafiya (wanda ta cika sanadin wannan cuta). Don haka sai Annabi (S.A.Ws) ya bukaci shi Uthman (R.A) ya ci gaba da zama a Madinah don lura da ita. An samu labarin irin nasarar da aka samu a yakin Badr a can Madinah yayin da jama'a ke komowa daga jana'izar Rukayyah. Don haka da Annabi (S.A.Ws) bai samu damar halartar jana'izarta ba.


Rukayyah (R.Ah) ta haifi da a lokacin da suke Habasha. An sa masa suna Abdullah, kuma yana raye mahaifiyar ta rasu, ko da yake shima ya rasu a shekara ta 4, bayan Hijirah. A lokacin yana da shekara 6.


Insha Allahu rubutu na gaba akan Ummu Kulthum (R.Ah) yar Annabi (S.A.Ws) amma kafin nan zan daniyi rubutu akan dan Ahmad Deedat saboda ya samu rauni a safiyar yau.

Muna kuma rokon Allah Ta'ala ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen.

Saturday, October 3, 2020

YADDA TALLAFIN SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI ZAI GUDANA

✍️

Ahmad Musa

Rajista don Tallafin Biyan Kuɗin sashi na farko ya fara ne a ranar Litinin, 21 ga Satumba. Kamar yadda yake a Satumba 25, 2020, tashar aikace-aikacen ta rubuta kusan masu nema 342,500.


A halin yanzu, sashi na biyu na aikace-aikacen neman tallafin  ya fara a ranar 1 ga Oktoba (01/10/2020).


Tsarin da 'yan Nijeriya 9,009 za su amfana a kowace jiha da kuma Babban Birnin Tarayya Aikace-aikacen tallafi na biyan kuɗin ya shiga matakin tabbatarwa



Tsarin zai kasance acikin makonni Biyu a kowani kusurwa uku a duk fadin kasar


Kusurwa na farko za'a fara yin registan ne a ranar ɗaya ga watan Oktoba (01/10/2020) har zuwa Goma ga watan (10/10/2020) a Jihohin

1. FCT

2. Lagos

3. Ondo

4. Kaduna

5. Borno

6. Kano

7. Bauchi

8. Anambra

9. Abia

10. Ribas

11. Plateau

12. Delta


Kusurwa na BIYU za'a fara ne a ranar 19 ga watan Oktoba (19/10/2020) a Jihohin

13. Taraba

14. Adamawa

15. Bayelsa

16. EDO

17. Ogun

18. Ekiti

19. Katsina

20. Kebbi

21. Kogi

22. Kwara

23. Enugu

24. Ebonyi


Kusurwa na Uku kuma za'a fara a ranar 9 ga watan Nuwamba (09/11/2020) har zuwa 21 ga watan (21/11/2020) a Jihohin

25. Akwa-Ibom

26. Cross-River

27. Zamfara

28. Yobe

29. Sokoto

30. Nasarawa

31. Niger

32. Imo

33. Oyo

34. Osun

35. Jigawa

36. Gombe

37. Benue


Yadda zaka samu wannan TALLAFIN shine

Zaka  shiga wannan website ɗin da zai kaika har wurin direct, shine:👇

https://survivalfundapplication.com/auth/register

Ko kuma Main site din ko board din a👇

www.survivalfund.com

 kayi yi rijistan da Ministry of Youths and Sports. Idan kayi zasu tun-tube ka gabar ta email dinka ko ta lambar wayar idan za'a fara bayar da rance.

.

Abubuwan da ake bukata:

1. Active email, email wanda yake aiki.

2. Lambar waya.

3. Address.

4. Wadanda zasu cika, maza ko Mata, daga shekara 18 zuwa 35.

5. C.A.C registration number.

Amma idan baka da CAC Number, baka taba rijistan da hukumar ba, toh ka tsallake shi kawai, registration din zai yiwu ko baka da lambar CAC din.

.

Allah yasa duk wanda ya cika ya dace...

Allah ya taimaki wannan shugaban kasa namu mai kokari da son taimakawa al-umma

Monday, September 21, 2020

LABARI TARIHIN MASARAUTAR ZAZZAU

Wannan wata makala ce da muka yi bayan da muka bukaci ku aiko tambayoyinku a kan tarihin masarautar Zazzau. BBC ta kwashe lokaci mai tsawo wajen bin diddigin amsoshin tambayoyin naku daga masana tarihin wannan masarauta ta Zazzau. Ita dai masarautar Zazzau tana daya daga cikin muhimman masarautun kasar Hausa da ma yankin Afirka ta yamma. Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni cewa, Zazzau wata dadaddiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun daruruwan shekaru da suka gabata, wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin musulunci. Zazzau Emirate Yadda kalmar ‘Zazzau’ ta samo asali Tushen wannan kalma ta ‘Zazzau’ yana da rassa biyu, na farko yana da nasaba da yanayin kasar ta Zazzau, wanda daga Katsinanci ke nufin ‘zo-zo’, wato kasa mai laka, ba mai rairayi ba, wadda za a iya yin shuka a kanta, kuma ta tsiro. A wani kaulin kuma ‘Zazzau’ na nufin wani takobi, wanda ja-goran jama’a yakan dauka ya jagoranci jama’a a wajen yaki. Mai daukar wannan takobi ba sarki ake kiransa ba, a wancan lokaci ana kiran sa ne ‘Madau-Zazzau’, wato ‘Mai Dauke da Zazzau’. Asalin Kalmar Zariya Zariya kalma ce da ta samo asali daga sunan Zariya ‘yar Sarki Bakwa Turunku, wadda kanwa ce ga Sarauniya Amina Bambancin Zazzau da Zariya Zazzau masarauta ce, wadda ta kunshi dukkan kasashe da garuruwan da ke bin masarautar. Zariya kuwa shi ne babban birnin da sarki yake zaune da hakimai da ’yan majalisarsa ana gudanar da mulki. Sauran hakimai da suke da kasashe suna kawo wa sarki rahoto, su kuma ana aika masu da umarni. Kafuwar Masarautar Zazzau Mahaya dawakin Zazzau A zamanin maguzanci, wato shekaru aru-aru da suka gabata, babu wani addini da ya shigo, sai al’adu ko rayuwa irin ta maguzanci. Kuma kaura daga wannan waje, a koma wancan waje, ita ce al’adar Bil’Adama, a kokarin a kokarin neman wajen da zai zauna ya sami ingatacciyar rayuwa. Mafi yawan ayyukan da jama’a kan yi a lokacin su ne, noma da kiwo. Wannan lokaci ne kuma masana tarihi ke kira zamanin ‘Zo-zo’, wato zamanin maguzanci, wanda ya kasance tun kafin shigowar addinin musulunci. Lokacin da al’umma suka rika taruwa, suna samun shugabanci, har sarakunan Habe suka fara mulki, aka samu kafuwar Hausa Bakwai, wato zuri’ar Bayajidda da Sarauniya Daurama. Kuma Zazzau na daya daga cikin kasashen da aka ba ’ya’yan Bayajida mulki. Bayanin da aka samo daga bakin Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Gunguma shi ne sarkin Zazzau na farko, kuma ya yi tafiyayya ne daga Daura, ya bi ta Kano da Rano, kuma ya fara yada zango a Kangi. Wadanda suka biyo bayansa sun kafa biranen mulkinsu ne a Kawari da Rikocci da Wuciciri da kuma Turunku, kafin su je Zariya. Nohir ta auri wani bako, ta haifa masa da namiji, kuma aka sa wa dan suna dan Bakwa Turunku. Daga baya sunansa ya koma Bakwa Turunku, wanda ya gaji sarautar kawunsa Kawanissa a shekarar 1536. Bakwa Turunku ya yi sarauta ne a garin Turunku, kuma har yanzu akwai sauran kufan masarautar ta Turunku a can kasan tsaunukan da suke shimfide a yankin gabashin Zariya. Kafuwar birnin Zariya Kamar yadda aka sami labari daga wajen Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Zariya ‘yar Bakwa Turunku, kuma kanwar Sarauniya Amina ce ta kafa birnin Zariya, don haka ake kiran birnin da sunanta. Hakan kuwa ya biyo bayan yadda hedikwatar mulki ta Zazzau ta yi ta sauya wuri saboda matsalar rashin ruwa, a zamanin mulkin Bakwa Turunku, wato mahaifin Sarauniya Amina da Zariya. Hedikwatar ta tashi daga Bomo zuwa Wucicciri zuwa Ancau zuwa Kargi, ta koma Turunku. A wancan lokaci an ce sai Bakwa ya ga Turunku ta yi wa mutanensa kadan a matsayin hedikwatar mulki, ga matsalar ruwa ana fama da ita. Saboda haka, sai ya koma Zariya a shekarar 1537. Daga nan ne kuma masarautar Zazzau ta koma Zariya. Amma ba a shiga Zariya kai tsaye ba, sai Bakwa Turunku ya gaya wa ‘yarsa Zariya, cewa ta je wajen kufannin iyayensu, wato Kufena kenan, ta je ta fara zama a wurin, kuma akwai rafi a wajen. Sai dai da Sarauniya Amina, wadda ita ce 'ya a wajen Zariya, ta dawo daga yake-yakenta, sai ta ce wurin ya yi fadi da yawa. Idan aka gina hedikwatar mulki a wurin a wancan zamani na yake-yake, to mahara za su iya kai masu hari. Saboda haka, ta ce a koma kusa da rafin da ake kira Fadamar Bono a cikin gari, wanda daga baya da Fulani suka karbi mulki suka mayar da sunan zuwa Fadamar Sarki. Da aka gama sake shata gari, sai Sarauniya Amina ta sa wa wannan zagayen da’irar da aka yi sunan kanwarta, wato Zariya. Don ta girmama suna ‘yar uwarta, kuma dalilin sunan garin Zariya kenan. Kuma ta gina gida a cikin gari, inda ya zama fadar Zazzau, inda mahaifinta ya zauna, kuma har yanzu nan ne fadar masarautar Zazzau. Ana kiran gidan da sunan ‘Gidan Bakwa’. Asalin Ganuwar Zazzau A zamanin da, mai karfi shi ke da iko a kasashen Hausa da sauran wurare, saboda haka kowacce kungiyar al’umma da suke so su yi karfi, sai sun kewaye kansu, yadda mahara ba za su shigo masu ba. Wannan shi ne dalilin ganuwa a kasar Hausa, kuma inda duk aka yi ta, an yi ne don wurin ya zama hedikwatar mulki na al’ummar wajen. To, a Zazzau wadanda suka fara yin ganuwa a cikin gari, aka mayar da cikin gari hedikwata, wato babban birnin mulki na Zazzau, su Bako Turunku ne, mahaifin Sarauniya Amina ta Zariya. Ganuwar Zariya, ita ce ta dauka tun daga dutsen Kufena, ta kewaya zuwa Hanwa, ta shigo wajen barikin soja, inda ake kira Jushin Waje. Ta biyo ta Kofar Galadima, ta Kofar Kona, ta hada da rafin Saye, sannan ta koma ta Gwargwaje, ta hadu da Wusasa, kana ta koma Kufena. Saboda sanin dabarun yaki, sai Sarauniya ta sa bawanta, wato Bono, ya je ya sara da’ira da rafin Sarki a tsakiya ya kewaya aka yi kofofin garin guda takwas, wadanda suka hada da Kofar Kibo, da Kofar Kona da Kofar Galadima, da Kofar Bai, da Kofar Doka wadda a da ake kira Kofar Kano, da Kofar Jatau, da Kofar Kuyambana da kuma Kofar Gayan. Sarauniya Amina Sarauniya Amina Habe ce ta Zazzau, sai dai wasu masana tarihi na kallon ta a matsayin Sarauniya, amma ba Sarki ba ce, don haka babu sunanta a jerin sarakunan Habe. Ma’ana, akwai sarautu da ake ba ’ya’ya mata a da a karkashin sarautar Habe. Alal misali, akwai Sarauniya, akwai Gimbiya, akwai Iya, akwai Madanni, da dai sauran su. Duk wadannan sarautu ne na ’ya’yan sarakunan Habe. Saboda haka, Sarauniya Amina ba wai ta zama ita ce Sarki ba, a lokacin mahaifinta (Bakwa Turunku) yana sarki, ita kuma tana matsayin sarauniya, wato babbar ’yar sarki. Bisa al’ada, babban dan sarki shi ne shugaban rundunar sojoji na wannan masarauta. To, ita Amina ita ke rike da wannan kambi, kuma ita ta yi ta yake-yake. Ta buga daga Zazzau ta yi arewa har Kano, har Katsina, ta kare iyakokin masarautar Zazzau. Ta yi kudu da yamma, don kara fadi kasa da karfin mulki, kuma da haka ne ta dangana da kasar Naija ta yanzu, ta dangana da kasar Idah, wato kasar Attah Gara a jihar Kogi. Ta je har kasar Nasarawa ta yau, saboda karfin yaki da iya gudanar da yaki da jaruntaka. Tana da rundunoni da take jagoranta, kuma duk inda suka tunkara suna yin nasara, kamar yadda tarihi ya nuna. QUEEN AMINA Sarakunan Habe Tarihi ya nuna cewa, an yi sarakuna sittin na Habe, wadanda suka mulki masarautar Zazzau tun daga kan Gunguma, wanda shi ne ya fara yin sarauta a matsayin ‘Madau-Zazzau’ na farko a wancan lokaci, kuma shi jika ne na Bayajidda. Habe sun kwashe shekaru fiye da dari suna mulki, har ya zuwa lokacin mulkin Sarkin Zazzau Makau, wanda shi ne na karshe a jerin sarakunan na Habe, wanda shi ne ya fara zuwa Suleja (wadda aka fi sani da Abu-Ja tun asali). Ga kuma jerin sunayen sarakunan na Habe: Gunguma Matazu Tumsah Tumusa Suleman Maswaza Dinzaki Nagogo Katchina Nawanci Macikai Kawo Bashi Kar Majidadi Dihirahi Jinjiku Sakannu Monan Abu daga shekarar 1550 zuwa 1530 Gidan Dan Masukanan daga shekarar 1530 zuwa 1532 Nohir daga shekarar 1532 zuwa 1535 Kawanissa daga shekarar 1535 zuwa 1536 Bakwa Turunku daga shekarar 1536 zuwa 1539 Ibrahim daga shekarar 1539 zuwa 1566 Karama daga shekarar 1566 zuwa 1576 Kafo daga shekarar 1576 zuwa 1578 Bako daga shekarar 1578 zuwa 1581 Aleyu I daga shekarar 1581 zuwa 1587 Isma’ilu daga shekarar 1587 zuwa 1598 Musa shekarar 1598 Gadi daga 1958 zuwa 1601 Hamza shekarar 1601 Abdullah daga shekarar 1601 zuwa 1610 Burema daga shekarar 1610 zuwa 1613 Aleyu II daga shekarar 1613 zuwa 1640 Muhammad Rabo daga shekarar 1640 zuwa 1641 Ibrahim Basuki daga shekarar 1641 zuwa 1654 Bako II daga shekarar 1654 zuwa 1657 Sukana daga shekarar 1657 zuwa 1658 Aeyu III daga 1658 zuwa 1665 Ibrahim daga shekarar 1665 zuwa 1668 Muhammad Abu daga shekarar 1668 zuwa 1686 Sayo Ali daga shekarar 1686 zuwa 1696 Bako Dan Musa daga 1696 zuwa 1701 Is’haq daga shekarar 1701 zuwa 1703 Burema Ashakuka 1703 zuwa 1704 Bako Dan Sunkuru daga shekarar 1704 zuwa 1715 Muhammad Dan Gunguma daga shekarar 1715 zuwa 1726 Uban Bawa daga 1726 zuwa 1733 Muhammad Gani daga shekarar 1733 zuwa 1734 Abu Muhammad Gani shekarar 1734 Dan Ashakuku daga shekarar 1734 zuwa 1737 Muhammad Abu daga shekarar 1737 zuwa 1757 Bawo daga shekarar 1757 zuwa 1759 Yunusa daga shekarar 1759 zuwa 1764 Yakubu daga shekarar 1764 zuwa 1767 Aleyu IV daga shekarar 1767 zuwa 1773 Cikoku daga shekarar 1773 zuwa 1779 Muhammad Maigamo daga shekarar 1779 zuwa 1782 Is’haq Jatau daga shekarar 1782 zuwa 1802 Muhammad Makau daga shekarar 1802 zuwa 1804 Yadda wasu wurare suka fita daga masarautar Zazzau Lokacin da Shehu Usman Danfodiyo ya kawo jihadi a wuraren Hausa Bakwai da Banza Bakwai, Malam Musa yana jagorancin yaki. A tarihince, an ji cewa an kama Zazzau ba tare da an kashe ko da mutum daya ba. Malam Musa ya shiga Zazzau ta Kofar Bai, a lokacin sarkin Zazzau na karshe na Habe, Sarki Makau ya fita da dakarunsa, ya bi hanyar Hunkuyi, hanyar Kudan, hanyar Kano, tun da an ba shi labari cewa, Malam Musa zai biyo ta hanyar Kano, to sai ya bi wannan hanya. Shi kuma Shehu Usman Danfodiyo, sai ya ba Malam Musa shawara to ya kauce wa wannan hanya. Ana ganin hakan ba ya rasa nasaba da irin ilhamar manyan malamai na da, bayin Allah, suna addu’a, suna rokon Allah Ya ba su haske da ilhamar yadda abubuwa za su kasance. Sai aka fada wa Malam Musa, cewa kar ya bi waccan hanya ta Kano, ya zagaya ya bi ta garin Likoro. Kuma haka ya bi, ya zagaya ya bi Farin Kasa da ke kasar Soba ta yanzu, sannan ya bullo wa Zariya ta Kofar Bai, ya kuma shiga garin. Bayan shi kuwa Sarki Makau yana ta baryar arewa maso gabas, yayin da Malam Musa ya bullo ta arewa maso yamma, saboda haka ba a hadu an gwabza yaki ba. Da haka Malam Musa suka shiga cikin birnin Zariya, suka rufe kofofin birnin, Sarki Makau na waje, yana jira, sai labari ya isa gare shi, cewa ai Fulani sun shiga Zariya sun kulle kofofi, wato an kori su Sarki Makau kenan. Daga can Sarki Makau ya gudu, ya nufi kudanci, ya je nan, ya je can, don a lokacin akwai sarakuna irin su Sarkin Fatika da Sarkin Kajuru da Sarkin Kauru da sauran su, wadanda duka da suna bin Sarkin Zazzau na Habe. Amma da Fulani suka zo, sai suka yi wa Sarki Zazzau Makau tawaye, suka bi Fulani. Suka ci gaba da biyayya, suka kuma zauna a karkashin Sarkin Zazzau musulmi, Bafulatani. Da haka fadin kasar Zazzau ya fara raguwa. Bayan da Sarki Makau ya bar Zazzau, ya nufi kudanci yana neman goyon bayan kananan sarakunasa da ke can gefe, wadanda tun zamanin Sarauniya Amina aka ci su da yaki, suna biyayya ga masarautar Zazau. To, Shehu Usman Danfodiyo ya ce, idan mayakan Malam Musa sun sadu da wani wuri da wani babban dutse a kudu maso yamma da Zazzau, su tsaya a wurin. Iyakar daular da yake so ya tabbatar kenan. Inda Makau ya tafi, ya wuce wannan wuri, to, kar su bi shi. Hakan ne kuma aka yi. Wannan shi ya sa aka kafa Zazzau Suleja a wurin, shi Sarkin Zazzau Makau shi ya tsaya a nan, kuma dakarun Malam Musa ba su ci gaba da bin su ba, suka koma Zariya. Saboda haka, ba a yi yaki da ya wuce wannan wuri ba. Wato dai masarautar Suleja daga Zazzau ta fito, don haka har gobe masu sarautar Suleja suke kiran kansu da mukamin Sarkin Zazzau, amma Suleja. Shi ya sa za ka ji ana cewa, Sarkin Zazzau Suleja. Kuma duk sunayen unguwannin da ke cikin birnin Zariya, su ne za ka samu a Suleja, kamar su Kwarbai, Anguwan Fatika, su Kusfa, Anguwan Iya da dai sauransu. Saboda sun maimaita wadannan abubuwa da suka baro a Zariya. Sai dai kuma a wani kaulin, an ce Malam Musa ya ziyarci Zariya ne tun kafin jihadin Shehu Usumanu Danfodiyo, kuma ya zauna a birnin yana koyar da karatun Al-Kur’ani da sauran littattafan addinin musulunci. To, da jihadin ya shigo, ya kasance yana cikin mukarraban Mujaddadi Shehu Usumanu Danfodiyo, kuma ya sami matsayin ja-goran yaki. Da haka Malam Misa da mayakansa suka kai hari ga Muhammadu Makau, Sarki na sittin a jerin sarakunan Habe, a ranar Asabar goma ga watan Zulhaji a shekarar 1804, lokacin yana filin sallar Idi da ke wajen garin Zariya. Duk da yake dai Muhammadu Makau yana tare da dimbin mazaje tare da shi a lokacin harin, an ci shi da yaki. Saboda ba sa iya komawa cikin gari su dauko makamansu. Don haka aka tilasta masa tserewa tare da wasu magoya bayansa zuwa Zuba da ke kudancin yankin masarautar Zazzau, inda a can ne ya yi tirjiya ga hare-haren Fulani. Daga cikin mutum dubu uku da ke tare da shi akwai ‘yan uwansa Abu-Ja da Abu-Kwaka. A wannan wuri ne Sarki Makau ya zauna, kuma wadanda suka gaje shi suka karfafa, suka kafa wata sabuwar masarautar Zazzau ta Habe mai cin gashin kanta a kasar da daga baya aka rika kira Abuja. Da ma kuma jama’ar yankin suna biyayya ga sarakunan Zazzau. Wannan masarauta ta Habe ta rayu har ya zuwa lokacin zuwan Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, duk kuwa da matsanantan hare-hare da Fulani ke kai masu. Kuma sarakunann Zazzau na Abuja, sun rike mukaman da suke da su na asali tun daga Zariya. Sarakunan Habe na Suleja (Abu-Ja) Sarakunan Habe na Suleja (Abuja), sun samo asali ne daga tsatson Is’haq Jatau, Sarkin Zazzau na hamsin da tara a Zariya, wanda ya yi sarauta daga shekarar 1782 zuwa 1802. Ga kuma jerin sarakunan da suka yi mulki a wannan masarauta ta Suleja (Abu-Ja) daga farko zuwa yau: Muahammadu Makau daga shekarar 1804 zuwa 1825 Abu-Ja daga shekarar 1825 zuwa 1851 Abu-Kwaka daga shekarar 1851 zuwa 1877 Ibrahim Iyalai daga shekarar 1877 zuwa 1902 Muhammad Ganu daga shekarar 1902 zuwa 1917 Musa Angulu daga shekarar 1917 zuwa 1944 Suleman Barau daga shekarar 1944 zuwa 1979 Ibrahim Dodo Musa daga shekarar 1979 zuwa 1993 Muhammad Awwal Ibrahim daga shekarar 1993 zuwa yanzu A yanzu dai akwai masarautu biyu na Zazzau, wato Zazzau ta Fulani da ke da hedikwata a Zariya, da kuma Zazzau ta Habe mai hedikwata a Abuja wato wurin da a yanzu aka fi sani da Sule-Ja). Sarakunan Fulani A lokacin da Shehu Usmanu Dafodiyo ya yi jihadi daga shekarar 1804, kasar Zazzau ta dangana da inda Habe suka tsaya, wato kasar Idah a jihar Kogi ta yau. A zamanin Sarkin Zazzau, Malam AbdulKarim, daga baryar kudu masarautar Zazzau ta dangana da har zuwa inda a yanzu ake kira Nasarawa, kuma har zuwa gabar kogin Benuwai. A baryar arewa kuwa ta yi iyaka da sauran kasashen Hausa bakwai, kamar Katsina ta fuskar arewa, da Kano ta fuskar arewa maso gabas, sai Bauchi da Filato a arewa maso yamma. Kuma daga Zazzau ne ake nada sarakunan kasashen da ke karkashin masarautar ta Zazzau Sarkin Zazzau na farko a karkashin daular Usumaniyya, shi ne Malam Musa, wanda Shehu Usumanu Danfodiyo ya ba tutar jaddada musulunci a kasar Zazzau, kuma na karshe kuma shi ne Sarkin Zazzau Makau wanda Turawan mulkin mallaka suka kawar. Ga kuma jerin sunayen sarakunan Zazzau na Fulani: Malam Musa daga shekarar 1804 zuwa 1821 Malam Yamusa deaga shekarar 1821 zuwa 1834 Malaam AbdulKarimu daga shekarar 1834 zuwa 1846 Malam Hammada daga shekarar 1846 zuwa 1853 Mamman Sani daga shekarar 1846 -1853 Sidi AbdulKadir daga shekarar 1853-1853 Malam AbdusSalami daga shekarar 1853 zuwa 1854 Malam AbdulLahi (nadi na farko) daga shekarar 1857 zuwa 1871 da (nadi na biyu) daga shekarar 1874 zuwa 1879 Malam Abubakar daga shekarar 1879 zuwa 1888 Muhammadu Sambo daga shekarar 1888 zuwa 1890 Muhammadu Yero daga 1890 zuwa 1897 Sarki Malam Kwasau daga 1897 zuwa 1902 (shi ne sarki na karshe kafin zuwan Turawa) Zuwan Turawan mulkin mallaka Alu Dan Sidi (shi ne Sarkin Zazzau wanda Turawan mulkin mallaka suka fara nadawa) daga shekarar 1903 zuwa 1920 Sarki Dalhatu daga shekarar 1920 zuwa 1924 Sarki Ibrahim Dan Sarkin Zazzau Kwasau daga shekarar 1924 zuwa 19337 Sarki Jafaru daga shekarar 1937 zuwa 1959 Alhaji Muhammadu Aminu daga shekarar 1959 zuwa 1975 Alhaji Shehu Idris (wanda ke kan karagar mulki yanzu) daga shekarar 1975 zuwa yau Gidajen Sarautar Zazzau A karkashin Daular Fulani, masarautar Zazzau tana da gidaje hudu, wadanda suka hada da: · Gidan Mallawa, wanda Malam Musa ya kafa, 1. Sarkin Zazzau Malam musa 2. Sarkin Zazzau Malam Abdulkadir dan Musa 3. Sarkin Zazzau Malam Abubakar dan Musa 4. Sarkin Zazzau Malam Alu Dan Sidi. · Gidan Barebari, wanda Yamusa ya kafa, 1.Sarkin Zazzau Malam Yamusa 2. Sarkin Zazzau Malam Hammada dan Yamusa 3. Sarkin Zazzau Malam Mamman Sani dan Yamusa 4. Sarkin Zazzau Malam Abdullahi dan Hammada 5. Sarkin Zazzau Malam Yero dan Abdullahi 6. Sarkin Zazzau Malam Kwasau dan Abdullahi 7. Sarkin Zazzau Malam Dalhatu dan Yaro 8. Sarkin Zazzau Malam Ibrahim dan Kwasau 9. Sarkin Zazzau Malam Ja'afaru dan Isiyaku · Gidan Katsinawa, wanda Malam AbdulKarim ya kafa, 1. Sarkin Zazzau Malam Abdulkarim 2. Sarkin Zazzau Malam Sambo dan Abdulkarimu 3. Sarkin Zazzau Malam Muhammadu Aminu 4. Sarkin Zazzau Malam Shehu dan Idrisu Auta · Gidan Sullubawa (Fulani), wanda Malam AbdusSalam ya kafa. 1. Sarkin Zazzau Malam Abdulsalam Kowanne gida dai ya biyo asalin inda wanda ya kafa shi ne ya fito. Mallawa Fulanin Futo Toro ne da suka fito daga kasar Mali, Barebari kuma sun fito ne daga Kukawa a yankin da a yau aka fi sani da Jihohin Barno da Yobe, amma asali su Fulani ne, kuma ana kallon su ne a matsayin Fulani. Saboda haka ne ma ake kiransu da Fulata-Barno. Haka Sullubawa Fulani ne da suka fito daga yankin jihohin Sakkwato da Kebbi, kuma yadda AbdusSalami Basullube ya sami sarautar Zazzau kenan. Yadda aka sami gidaje hudu na sarautar Zazzau Gidan sarautar Zazzau ya kasu hudu ne, saboda Zazzau kasa ce wadda ta tattara dimbin al’umma da suka fito daga wurare daban-daban, don neman ilimin addinin musulunci. Saboda haka, a lokacin da jihadin Shehu Usman Danfodiyo ya zo, an sami malama ne masana ilimin addinin musulunci, da shari’o’i, da kuma ka’idar mulki na musulunci. A lokaci ba wai ana la’akari ne da cewa wane ya gada ko wane ne ya gada ba, ana neman wanda zai zama khalifa, don tabbatar da kafuwar addinin musulunci a Zazzau. Zazzau wata cibiya ce, tun ma kafin jihadi Shehu Usman Danfodiyo, saboda kasancewarta ‘Zo-zo’, kasa mai albarka, mai daukar komai da komai na noma, tana da laima da ni’ima. Kowa yana son ya je ya zauna a Zazzau, ya amfana ta fuskar noma da kiwo. Wannan ya sa Fulani da yawa suka zauna a Zazzau tun zamanin mulkin Habe, kuma da yawansu abin da suke yi baya ga kiwo, shi ne karatun addini. Kuma lokacin da dan uwansu Shehu Usman Danfodiyo ya bullo, sun kai masa gaisuwar caffa, suka yi masa mubayi’a, ya yarda da su. Suka zauna da shi, suka yi karatu tare da shi, suka yi yake-yaken da aka yi tsakanin Sarkin Gobir da Usman Danfodiyo. Tun kafin a yi ganuwa, akwai mutane, wato Fulani, irin su Malam Musa da Yamusa da Malam AbdulKarim da su AbdulSalam da ke zaune a cikin garin Zariya, suna koyarwa ta addinin musulunci. Da suka ji bullowar Shehu Usman Danfodiyo yana zuwa wurare daban-daban yana kira da a gyara addinin musulunci, suka yadda da abin da yake yi, suka yi masa mubaya’a Tarihi ma ya nuna cewa, Malam AbdulKarim ya zauna da Shehu Usman Dan Fodiyo, ya yi karatu a wajensa. Shi kuwa Malam Musa kusan tsaran Shehu Mujaddadi ne, kuma tare suke tafiye-tafiye. Gidan Malam Musa Malam Musa shi aka ba tutar sarauta a lokacin da jihadi ya iso Zariya, Malam Musa shi aka ba wannan tuta, don ya yi jagoranci, kuma bayan mutuwar Malam Musa, ba a mayar da sarautar ta zama gado ba. To, bayan mutuwarsa ba a mayar da abin ya zama gado ba, sai aka ba wani daga cikin malaman da suke tare da Shehu Usman Danfodiyo, wato Malam Musa. Kuma Shehun ne da kansa ya ba shi tutar halifanci. Gidan Malam Yamusa Kana sai Shehu Usman Danfodiyo ya ba Malam Yamusa shugaban rundunar sojojin yaki na Malam Musa a matsayin Madakin Zazzau. Gidan Malam AbdulKarimu Shi kuma Malam AbdulKarimu, Shehun ya ba shi sarautar Sa’in Zazzau, wato mai ilimin rabon arzikin kasa.Ya san masu dabbobi da suka cancanci bayar da zakka, ya san manoman da suka cancanci bayar da zakka, ya san nisabin dukiyar da za a fitar wa zakka. Ya kuma san su wa ya kamata a ba zakkar. Gidan Malam AbdulSalam Shi kuwa Malam AbdulSalami yana cikin dalibai Fulani wadanda suka yi amfani wajen taimakon Shehu Usman Danfodiyo a yake-yaken da ya yi tsakaninsa da Sarkin Gobir. Amma shi ba ya bullo ne kamar yadda su Malam Musa da Yamusa da AbdulKarimu suka bullo ba. Hawan Malam AbdulSalam kan gadon sarauta ya kasance raba-gardama ne, saboda lokacin da sarautar Zazzau ta koma gado, ’ya’yan gidan sarakunan guda uku suka fara cewa sai daga cikinsu ne za a sami wanda zai zama sarki a Zazzau, sai ‘ya’yan Sarkin Zazzau Yamusa suka fara irin wannan sarautar. Inda Hammada ya fara sarauta, daga nan sai kanensa Mamman Sani. Bayan Mamman Sani ya kau, sai Sidi AbdulKadir, babban dan Malam Musa da Shehu Usman Danfodiyo ya ba tuta, ya zama sarki bisa gado. Shi ma yana da ilimin addini, kuma ya cancanci rike sarautar. Sai dai bayan da Sidi AbdulKadir ya zama sarkin Zazzau, an yi ta samun kwamacala da rigingimu, tun da abin ya zama gado kowa ma dan gida yana ganin ya cancanci rike sarautar. Daga nan aka fara samun rashin yarda da juna, har aka kai kara Sakkwato, aka dakatar da Sarkin Zazzau Sidi AbdulKadir daga sarauta. Shi kuma ya ce, duk zargin da ake masa na sarautar ba shi kadai yake sarautar ba. Tare da shawarar dukkan ’yan majalisarsa ake yi, wato su masu son a ba su sarautar nan. Saboda haka, ba wanda ya cancanta a cikinsu, kamar yadda shi ma bai cancanta ba. Saboda haka, sai sarkin musulmi na wancan lokaci ya ga ya fi dacewa a dauko wani malami cikin daliban Shehu Danfodiyo a ba shi jagoranci, duk da ya manyanta a wannan lokaci. Kuma lokacin ya yi tsawo, Malam Musa ya yi shekaru goma sha, Yamusa ya yi shekaru goma sha, AbdulKarim ya yi shekaru goma sha, Hammada ya yi ’yan kwanaki, Mamman Sani ya yi shekaru, Sidi AbdulKadir ya yi wata takwas zuwa goma a gadon sarauta. To, idan ka tara wadannan shekaru, ka ga an dumfari shekaru arba’in. To, shi Malam AbdulSalam idan ka dora shekara arba’in a kan shekarunsa, ka ga ya manyanta. Amma sai sarkin musulmi na wancan lokaci ya ce a ba AbdulSalami sarautar Zazzau ya rike. Da haka ya zama raba-gardama. Ba a ba kowa ba daga cikin ‘ya’yan wadancan sarakuna. Wannan kuma shi ne dalilin zuwan gida na hudu a sarautar Zazzau kenan, wato don a sami natsuwa. Ta haka ne aka sami wadannan khalifofi guda hudu, kuma kowannensu an ba shi sarauta ne a matsayin kansa na masanin addinin musulunci, na mai biyayya da gaskata abin da jihadin Shehu Usman Danfodiyo ya kawo bisa koyarwa Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW). Tarihin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris Haihuwa da Tsatson Sarki Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo. Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu a cikin ‘ya’yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Danfodiyo ya yi a kasar Zazzau, kuma shi ne ya assasa gidan Katsinawa a sarautar Zazzau. Ina Sarki ya taso? Shi Mai martaba Sarki lokacin mahaifinsu yana Mai Unguwa a unguwar Iya a nan aka haife shi. Unguwar Iya wata unguwa ce da ke tsakanin unguwar Durumi da Kuyanbana. A nan ya girma, ya shekara akalla bakwai, inda har ya shiga makarantar allo, ya fara karatun addini. A nan dai unguwar Iya ya yi makarantar farko da Bature ya gina a cikin birnin Zariya, wadda ake kira ‘Town School one’, ita ce kuma makaranatar ‘Kofar Kuyanbana Local Government Education Primary School’. Yanzu ana ce mata ‘Waziri Lawal Local Government Education Primary School’, a nan ya fara karatu. Bayan ya gama sai ya tafi Alhudahuda College, lokacin ana kiran makarantar da sunan ‘Middle School’. Daga nan aka yi masa sauyi, ya koma makarantar koyar da malunta a Katsina lokacin ana kiran ta ‘Katsina Teachers’ College’.To, a nan ya koyi aikin koyarwa, wanda shi ne babbar sana’arsa ta farko da ya iya. Daga baya mai martaba ya sauya daga malamin makaranta ya shiga aikin mulki, wanda har ya je kasar Ostireliya (Australia). Yana cikin daliban farko da ofishin jakadancin Ostireliya suka dauki dawainiyarsu suka je suka yi karatu na koyon ilimin mulki a kasar ta Osireliya Wuraren da ya yi aiki Daga shekarar 1956 ya koyar a wurare daban-daban a cikin garin Zariya da kauyuka. Ya koyar a Zangon Aya, ya koyar a Paki, har ya yi hedimasta a Pakin. Ya kuma yi hedimasta a Hancin Kare a makarantar ‘Town School No.3’’. A shekarar 1962 ya koma aikin mulki, lokacin da ya koma karkashin hukumar ‘NA’ (Native Authority) ta Zariya a zamanin Sarkin Zazzau Aminu. Inda ya gwama aiki biyu, wato yana aiki a hukumar ‘NA’, kuma yana aiki a matsayin jami’in sadarwa na hukumar kula da kananan hukumomi da masarautu na jihar Arewa. Daga baya Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya ba shi mukamin Babban sarakatare na musamman na sarki. Daga nan ne sai aka nada shi sarauta, ya zama wakilin ofis, wato mai daukar nauyin duk abin da ya shafi aikin masarauta a karkashin ‘Native Authority’ a wannan lokacin. Ya rike wannan mukami na tsawon kamar shekara biyu zuwa uku, sai Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya nada shi hakimin birni da kewaye, mukamin da ya rike na tsawon shekara biyu zuwa uku, yana hakimi. Kuma Dan Madamin Zazzau. A shekarar 1975 likafarsa ta yi gaba, aka ba shi a sarautar Sarkin Zazzau. Sauyin da ya kawo a sarautar Zazzau cikin shekaru arba’in da biyar yana mulki Makusantan Sarkin suna ganin ba wani al’amari da ya shafi rayuwar Zage-zagi a birnin Zariya ko a masarautar Zazzau ne da ba a sami ci gaba ba. Ta fuskar ilimi, tun daga kananan makarantun firamare zuwa sakandire, zuwa na gaba da sakandire, zuwa jami’o’i, makarantun sojoji da sauransu da aka yi a masarautarsa, akalla ba za a rasa makarantu ashirin ba. Iyalin Sarki Allah Ya albarkaci mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris da iyali masu yawa. Yana da mata hudu, da ‘ya’ya maza da mata da yawansu ba zai gaza arba’in da biyu ko da biyar ba. Dabi’u da halayen Sarki Daya daga cikin hakiman masarautar Zazzau, Salanken Zazzau, Dokta Muhammadu Bello AbdulKadir, ya ce, babbar baiwar da Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, shi ne hakuri, yana da hakuri matuka. Ga shi kuma yana da kawaici, wanda a sakamakon haka ne ya kai kusan shekara ashirin yana sarauta, amma bai nada kowa daga cikin ‘ya’yansa sarauta ba, saboda kawaici. Sai da dattawa suka matsa masa, cewa idan bai nada ‘ya’yansa a sarauta ba, wa zai nada masa su. Hakurinsa da dauriya suka sa Zazzau ta zama kowa ya zo karbabbe ne, zai zo ya sami karbuwa wajen al’umma ya yi kasuwanci, ko ya nemi ilimi, ko ya yi kasuwanci ko sana’a da sauransu. Don haka, birnin Zariya ya zama wata matattarar kowacce kabila daga sassa daban-daban na Najeriya; ba kabilar da ba za ka samu ba a masarautar Zazzau. Masallacin Juma’ar masarautar Zazzau Zazzau wurin ne wanda tun kafin bullowar jihadin Shehu Usman Danfodiyo akwai rukuni-rukuni na Fulani a cikin gari da kauyuka wadanda aikinsu shi ne bayar da karatu na addinin musulunci. Kuma tun a wannan lokaci akwai masallacin juma’a a unguwar Juma cikin birnin Zariya, wanda aka gina a zamanin mulkin Isiyaku Jatau wanda Habe ne. Malaman unguwar Juman nan ko da aka yi jihadi sun ci gaba da limanci, kuma har yau su ke limanci, tun da su ma Fulani, kuma an same su da iliminsu. Ko da Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim ya gina masallaci a kofar fada, wancan masallacin na unguwar Juma ya rushe, an ci gaba da yin sallar Juma’a tare da limanci wadannan Fulani na unguwar Juma.Har yau zuri’arsu ke limanci. Abin da kasar Zazzau ta ginu a kai Ita Zazzau kasa ce da ma da ta ginu ne a kan abubuwa biyu, wato ilimin addinin musulunci, da harkar noma da kiwo. Kuma ko da Shehu Usman Danfodiyo ya yi jihadinsa abin da ya karfafa kenan. Wasan Kanawa da Zage-zagi Kamar yadda masana tarihi kan fada, mai karfi shi ke da iko. To, a wancan zamani, daular da ta yi karfi sai ta yunkura ta je ta mamaye wata. To, inda aka yi nasara, sai ka ji, amma inda aka gwabza, aka yi kare jini biri, ko kuma kowa ya tare kan iyakarsa, sai ka ji irin wadannan wasannin suna aukuwa. Haka ma inda aka sami nasarar cin su da yaki, sai ka ji irin wannan wasa yana faruwa. Misali za ka ga Katsinawa da Gobirawa ana irin wannan wasa. To, Kanawa da Zage-zagi ma akwai wannan wasa, cewa ita Sarauniya Amina ta kai hari Kano har Kofar Mata. Wannan kofar ai ana cewa nan ne aka dakatar da Sarauniya Amina, aka hana ta shiga cikin birnin Kano. A wancan zamani na mulkin Habe dai, an ce an wani sarkin Kano ya kawo farmaki har Zariya, amma aka tare shi a tsakanin yankin da a yanzu aka sani da karamar hukumar Kubau, wajen garin Kargi. Aka yi ba-ta-kashi. Saboda haka, ba mamaki ka ji ana wasa tsakanin Fulani da Barebari, tsakanin Katsinawa da Gobirawa, tsakanin har Yarabawa da Gobirawa. Kuma za ka ga irin wannan wasa yana dada dinke zumunci ne, ba yana batawa ba ne. Wannan dai duk a zamanin mulkin Habe ne aka yi ire-iren wadannan hare-hare. Amma yayin da aka sami shigowar daular Usumaniyya, sai kasashen suka zama daya, addinin musulunci ya hade su. Saboda haka, wata kasa ba ta kai wa wata kasa farmaki ba a cikin titocin da Shehu Usumanu Danfodiyo ya kafa. Sun zama abokan aiki, abokan hulda, kuma abokan shawarar juna. Girman kasar masarautar Zazzau a halin yanzu Sauyin da aka samu bisa sabon tsari na gwamnati, a yanzu a kowacce karamar hukuma ana da gundumomi ashirin da uku wadanda hakimai suke mulki a karkashin Mai Martaba Sarkin Zazzau. Kamar dai yadda gwamnatin jiha mai ci yanzu ta mayar da su. Amma gwamnatin baya ta nunnunka wadannan gundumomi, saboda ana shigo da harkar siyasa a cikin masarautun. Wata gwamnatin ta zo ta kara gundumomi, har sun kai tamanin da shida, ita kuma wannan gwamnati da ta zo sai ta rage su zuwa ashirin da uku. A zamanin mulkin soja an yanke wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar Kaduna, wadanda ke lardin Zazzau, wadanda suka hada da Kaciya da Zonkwa. Ta yankin kudu, sai aka bar lardin na Zazzau da kananan hukumomin Igabi da Kaduna ta kudu da Kaduna ta Arewa. Ta arewa akwai kananan hukumomin Giwa da Kudan, ta gabas kuwa akwai Makarfi da Ikara da Kubau. A yankin tsakiya kuwa akwai kananan hukumomin Soba da Sabon Gari da Zariya. A yanzu kananan hukumomi goma sha daya da gundumomi ashirin da uku kenan suke bin masarautar Zazzau a yau. A da kuwa tun daga karamar hukumar Kaciya, zuwa Chikun, har zuwa Kagarko, duk suna bin Zazzau ne. Amma daga baya aka sami wata gwamnati ta soja ta yanke wadannan kananan hukumomi, ta yi wasu sababbin masarautu, abin da ya sa aka sami masarautu kusan talatin da biyu. Saboda ra’ayin siyasa na son a ba kowacce kabila ‘yancinta, kar a ce an danne wani yanki a jihar. H za ta dauki

SHAWARORI TAKWAS GA MASU CIKI SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI

********************************* Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro. 1. Yana da kyau Macce me ciki ta siffantu da halaye na kwarai tare kuma da gujewa munanen halaye. 2. Saurarar karatun Alqur'ani na mintuna 30 kullum ga macce mai ciki kan taimaka wajen samun natsatstsen yaro. 3. Kauracewa duk wani magani da ba likita ne ya bada umurnin a sha ba, kan taimaka wajen samun lafiyayen jariri. 4. Macce mai ciki ta guji rashin yin bacci da wuri, samun bacci na awa 8 kan taimaka wa kwakwalwar jaririn da za'a haifa. 5. Macce mai ciki ta guji aikin wahala ko kuma wani abu wanda yayi kama da shi domin samun lafiyar jikinta da ta jariri. 6. Mai ciki ta rika kula da abinci kafin taci, ta tabbatar baku tsakuwa ko datti a cikin abinda zata sha. 7. Yawaita cin kayan lambu irinsu, Zogale, Cucumber, kankana, lettuce, alayyahu da sauransu. 8. A karshe yana da kyau mai ciki ta rika cin dabino hudu a rana biyu da safe biyu da dare koma fiye da su. Allah ya baku ikon saukewa, masu nema Allah ya basu, wayanda ke da Allah ya basu abin ciyarwa da ikon tarbiyantarwa.

Friday, April 24, 2020

Ramadan Tafsir 1441/2020* *01-Ramadan-1441* *24-04-2020*

Suratul Baqara

Tare Da *Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah).*


Domin Subscribe na YouTube channel namu Shiga ta Link din Kasa nan.

https://www.youtube.com/channel/UCmC9fMpvNGwheErpsSvVZyA

Domin Subscribe YouTube Channel Din sai ku Shiga ta Link din Kasa Nan.


Thursday, April 23, 2020

TAKAITACCEN TARIHIN YAREN LARABCI

TAKAITACCEN TARIHIN YAREN LARABCI

Babu shakka cewa yare yana daga cikin abubuwan da ke tsayar da Al’umma ya kuma bunkasa ta. Haka kuma kowace al’umma tana samun cigaba ne da bunkasa gwargwadon yadda yarenta ke samun cigaba.

Tarihi ya nuna cewa yaren Larabci yana daga cikin dadaddun yarukka, kuma shi ne mafi girmansu ga daraja, mafi kyawonsu ga tsari, kuma mafificinsu ga daukaka.

An yi sabani mai yawa dangane da wanda ya fara Magana da yaren Larabci. Wasu malamai na ganin cewa Ya’arib ne ya fara Magana da yaren, wasu kuma na ganin Annabi Isma’il (A.S) dan Annabi Ibrahim (A.S) ne ya fara Magana da yaren. A yayin da wasu ke ganin Annabi Adam (A.S) ne.

SHAFIN DA ZAKU SHIGA DOMIN KOYON KARATUN LARABCI DA TAJWID CIKIN SAUKI

SHAFIN DA ZAKU SHIGA DOMIN KOYON KARATUN LARABCI DA TAJWID CIKIN SAUKI

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki. Wanda ya baiwa yaren larabci muhimmancin gaske da kuma kulawa ta hakika. Wanda ke cewa: “hakika mun saukar da wannan Kur’ani da yaren larabci ko da za ku fahimta” Tsira da aminci su tabbata ga Annabinsa Balarabe, da alayensa da Sahabbansa da daukacin wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka: wannna Manhajar mun bude tane saboda mukoya karatun larabci cikin sauki, kafin muci gaba da darasi zamu ɗanyi bayani gameda matsayar Yaren larabci a addinin ta hanyar wayannan makalar :

1.Muhimmancin yaren Larabci
2.Fifikonsa akan sauran yarukka
3. Darasi (Huruful Hija'iyyah)

✓*FB-PAGE*
Shiga wannan link kuyi liking kuma ku following domin samun Darsuka akan hakan 👇👇👇👇👇👇👇�
Page-https://www.facebook.com/111306253888584?referrer=whatsapp

√*FB-GROUP*
Shiga wannan link kuyi Joining domin samun Darsuka akan hakan 👇👇👇👇👇👇👇�
https://www.facebook.com/groups/258528722183149/

√*WEBSITE*
Shiga wannan link kuyi Joining domin samun Darsuka  da kuma vedeo akan hakan 👇👇👇👇👇👇👇�
https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

√*WHATSAPP-GROUP*
Shiga wannan link kuyi Joining domin samun Darsuka  da kuma vedeo akan hakan 👇👇👇👇👇👇👇�
https://chat.whatsapp.com/JtcwBSYH3Vu9AIzRB0gGO8

√*YOUTUBE-CHANEL*
Shiga wannan link kuyi SUBSCRIBE domin samun  vedeo akan hakan 👇👇👇👇👇👇👇�
https://www.youtube.com/channel/UCmC9fMpvNGwheErpsSvVZyA

Saturday, April 18, 2020

MAKIRCIN SHAIDAN KAN AL'UMMAR ANNABI (S.A.Ws) PART 1

Ali dan Abi dalibi ya bada wani labari da yake nuna makircin shaidan da yake shiryawa a hankali har ya rugurguza mana imani.

Wannan labari akan wani mutum ne mai imani da yawan aiyukan addini, da yake zaune nesa da garinsu domin kuwa garin
mamaye yake da alfasha.

A cikin wannan garin akwai wasu mazaje su uku ‘yan uwan juna da suke kula da
kanwarsu wadda ita ma babu ruwanta.

Wata rana sai sukayi shawara su dauke ta su kaita can wajen gari inda wancan bawan-Allah yake zaune ko ta kubuta
daga munanan dabi’un da suka mamaye garin.

Daga farko wannan bawan-Allah ya ki don kuwa yasan hadarin kadaituwa da budurwar da ba matarsa ba.

Amma sai nan da nan shaidan ya rada masa “kaga, kai ne mutumin da yafi kowa tsoron Allah a wannan waje.

Idan kaki karbar wannan yarinya har ta koma wancan garin, lallai da sannu zata lalace.” Don haka sai ya karbe ta.

Sai ya kar beta.

Da farko yana bar mata abinci a bakin kofar dakin ya tafi abinsa, sai shaidan ya dawo ya kuma rada masa cewa” ta yaya kasan cewa hakika tana samun abincin?

Zai fi ka rinka dakatawa kadan kana
tabbatar da cewa tana samun abincin ba wata dabbar bace ke cinyewa.” Saboda haka sai ya rinka tsayawa.

Bayan wani dan lokaci sai shaidan ya rada masa “kaga ga yarinya mai hazaka a kulle a gidan nan kai kuma gaka da irin wannan tarin ilimi.

Ba zai fi ba ace ka fara koyar da ita in yaso zamanta anan baya zama hasara ba gaba daya?”.

To daga nan fa sai ya fara koyar da ita darussa.

Da farko yana barin wani abu a tsakaninsu saboda gudun fitina, amma sai shaidan ya bashi shawara a zuci cewa ya kamata ya rinka kallon idanunta yayin karatun domin ya tabbatar da cewa tana koyon, ba barci kawai take yi ba abinta.

Daga nan fa shaidan yasan cewa tarkon nasa ya danu. A hankali a hankali har sai da mutumin nan yayi wa yarinya ciki.

Bayan hakan ya auku sai ya dawo ya rada masa cewa ”to fa kai ne mafi imani a garin nan.

Yanzu ko mutuncin ka ya gama yawo (in
har aka gano wannan katobara).

Abin da yafi sai ka kashe ta ka binne, in yaso sai ka cewa ‘yan uwanta ‘rashin lafiya tayi, kuma duk da kokarin ka na neman magani sai da cutar ta kashe ta’.
Wannan tabbas zai fi wancan abin kunyar”. Haka kuwa ya yi.

Da ‘yan uwanta suka zo duba ta, mutumin har da hawaye, yana basu labarin yadda cuta ta kamata, da irin kokarin da yayi na magani har ta mutu.

Babu wata jayayya suka yarda, don kuwa kowa ya san shi mutumin kirki ne.

A ranar da daddare duk su ukun sukayi mafarki cewa wannan mutumin ne ya kashe musu ‘yar uwa ya binne a wani wuri.

Da safe sukayi ta mamaki da ta’ajabi ga yadda duk su ukun sukayi mafarki iri daya, sai suka yi shawara da su je wannan wuri da suka gani a mafarki su tone.

Ai kuwa sai ga gawar yarinya har da juna biyu. Suka kamo wannan mutum suka tafi da shi cikin gari gaban jama’a.

Mutane suna can suna shawarwarin yadda za’a yi da shi sai shaidan ya zo masa ya nemi mutumin da yayi masa sujjada inyaso shi kuma zai fitar da shi daga wannan bala’i.

Da mutumin ya ga ba mafita sai ya yarda kuma ya aikata hakan (wal iyazu billahi).

Daga nan shaidan ya bace ya rabu dashi ya barshi a cikin masifa da halin da na sani.

Haka kuma wato shaidan bazai taba hakura ba har sai ya ga mutum ya cika.

Ya 'Yan Uwa kunji Fa Makircin Shaidan akan mu....Ya Allah ka tsare mu da Shaidan Alfarmar Annabi (S.A.Ws)

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Friday, April 17, 2020

DALILIN FARUWAR LUWADI DA MADIGO A DUNIYA

Akwai Wani GARI wanda ake kira da SADUMU, shi Wannan garin ba wani babban gari bane, kuma Mutanen da ke cikin sa duk kafiraine, su wayannan kafirrai sun kasance basa son baki, basu son bako ya shiga garin nasu na SADUMU.

To ganin Haka da SHAIDAN (LA) Yayi sai Ya rikida ya cenza suffa ya zama tsoho, sai ya nufi garin yana shiga sai ya fara tara wadannan mutane Yace dasu "Idan har kuna son baki su daina zuwa Wannan gari naku, to ga yadda zakuyi.

Sai kawai ya basu kansa yace suyi LUWADI da shi, da wasunsu sukayi sai yace to ku dinga yiwa maza haka, idan kuma matane, sai macce ta dinga neman 'yar uwarta Macce.

Sannan yace to duk wanda yazo Wannan gari naku sai kuce masa sai kunyi wannan abin da shi, to daga nan kowa ma zai dinga qin zuwa garinnan naku.

To Wannan mummunan abu da shaidan (LA) ya nuna musu sai yayi tasiri a zuka tansu, dan haka duk mutumen da yaje wannan gari sai kawai su bishi sai sunyi wannan abu da shi.

Wannan tasa Allah (swt) ya aiko musu da Annabi Ludu (AS) domin yayi musu gargadi akan wannan mummunar al'ada da sukeyi ya kira su zuwa ga hanyar shiriya.

La'anar ALLAH ta kara tabbata ga SHAIDAN (LA)

( Mai neman karin bayani ya duba RAUD L-UNUF ko kuma sasul Anbiya'I)

ALLAH YA TSARENI YA TSAREKU YA TSARE DUKKAN MUSULMI DAGA WANNAN BALA'I WAYANDA KUMA KEYI ALLAH YA SHIRYESU SU DAINA..

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Thursday, April 16, 2020

KARO NA FARKO A TARIHIN NIGERIA...

Shugaban kasa Buhari ya amince an war-ware bashin dake tsakanin gwamnatin Nigeria da kamfanonin samar da wutar lantarki, da kamfanonin rarraba wutar da masu dakon iskar Gas da ake amfani dashi, an biya su bashin su Naira biliyan 190, sannan aka kara musu da Naira biliyan 30 su samar da wuta na watanni uku masu zuwa, wannan ne karon farkon da aka war-ware bashin, tun bayan sayar da kamfanin samar da wutar da gwamnatin PDP karkashin jagorancin Good Luck Jonathan tayi a 2013.
.
Kamfanonin sun karbi Naira biliyan 220, shugaban kasar ya umarci Ministan wuta Saleh Mamman da manajan NNPC su dauki nauyin kula da samar da iskar Gas din kai tsaye.
.
Shugabanni kamfanonin sun tabbatar da kudaden sun shiga hannun su, tare da alkawarin samar da wuta mafi karanci na awanni goma sha shida a kowane rana.
Yankuna da dama na Nigeria sun fara shaida hakan, yayin da wasu yankin suke jira tukun.
Wutar da aka samar daga jiya 15 ga wata, shine irin sa na farko a tarin Nigeria, wurin yawa da kuma karfi.

Thursday, April 9, 2020

FADAN KABILANCI A SOUTHERN TARABAN NIGERIA, GA MAFITA

Firgici da razana na tashin hankali na kokarin kewaye yankunan din (Donga, Takum And Wukari Roads), Al'amarin yana so yasake girmama, ya kamata musani Kowane Mutum yana da hakkoki masu yawa a kan Dan'uwansa Mutum

Musamman abokin zamantakewa na Kasa ko Gari, ko Makaranta, da duk wani waje da alaka ta kan hada juna kamar wajan aiki da Makamantansu.

Babban ma'auni na hakkin junanmu a kanmu shi ne wanda ya zo a cikin Hadisai na cewa: "Mu duba duk abin da muke so a yi mana sai mu yi wa mutane shi, mu kuma duba duk abin da muke ki a yi mana shi sai mu guji yi wa mutane shi".

Misali;
Kana kin a wulakanta ka ma'ana baka son a wulaqantaka, kuma kana son a girmamaka, to a nan sai ka ki wulakanta mutane kuma ka
girmama su.

Wannan hadisi da za a yi aiki da shi, da Duniya gaba daya ta zauna cikin aminci, da ta Juya ta sama tsaftsaf, da so ya game tsakanin mai kudi da talaka, da mai ilimi da maras ilimi, da miji da mata, da 'ya'ya da iyaye, da malami
da dalibi, da mai mulki da wanda ake mulka, da dukkanin nau'i na mutane gaba daya.

Amma yau abin haushi,

Mai kuddi na kyamar Zamantakewa da Talakka, haka Mai Mulki na fifita kan shi fiye da talakka, Mata da Miji ba'a zaman Lafiya, Uba ko Uwa na Fada da 'Ya'yansa, Malami na Hassadar Dalibinsa.

Addu'ar Mu anan itace,

Ya Allah ka sa mu cika da Imani kuma ka debe mana Hassadar Junan Mu, Ya Allah ka bamu Lafiya Da Zaman Lafiya.

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Friday, April 3, 2020

TAMBAYA MAI MA'ANA KU TSAYA KU KARANTA

Nakasance inayin azumin litinin da alhamis. Sai ake cewa wai yanzu sha'aban yashigo Ramadan ya gabato wai bai halalta incigaba ba saidai inanjeyishi har bayan idi sallah incigaba shin malam hakane?

AMSA
*****
Watan Sha’aban wata ne da Manzon Allah (SAWW) yake yawaita azumin tadawwa’i a cikinsa fiye da kowane wata a bayan Ramadan. Kamar yadda
Uwar Muminai A’isha (Allah Ya yarda da ita da mahaifinta) ta ruwaito cewa “Manzon Allah (SAWW) ya kasance yana
azumi har mu ce ba ya shan ruwa, kuma in yana sha ruwa har mukan ce ba ya azumi.

Amma ban ga Manzon Allah (SAWW) ya cika wata yana azumi ba, sai na watan Ramadan, kuma ban gan shi yana yawaita azumi ba kamar
yadda yake yi a watan Sha’aban.” (Buhari da Muslim).

Ibn Hajar ya ce,"Wannan Hadisi dalili ne kan falalar azumin Sha’aban." (Fathul Bari Mujalladi na 4 shafi na 253).

A cikin Lada’iful Ma’arif shafi na 247 Ibn Rajab ya ce “Amma azumin Manzon Allah (SAWW) a mafi shaharar Sunnah ya ksance yana azumtar Sha’aban fiye da kowane wata.” Yayin da San’ani ya ce "A cikinsa (Hadisin) akwai dalilin cewa ya kebance Sha’aban da yin azumi fiye da waninsa.” (Subulus
Salam, Mujalladi na 2 shafi na 342).

Kuma Sayyada A'isha (RA) ta ce “Watan da Manzon Alla (SAWW) ya fi so ya azumnta a cikin watanni shi ne Sha’aban, sannan ya sadar da shi da Ramadan.” Ahmad ya ruwaito shi a Musnad, kuma Abu Dawuda da Nisa’i sun ruwaito shi, kuma Hakim ya ce Sahihi ne a bisa sharadin Buhari da
Muslim, yayin da Albani ya inganta shi a cikin Abu Dawud. Hadisi na 2124.

Akwai ruwayoyi da dama kan falalar yawaita azumi a watan Sha’aban, kuma malamai sun karfafa haka tare da yin maganganu a kai. Ni dai ban san in da akace baabu kyau azumtar SHA'ABAN ba.

JAN HANKALIN DA ZANYI ANAN

• Jama'a Kowane bangare na rayuwa ana lura da abin da ake kira da harshen nasara “Specialization” don sauraro
da auna mai magana a bangaren, da kuma bashi kima ko rashin kima.

Likita da cuta.. lawyer bangaren
kare tuhuma da sauransu…
'Politician' abin da siyasa…
“Engineer”… da dai sauran
bangarori na rayuwa.
To shin bangaren da ya shafi addini ba shi da irin wannan
“Specialization” ne? sai ka ga…

kowa yana tsoma baki game da abin da ya shafi addini? Kowa yakan yi fatawa sannan ya dage bisa matsayinsa, ko da kuwa ba zai iya karanto maka aya guda ta kur’ani daidai ba? ballanta ma a ce ya san harshen da wannan shari’a ta sauka da shi?

Magabata masu dimbin sani na
shari'a har Alla-alla suke idan a ka samu mas’ala sabuwa ya zamanto wani daga cikinsu ya hutasshe amsarta, saboda girman hadarin gaggawa cikin bayar da fatawa.

A kan hukuncin shiga garin da
annoba ya fadawa, sai da Umar
(RA) ya tara kusan dukkan
Sahabbai da suke tare da shi, ko akwai wanda ya taba jin
hukuncinsa, duk suka ce ba su da masaniyar hakan, sai daga can karshe ne, aka samu AbdurRahman bn Auf (RA) ya yi bayanin hukuncin…

JAMA’A LALLAI MU YI HATTARA! MU RIKA MAGANAR DA MUKE DA MASANIYA BISA HUJJA DA DALILI!

ABIN DA BA MU SANI BA MU CE
ALLAH SHINE MASANI.

*WALLAHU A'ALAM*

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Thursday, April 2, 2020

YADUWAR ALFASHA NA KAWO CIWUKKA DA ANNOBA


Annabi (S.A.WS) yace “Alfasha bata taba bayyana a cikin wasu mutane har sukai ado da ita ba face annoba ta watsu acikinsu da ciwukkan da basu taba ganin irin suba.

Friday, March 27, 2020

FASSARAR FATAWA KAN CANJA WAJE DON SALLAR NAFILA*

Dayawa muna ganin masu sallah suna canja wajen sallah bayan idar da sallar farilla don yin sallar nafila, kuma mafi yawa su kan yi hakan, ba tare da ililmin hukuncinsa ba.*

*Shin canja waje tsakanin salloli*

*Bidi'a ne?*
*Ko Sunnah?*
*Ko abinso?*
*Ko kuma wajibi?*

*Kuzo muji hukuncin canja waje tsakanin salloli.*

*An tambayi Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah), shin akwai wani dalili kan canja muhalli don yin sallar nafila bayan farillah?*

*AMSA(JAWABI)?*

*1*  *Yazo cikin hadisin mu'awiyya (RA) yace:  Annabi(SAW) ya umurce mu da, kada mu hada sallah da sallah har sai mun yi magana, ko mun fita (daga cikin masallaci).*
*Muslim ya ruwaito.*

*Malamai ma'abota ilimi sun riki wannan kan zaifi kyau, a rarrabe farilla da nafila ko ta hanyar magana ko canja wajen sallah.*

*2*  *Daga Azraq ibn Qais yace: wani mutum yayi sallah tare da manzon Allah(SAW) sai ya mi ke, don yin safa'i, sai Sayyidina Umar ya kamo kafadarsa ya hana shi, yace zauna. Yace masa ahlil kitab su hallaka ne, saboda ba sa rarrabe sallolinsu.*

*Sai Annabi(SAW) ya mi ke ya ke cewa:* *Allah ya datar da kai Umar ibn kattab.* *Abu Dawud ya ruwaito, Albani ya inganta shi.*

*Don haka, yin istighfari sau uku (3) ya isar a matsayin magana.*
*Kayi kokarin isar da sakon, ga 'yan uwa musulmi.*

*Daga karshe:*

*Mai yiwuwa wannan hukunci zaifi amfani wajen mata saboda sun fi yin sallah a gida su kadai.Tana sallar farilla saita mi ke, ta kawo nafila, babu magana a tsakaninsu.*
*Don haka a yi kokari, a isar da wannan sako ga wasu.*

*Yada ilimi yana daga cikin manyan ayyukan alkhairi.*

FASSARAR FATAWA KAN CANJA WAJE DON SALLAR NAFILA*

Dayawa muna ganin masu sallah suna canja wajen sallah bayan idar da sallar farilla don yin sallar nafila, kuma mafi yawa su kan yi hakan, ba tare da ililmin hukuncinsa ba.*

*Shin canja waje tsakanin salloli*

*Bidi'a ne?*
*Ko Sunnah?*
*Ko abinso?*
*Ko kuma wajibi?*

*Kuzo muji hukuncin canja waje tsakanin salloli.*

*An tambayi Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah), shin akwai wani dalili kan canja muhalli don yin sallar nafila bayan farillah?*

*AMSA(JAWABI)?*

*1*  *Yazo cikin hadisin mu'awiyya (RA) yace:  Annabi(SAW) ya umurce mu da, kada mu hada sallah da sallah har sai mun yi magana, ko mun fita (daga cikin masallaci).*
*Muslim ya ruwaito.*

*Malamai ma'abota ilimi sun riki wannan kan zaifi kyau, a rarrabe farilla da nafila ko ta hanyar magana ko canja wajen sallah.*

*2*  *Daga Azraq ibn Qais yace: wani mutum yayi sallah tare da manzon Allah(SAW) sai ya mi ke, don yin safa'i, sai Sayyidina Umar ya kamo kafadarsa ya hana shi, yace zauna. Yace masa ahlil kitab su hallaka ne, saboda ba sa rarrabe sallolinsu.*

*Sai Annabi(SAW) ya mi ke ya ke cewa:* *Allah ya datar da kai Umar ibn kattab.* *Abu Dawud ya ruwaito, Albani ya inganta shi.*

*Don haka, yin istighfari sau uku (3) ya isar a matsayin magana.*
*Kayi kokarin isar da sakon, ga 'yan uwa musulmi.*

*Daga karshe:*

*Mai yiwuwa wannan hukunci zaifi amfani wajen mata saboda sun fi yin sallah a gida su kadai.Tana sallar farilla saita mi ke, ta kawo nafila, babu magana a tsakaninsu.*
*Don haka a yi kokari, a isar da wannan sako ga wasu.*

*Yada ilimi yana daga cikin manyan ayyukan alkhairi.*
*FASSARAR FATAWA KAN CANJA WAJE DON SALLAR NAFILA*

*Dayawa muna ganin masu sallah suna canja wajen sallah bayan idar da sallar farilla don yin sallar nafila, kuma mafi yawa su kan yi hakan, ba tare da ililmin hukuncinsa ba.*

*Shin canja waje tsakanin salloli*

*Bidi'a ne?*
*Ko Sunnah?*
*Ko abinso?*
*Ko kuma wajibi?*

*Kuzo muji hukuncin canja waje tsakanin salloli.*

*An tambayi Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah), shin akwai wani dalili kan canja muhalli don yin sallar nafila bayan farillah?*

*AMSA(JAWABI)?*

*1*  *Yazo cikin hadisin mu'awiyya (RA) yace:  Annabi(SAW) ya umurce mu da, kada mu hada sallah da sallah har sai mun yi magana, ko mun fita (daga cikin masallaci).*
*Muslim ya ruwaito.*

*Malamai ma'abota ilimi sun riki wannan kan zaifi kyau, a rarrabe farilla da nafila ko ta hanyar magana ko canja wajen sallah.*

*2*  *Daga Azraq ibn Qais yace: wani mutum yayi sallah tare da manzon Allah(SAW) sai ya mi ke, don yin safa'i, sai Sayyidina Umar ya kamo kafadarsa ya hana shi, yace zauna. Yace masa ahlil kitab su hallaka ne, saboda ba sa rarrabe sallolinsu.*

*Sai Annabi(SAW) ya mi ke ya ke cewa:* *Allah ya datar da kai Umar ibn kattab.* *Abu Dawud ya ruwaito, Albani ya inganta shi.*

*Don haka, yin istighfari sau uku (3) ya isar a matsayin magana.*
*Kayi kokarin isar da sakon, ga 'yan uwa musulmi.*

*Daga karshe:*

*Mai yiwuwa wannan hukunci zaifi amfani wajen mata saboda sun fi yin sallah a gida su kadai.Tana sallar farilla saita mi ke, ta kawo nafila, babu magana a tsakaninsu.*
*Don haka a yi kokari, a isar da wannan sako ga wasu.*

*Yada ilimi yana daga cikin manyan ayyukan alkhairi.*

FASSARAR FATAWA KAN CANJA WAJE DON SALLAR NAFILA*

Dayawa muna ganin masu sallah suna canja wajen sallah bayan idar da sallar farilla don yin sallar nafila, kuma mafi yawa su kan yi hakan, ba tare da ililmin hukuncinsa ba.*

*Shin canja waje tsakanin salloli*

*Bidi'a ne?*
*Ko Sunnah?*
*Ko abinso?*
*Ko kuma wajibi?*

*Kuzo muji hukuncin canja waje tsakanin salloli.*

*An tambayi Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah), shin akwai wani dalili kan canja muhalli don yin sallar nafila bayan farillah?*

*AMSA(JAWABI)?*

*1*  *Yazo cikin hadisin mu'awiyya (RA) yace:  Annabi(SAW) ya umurce mu da, kada mu hada sallah da sallah har sai mun yi magana, ko mun fita (daga cikin masallaci).*
*Muslim ya ruwaito.*

*Malamai ma'abota ilimi sun riki wannan kan zaifi kyau, a rarrabe farilla da nafila ko ta hanyar magana ko canja wajen sallah.*

*2*  *Daga Azraq ibn Qais yace: wani mutum yayi sallah tare da manzon Allah(SAW) sai ya mi ke, don yin safa'i, sai Sayyidina Umar ya kamo kafadarsa ya hana shi, yace zauna. Yace masa ahlil kitab su hallaka ne, saboda ba sa rarrabe sallolinsu.*

*Sai Annabi(SAW) ya mi ke ya ke cewa:* *Allah ya datar da kai Umar ibn kattab.* *Abu Dawud ya ruwaito, Albani ya inganta shi.*

*Don haka, yin istighfari sau uku (3) ya isar a matsayin magana.*
*Kayi kokarin isar da sakon, ga 'yan uwa musulmi.*

*Daga karshe:*

*Mai yiwuwa wannan hukunci zaifi amfani wajen mata saboda sun fi yin sallah a gida su kadai.Tana sallar farilla saita mi ke, ta kawo nafila, babu magana a tsakaninsu.*
*Don haka a yi kokari, a isar da wannan sako ga wasu.*

*Yada ilimi yana daga cikin manyan ayyukan alkhairi.*
*FASSARAR FATAWA KAN CANJA WAJE DON SALLAR NAFILA*

*Dayawa muna ganin masu sallah suna canja wajen sallah bayan idar da sallar farilla don yin sallar nafila, kuma mafi yawa su kan yi hakan, ba tare da ililmin hukuncinsa ba.*

*Shin canja waje tsakanin salloli*

*Bidi'a ne?*
*Ko Sunnah?*
*Ko abinso?*
*Ko kuma wajibi?*

*Kuzo muji hukuncin canja waje tsakanin salloli.*

*An tambayi Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah), shin akwai wani dalili kan canja muhalli don yin sallar nafila bayan farillah?*

*AMSA(JAWABI)?*

*1*  *Yazo cikin hadisin mu'awiyya (RA) yace:  Annabi(SAW) ya umurce mu da, kada mu hada sallah da sallah har sai mun yi magana, ko mun fita (daga cikin masallaci).*
*Muslim ya ruwaito.*

*Malamai ma'abota ilimi sun riki wannan kan zaifi kyau, a rarrabe farilla da nafila ko ta hanyar magana ko canja wajen sallah.*

*2*  *Daga Azraq ibn Qais yace: wani mutum yayi sallah tare da manzon Allah(SAW) sai ya mi ke, don yin safa'i, sai Sayyidina Umar ya kamo kafadarsa ya hana shi, yace zauna. Yace masa ahlil kitab su hallaka ne, saboda ba sa rarrabe sallolinsu.*

*Sai Annabi(SAW) ya mi ke ya ke cewa:* *Allah ya datar da kai Umar ibn kattab.* *Abu Dawud ya ruwaito, Albani ya inganta shi.*

*Don haka, yin istighfari sau uku (3) ya isar a matsayin magana.*
*Kayi kokarin isar da sakon, ga 'yan uwa musulmi.*

*Daga karshe:*

*Mai yiwuwa wannan hukunci zaifi amfani wajen mata saboda sun fi yin sallah a gida su kadai.Tana sallar farilla saita mi ke, ta kawo nafila, babu magana a tsakaninsu.*
*Don haka a yi kokari, a isar da wannan sako ga wasu.*

*Yada ilimi yana daga cikin manyan ayyukan alkhairi.*

Sunday, March 22, 2020

HANYA MAFI SAUKI DA ZAKA YI GWAJIN COVID-19 DA KUMA HANYA DA ZAKA KASHE SHI IDAN YA SHIGE KA A LOKACIN

Sabuwar cutar Coronavirus NCP * baya nuna alamun kamuwa da cutar har na tsawon kwanaki, * wanda ba za'a san shi ba idan mutum ya kamu.
Amma idan har kabar lokacin da yafara nuna alamun Zazzaɓi ko tari sannan ka garzaya zuwa asibiti toh huhunka yariga da ya kamu da ƙwayar fibrosis da kashi hamsin cikin ɗari kuma ka makara.

Masana na Taiwanese suna ba da shawarar yin sauƙaƙenƙen gwadi wanda za mu iya yi da kan mu kowace safiya: Ka ja numfashinka ba tare da ka sauke ba na sama da dakika 10.
 Idan ka samu nasarar kammala shi ba tare da tari ba, ba tare da wata damuwa ba, da azanci, da dai sauransu, wannan yana nuna cewa babu zazzabin kwayar fibrosis a cikin huhun ka, yana nuna da gaske babu kamuwa da cutan

A irin waɗannan lokuta masu wuya, yin wannan gwadi kowace safiya a cikin tsabtataccen iska!
Waɗannan kyawawan shawarwari ne masu ƙamari daga likitocin ƙasar Sin (China) da suka lura da luggogin COVID-19. Kowa ya kamata ya tabbata cewa bakinsa da makogwaron sa na da laushi, basu bushe ba, ka dinga shan ruwa akalla kowani bayan minti 15.

Saboda Ko da kwayar cutar ta shiga bakinka ... ruwa zai dauke shi ta cikin esophagus ya biyo dashi cikin ciki. Matukar yashiga cikin Ka... acid da yake cikin Ka  zai kashe duk ƙwayoyin cutan. Idan ba kwa shan isasshen ruwa a kai a kai ... ƙwayar na iya shiga ta hanyoyin iska yakuma shiga cikin huhunka ya haifar maka da COVID-19.

Ya Allah ka kare mu daga kamuwa da wannan cutar kuma ka yafe mana kura-kuran mu, Kasa Aljannar Firdausi itace makomarmu baki daya. Ãmīn ya Qādiyal Hājah

~ https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

TAMBAYOYIN BIYAR DA KOWANNE MUSULMI YA KAMATA YA SAN AMSAR SU.

1. WANENE YA HALICCE NI?
Wanda ko  Wanne Musulmi Ya san Wannan Tambayar Sai dai Na kawota dan Itace ta zama Wajibi ta fara shigowa a Jeren Wayannan Tambayoyin, To tunda kowanne Musulmi Ya san Wanda Ya halicce shi Sai tambaya ta Biyu.

2. DON ME YA HALICCE NI?
Allah (swt) da kansa Ya Bamu Amsar wannan Tambaya Sai dai Wasummu basa ma lura da Amsar ballantana Suyi abinda Allah (swt) Yace.

Allah (swt) Yana Cewa "BAN HALICCI MUTUM DA ALJANI BA SAI DON SU BAUTA MIN".

3. TO YAYA NE AKEYIN BAUTAR?
Kowannen Mu ya kamata Yasan Cewa Bauta dole bata Yuwa Sai da Ilmi kuma Dole ne Sai Da Yin tambaya akan abinda Ya shafi Ilmi Shi kan shi.

Sharuddan Yin Bauta
- Ka samu a cikin Al'qur'ani Ance Ayi.
- Ka dauko Yanda Magabata na Kwarai Suka yi bautar, Ma'ana Yanda Suka Dauko Yanda Manzon Allah (saww) Yake yin bautar.
- kayi Badan Wani ko wata Ya Yaba maka ba.

4. A INA NAKE YANZU?
Ma'ana A ina nake Yanzu? Shin Ina nan In da Allah ke son Ya Ganni? Ko kuma Na saki Hanya?

5. ZUWA INA MAKOMA TA ZATA KASANCE?
Bayan Duk Wayannan Tambayoyin Guda Hudu to tambaya ta Biyar Duka ta fisu Tsoro da Rudani, Amsar tambayar Makomata Wutane ko kuma Aljanna.

Lalle Wayannan Tambayoyin Abin Dubawa Ne Ga Kowanne Musulmi Mai Hankali.

Wallahi Wa sun Mu da Yawa Sun Yarda Da Allah ne Ya Halicce Su Amma basu san Yarda Shi Yake da Ikon Yi musu Komai ba, Basa Neman Taimakonsa Sai Na Bokaye da 'Yan bori.

Wallahi Da Yawan Wasummu Basu Ma Iya Karanta Fatiha Dai dai ba, Amma Idan Zaka Lissafa Wakokin Kafirrai Zakaji Ya Fi hardace Su Fiye da Surorin Al'Qur'ani koma Sunayen Allah.

Wallahi Wasummu Basa Tuna Mutuwa Ko kadan, Kullum Tunanin Su Ya Za'ayi na Samu Kuddi, ko wani abu makamancin haka, Amma basa Tunanin Shin Ana Amsar Ibada ta, Shin Zan Iya Mutuwa Yau, Shin Meye Zunubbai na A gurin Allah (swt).

Wallahi Da Yawa Daga Cikin Mu Har Sun Manta Da Suyi Istigfari Sai Dai Kullum Suna kan Whatsapp, Facebook, Twettr, Istagram, da Sauransu.

Wallahi Mu komawa Allah (swt) ko zamu Samu Rabauta.

Ya Kamata Kana Gama Karatun Wannan Post Din Ka Tashi Kayi Istigfari, Kace " ASTAGFIRULLAHI" ko sau 100, Kada Ka bari Har Ajuma Dan Zaka Iya Mutuwa Yanzu.

ALLAH YA SAMU DACE DUNIYA DA LAHIRA, KUMA ALLAH YA TSARE JIKKUNAN MU DA WUTAR JAHANNAMA.

ahmadmusainc.blogspot.com

Saturday, March 21, 2020

JINJINA GA IYAYE *****************

Idan mutum ya yi NAZARIN wahalar da IYAYE suka sha wajen tashinsa, da daure ma kurciyarsa har zuwa sadda zai yi hankali shi kadai ya isa ya nuna masa
girman hakkin IYAYE a kan sa.

To, ina ga kuma in mun koma ga alhakin uwa na daukar ciki wata tara tsakanin lafiya da ciwo, laulayi da haraswa, da kyamar abinci da raunin jiki da nauyin ciki har zuwa ga nakuda wadda wata 'yar karamar lahira ce mata suke zuwa a mafi
yawan lokuta!

Annabi (saww) Ya nuna mana Muhimmancin Iyaye a hadisai da dama musamman ita Uwa.

YA DAN UWA/'YAR UWA musulmi/ma

Mu gode wa Allah da ya sa mu cikin inwar addinin musulunci da karantarwarsa.

Daga cikin abinda TURAWA ke fama da shi a yau mai tada hankali shine;

Akwai tanadin da kowane mutum yake yiwa kansa na kuddi don tsufansa.

Dole ne mutum ya tara wasu makudan kudade da zasu amfane shi idan ya tsufa. Don me?

Don babu wanda zai kula da shi idan ya tsufa. In ba haka ba kuwa lalle ne zai kare rayuwarsa a gidan nakasassu da
gajiyayyu wanda gwamnati ta tanada wanda kuma ba shi da banbanci da zaman fursuna a kurkuku.

A lokacin su kuma 'ya'yansa maza da mata na can suna soyayya da abokai da kawayensu ba wanda ya damu da shi.

A kasashen turawa akwai kowace doka har da ta hakkin karnuka amma babu wata doka akan hakkin IYAYE. Don me? Wai don kada a takura wa 'ya'ya! Za
a shiga cikin 'yancinsu!!

Musulunci ya banbantamu da su ta in da ya nuna mana cewa iyaye suna da hakki sosai ga 'ya'yan su koda kuwa bayan sun MUTUNE.

Wata likita ta bada labarin wani mutum mai biyayya mai ban mamaki.

Tace wata Tsohuwa ce wawiya da ba a haife ta ma da hankali ba.

'Dan ta ya zo da ita yana mai tsananin kula da ita. Ba ya son komi ya same ta. Kullum idonsa na kan wannan mahaifiyar tashi.

Saboda mamakin irin yanda yake kula da mahaifiyar tasa, yasa wannan likita ta tambaye shi, kuma ya sanar da ita cewa tun lokacin da aka haifeta (ita mahaifiyar tasa) tana fama  da tabuwar hankali kuma bata san abinda take yi ba.

An aurar da ita ga mahaifinsa bayan ta samu cikinsa sai mahaifin ya kasa hakura da zama da ita, ya sauwake mata ta koma hannun iyayenta. wannan abin ba karamin tashin hankali ya saka wannan matar ba.

Akan haka yasa ta kara shiga tsananin tashin hankali.

Tashin hankalin da wannan matar ta shiga shine, yasa ya bar komai baya komai sai kula da ita mahaifiyarsa.

Ku duba fa shi  wannan ya kula da uwar da cikinsa kawai ta dauka bata san wahalarsa kowace iri ba yana ta tarainiya da ita haka.. To, mu da iyayenmu suka sha kowace irin wahala a kanmu ya zamu yi kenan?!

A cikin tarihin magabata akwai labarai masu kayatarwa game da bin wannan umurni na ubangiji na kwautaatawa iyaye.

1. Mis'ar bin Kidam (rta) ya taba kawo ma
mahaifiyarsa ruwa bayan ta nemi haka amma ko da ya zo ta yi bacci. Sai ya tsaya har gari ya waye bai tashe ta ba kuma bai tafiyarsa ba.

2. Muhammad bin Al-Munkadir ya ce, na kwana ina murza kafar mahaifiyata don ta ji dadin bacci, kanena kuma ya kwana yana sallah. Bana tunanin a bamu lada daya sai dai ni na fishi samun ladar.

3. Sayyidina Abu Huraira (rta) ya ga wani mutum yana tafiya bayan wani dattijo. Sai ya tambaye shi, wane ne? Ya ce, mahaifina. Sai ya ce: kada ka kira shi
da sunansa, kada ka zauna kafin sa, kuma kada kayi tafiya a gabansa.

Bayan haka ya kai dan uwa musulmi! Ka sani ba wani laifi a wurin Allah wanda yake gaggauta kama mai yinsa, ya debe masa albarka, ya barkata masa rayuwa tun a nan duniya kamar cuta wa iyaye.

Sai ka ga mutum ya damu da matarsa, ya kula da 'ya'yansa amma bai ko san halin da mahaifiyarsa take ciki ba.

Ankarbo daga Abu kahil, cewa Manzon Allah (saww) yace; ku cewa wanda yayi biyayya ga mahaifansa, a halin suna raye ko suna mace, to lalle Allah (SWT) ya yarda da shi a ranar Qiyama, sai muka ce yaya mutum zaiyi biyayya ga mahaifansa Alhali suna mace Ya Rasulillahi? Sai yace; ya nema musu gafara, kar ya zagi mahaifan wani balle a zagi na sa mahaifan.

YA ALLAH KA GAFARTAWA IYAYEN MU, KA YAFE MUSU KURAKURANSU...(AMEEN)

NI DAI KU SHAIDA NA TURO WANNAN BADAN KOMAI BA SAI DON TUNA WA DA MAHAIFANA DA KUMA ROKA MUSU GAFARA.

KACE AMEEN KUMA KA TURA GA 'YAN UWANKA DOMIN ROKAWA IYAYENKA GAFARA.

TAMBAYA AKAN GASHI A CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA.*

✍ Rubutawa: *Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah).*

TUN JIYA AKE BUGO MINI WAYA AKAN WAI WANI YA YI MAFARKI YA GA ANNABI MUHAMMAD SAW, WAI YACE MASA A BUƊE  ALKURNANI CIKIN SURATUL BAƘARA, ZA A GA GASHI SAI A JIƘA A SHA YANA MAGANIN CORONA VIRUS.
MANZON ALLAH SAW YACE :DUK WANDA YA YI MINI ƘARYA YA TANADI MASAUKINSA A CIKIN WUTA. BUKHARI DA MUSLIM

 WANNAN MAFARKI DA WANNAN MAGANA BA GASKIYA BACE SABODA DALILI GUDA GOMA:

-NA ƊAYA, MAFARKI DA ANNABI SAW GASKIYA NE, AMMA SAI KA GAN SHI YADDA YAKE A KAMANNINSA DA MAGANGANU SA DA HALAYANSA, WANNAN KUWA BAI YI KAMA DA YADDA ANNABI SAW YAKE ISAR DA SAKO BA, GASHI DA ALKUR'ANI.

- NA BIYU, ME YA HAƊA DA ALKUR'ANI MAI GIRMA  DA KUMA GASHI?.

- NA UKU, GASHIN NA WAYE, MUTUM KO DABBA? KUMA NA INA NE GASHIN?.

- NA HUƊU, DUK WANI GASHI IDAN BA NA ANNABI SAW BA, TO ZAI ZAMA KO ƘAZANTA KO NAJASA.

- NA BIYAR,  ME YASA BA'A YI AMFANI DA ALKUR'ANIN BA SAI GASHIN KAWAI?.

- NA SHIDA, ME YASA SAI A AFRIKA KAWAI AKE SAMUN WAƊANNAN SHIRMAN.

- NA BAKWAI, WAYE YA BUƊE ALKUR'ANIN KUMA YAGA GASHIN?.

- NA TAKWAS, INA WANDA YAGA MAFARKIN YAKE?.

- NA TARA, AN GWADA AKAN MAI CIWAN YA WARKE? KO YA WARKE BA ZAI ZAMA GASKIYA BA, DOMIN ZAI IYA ZAMA JARRABAWA.

- NA GOMA, ANYA BA SHEƊANU BANE DA BOKAYE, DA MASU SIHRI SUKE SON HALAKA MUTANE? DOMIN AYI WASA DA ALKUR'ANI MAI GIRMA DOMIN WATA MUSIFAR TA ƘARA SAUKA, KAMAR YADDA YA FARU A LOKACIN IBOLA DA GISHIRI?.

ALLAH YA TSARE MANA IMANI DA AKIDA YA YAYE MANA DUKKAN BALA'I.

Friday, March 20, 2020

SUBHANALLAH

Tun bayan da Mushirakan Larabawa suka kori Manzon Allah (SAW) daga garin Makkah yayi hijira tare da sahabbansa zuwa Madinah, daga baya Manzon Allah Ya sake dawo wa yaci Makkah da yaki (akayi Fathu Makkah), Musulunci ya kafu, shekaru sama da dubu daya da dari hudu da suka gabata ba'ayi wani lokaci da aka hana musulmai sallah a masallaci ba a fadin Kasar Saudiyyah har da Makkah da Madinah ba sai wannan karon

Jiya mahukuntan Saudiyyah sun bada umarnin rufe Masallacin Manzon Allah (SAW) dake birnin Madina da kuma Masallacin Harami dake birnin Makkah saboda masifar cutar annoba da ta addabi duniya (Coronavirus)

Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo yace:
Mu sani cewa lalle babu wata musifa da ta wuce a jarrabeka a cikin addininka, yau gashi ana ta rufe Masallatai, ana hana fitowa sallar Jam'i, har sallar juma'a da yawa daga kasashe sun bayarda sanarwa a dakata sakamakon wannan cuta, Lalle wannan abun tsoro ne! Kamar Allah Yayi fushi da mutane ne, yace: Ku fita ku bar min dakuna na (Masallatai) tunda barnaarku a bayan kasa tayi yawa.

Babbar musiba ce a rabaka da dakin Allah, a ce babu Umarah, babu Dawafi, babu sallar jam'i, lalle babu musibar da tafi musiba a cikin addini, tabbas Allah Yana fushi da mutane, Ya zama wajibi mu koma mu tuba ga Allah.

Allah Ka yafe mana, Ka kawo mana saukin wannan masifa Amin

Saturday, March 14, 2020

Abubuwa Guda Bakwai Wanda Allah Ya Jarabci Al'ummar Duniya Da A Su Cikin Wannan Shekarar Ta 2020

01. Dubannin mutame sun kamu da cutar KoronaVirus a fadin duniya.

02. A shekaran jiya anyi guguwa mai karfi a kasashen Misra da Sham.

03. Miliyoyin fari da dangwaye sun cika kasar Yamen da wasu kasashe a gabashin Afrika.

04. A shekaran jiya an samu wani bugun iska mai karfi wanda ya rinka tunbuke bishiyoyi a kasashen Palasdin da Urdun da Syria.

05. Birori sun cika tituna kasar Thailand saboda yunwa ya koro su, suna neman abinci.

06. A satin da ya gabata jemagu sun cika kasar Australia

07. Abu mafi muni shine, a wannan shekarar aka tsare mutane daga dawafi a daki mai alfarma saboda cutar KoronaVirus.

Ya Allah ka gafarta muna ka jikan mu amin.

Fityanul Islam Of Nigeria
14/02/2020

Tuesday, March 10, 2020

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...12..

Lokacin da wannan jakada ya zo wa Annabi sulaiman(A.S) mabiyansa suna tare da shi da hadiya a tare dasu, sai Annabi sulaiman(A.S)Yace shin zaku 'kare ni da dukiya, bayan abin da Allah(S.W.T)ya bani ? Na Annabta da mulki shine mafifici daga abinda ya baku na duniya, kai bari! Ku dai kuna farin ciki ne da kyautarku saboda al'faharin ku da tarkace-tarkacenku,  ka koma da abinda ka zo da shi na hadiya, lallai zamu zo musu da runduna wadda ba su da iko da ita, kuma lallai zamu fisshe su daga garinsu birnin saba'i, kuma zamu fisshe su in basu zo min suna masu mi'ka wuyaba.
       Lokacin da jakada ya koma musu da wannan kyautar sai ta sanya gadonta cikin 'kofa bakwai7 daga cikin katangar gidanta, gidan nata kuma yana cikin gidaje bakwai7, ta kulle 'kofofin ta sanya masu tsaro, sannan kuma tayi shirin tawowa gurin Annabi sulaiman(A.S)Dan taga abinda zai umarceta da shi, sai ta maraito acikin makwayo dubu goma sha biyu, ko wamne makwayo dubbai suna tare da shi, har izuwa kusa da Annabi sulaiman(A.S)da mil uku (3-m) , sai Annabi sulaiman(A.S)ya yi hashashe da ita  , sai yace yaku wad'annan jama'a wanene zai zo min da gadonta tun kafin su zo min suna masu mi'ka wuya, sai wani gwarzo daga Aljanu, wato mai tsananin 'karfi yce ni zan zo maka da shi kafin ka ta shi daga mazaunin shari'arka, (wato daga safiya zuwa rabin yini)ha'ki'ka ni mai 'karfi ne kuma amintacce ne ni ga abinda yake cikin gadon na jauharori da makamantansu, sai Annabi sulaiman(A.S)Yace ina son mafi sauri daga haka,  sai wani wanda yasan ilimin littafi ya ce ni zan zo maka da shi kafin idonka ya koma gareka idan kayi duba da shi izuwa  wani abu, sai ya subi sama, yana dawo da idon 'kasa sai ya ganshi a gabansa, lokacin da Annabi sulaiman(A.S)ya ga wannan gadon a gabansa sai yace wannan falalar Ubangiji ce don ya jarrabe ni zan gode masa ko zan butulce masa, wanda ya godewa ni'imar Allah, to tabbas ya gode dan kansa, domin sakamakon godiyar nan nasa ne, To tabbas Ubangiji mawadaci ne ga buran godiyar sa,  kuma mai karamane da Baiwa a bisa wanda ta butulce masa.
        Sai Annabi sulaiman(A.S)yace ku jirkita gadonta, zuwa halin da bazata ganeshi ba,  mu gani zata ganeshin? Domin jarraba hankalinta, lokacin da ta zo sai akace, shin kamar haka gadonki yake?  Sai tace kai kace shine kamar yadda suka shigar mata da kwatance, sai Annabi sulaiman(A.S)ya lura da cewa lallai tana da sani da basira, an bamu ilmi tun ga banta, mun kasance masu mika wuya, ya fad'i hakane don nuna godiya ga Allah, abinda kuma take bautawa ba Allah ba,ya tare ta  ga Bautar Allah(S.W.T) ha'ki'ka ita ta kasance daga mutane kafirai.
     Lokacin da ta tsaya gurin Annabi sulaiman(A.S)Sai aka ce da ita wannan rufi , rufine na gilas fari ruwan dad'i yake kwarara a 'kar'kashisa, akwai kifi da kwado da dabbobin ruwa, Annabi sulaiman(A.S)ya zuba su, lokacin da tagani sai ta zaci kunzomeman ruwa ne, sai ta yaye 'kafafuwanta guda biyu domin tsallaka ruwan, Annabi sulaiman(A.S)yana kan gadonsa gana kallonta, sai yaga 'kafafuwanta kyawawa, sai yace mata wannan rufi ne mai santsi na kaskon 'karau, sai ta ce Ubangiji ha'ki'ka na zalinci kaina da bautar waninka na mika wuya tare da Annabi sulaiman ga Allah Ubangijin Talikai.
      Sai ta nemi ya aure ta sai ya 'ki saboda gashin 'kafarta, sai shaid'anu sukayi, masa nur wato farar 'kasa, sai ya kawar da gashin, sai ya aure ta ya tabbatar da ita akan mulkinta, ya kasance yana ziyartarta sau d'aya a wata yana zama a wajanta kwana uku.
     Mulkinta ya 'kare da 'karewar mulkin Annabi sulaiman(A.S), An ruwaito cewa An khalifantar da shi gana d'an shekara shia uku(13), ya rasu kuma yana d'an shekara hamsin da uku(53).

WAFATIN ANNABI SULAIMAN(A.S)..

.ZANI GABA INSHA ALLAHU..

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...1O..

LABARIN BILKISU DA ALHUDA-HUDA.

     Malamai sukace, acikin labarun , Lokacin da  Annabi sulaiman(A.S)ya gama ginin Baitul Mu'kaddis, sai yayi nufin fita zuwa harami, sai ya tattara tawagarsa ta mutane da Aljanu da tsuntsaye da 'kwari, sun kai yawan Bataliya d'ari , sai iska ta d'aukesu zuwa harami, sai ya sauka anan yayi kwanaki iya yadda Allah yaso, har yayi aikin HAJJI , da sauran wasu ibadu, kuma ya gayawa mutanansa labarin zuwan Annabi Muhammad(S.A.W)sannan sai yayi nufin tafiya 'kasar yaman, sai ya fita daga makka da safe, ya nufi 'kasar yaman, su kai wani gari da ake SAN'A'A , a dai dai lokacin zawali( Wato lokacin sallar azahar)Tafiyar wata d'aya kenan,amma yayita a d'an wannan lokacin, sai ya ga wannan garin kyakkyawan garine, ga haske ga kuma kayan marmari 'kanshi sai tashi yake, sai ya sauka a wannan garin don yin sallah da kuma cin abincin rana, sai suka nemi ruwa basu samuba, Dama Alhuda-huda shine  d'an jagora gurin neman ruwa domin yana ganin ruwa a duk inda yake koda kuwa a 'kar'kashin 'kasane kamar yadda mutum yake kallon ruwa a kofi idan yana gabansa, idan ya hango ruwan sai ya tona, sai su kuma shaid'anu su tona su d'ebo, sai aka nemi Alhuda-huda baya nan.
       'Katadata ya rawaito cewa, Manzon Allah(S.A.W)yace, (NA HANEKU DA KASHE HUDAHUDA DOMIN SHINE JAGORA ANNABI SULAIMAN (A.S)GURIN RUWA) sai Annabi sulaiman(A.S)ya nemi Alhuda-huda Bai ganshiba, sai yayi masa wannan Al'kawarin na narko, shi kuma HUDAHUDA lokacin da yaga Annabi sulaiman(A.S)ya shagala da sauka a 'kasar SAN'A 'A, sai ya tashi sama domin ganin tsahon duniya da fad'inta, ya duba gabas da yamma, sai ya hango gonar BILKISU, sai ya sauka a cikinta , sai ya had'u da wani huda hudan wanda ake kiransa da suna (AFIR) shi kuma ALHUDA-HUDAN Annabi sulaiman(A.S)ana kiransa da suna(YA'AFUR)sai Afir yace da Ya'afur ina zaka! Kuma daga ina? Sai Ya'afur yace daga SHAM nake tareda sahibina sulaiman d'an Dauda(A.S)sai Afir yace waye sulaiman? Sai Ya'afur yace sarkin mutane da Aljanu da shaid'anu da 'kwari da dabbobi da iska,  sai Ya'afur yace to kai kuma daga ina? Sai Afir yace anan garin nake, sai Ya'afur yace waye sarkin garin? Sai Afir yace wata macece , sai yace ya sunanta? Sai Afir yace BILKISU, Amma fa sulaiman yana da mulki babba, sai dai bai kai na BILKISU ba, domin ita tana mulkin Yaman ne gaba d'aya, A 'k'kashinta akwai jagorori guda Dubu goma sha biyu(12,000)kuma kowa ne jagora yana da maya'ka dubu d'ari(100,000)ko zamu je kaga mulkinta? Sai yace ai kuma ina tsoro kada sulaiman ya nemeni lokacin sallah, idan yana bu'katar ruwa, sai Afir yace, ai Annabi sulaiman(A.S)Zai ji dad'i idan ka bashi labarinta, sai suka tafi domin yaje ya gani bayan ya gani, sai ya koma gurin Annabi sulaiman(A.S)dai dai lokacin sallar la'asar, to Dama wannan lokacin an nemi ruwa an rasa kuma an nemi Alhuda-huda baya nan.
      Amma wannan zance marar Tushe ne a malamai.
     A ruwayar d'an Abbas kuma cew  akayi, wani yanki na rana ya saraya akan Annabi sulaiman(A.S)sai ya duba gurin da Alhuda-huda yake bayanan sai ya yi kiran wannan tsuntsun mai suna Nasir ya tambaye shi cewa ina HUDAHUDA? Sai yace Ranka ya dad'e! Bansan inda yayi ba, kuma ban aike shi ko ina ba dayake shine shugaban tsuntsaye, sai Annabi sulaiman(A.S)yayi fushi sai yace , sai na azabtar da shi azabtarwa ko kuma in yankashi, ko kuma yazo min da wata hujja mai 'karfi, sai ga HUDAHUDA ya dawo, sai Nasir yace dashi ina kashiga yau? Ga shi Annabi sulaiman(A.S)Ya yi rantsuwa sai ya azabtar da kai,   sai HUDAHUDA yace kuma bai togace komaiba,  sai yace  a'a yace sai dai in kazo masa da hujja mai 'karfi,  sai ya ce yawwa, sai ya tashi ya tafi gurin Annabi sulaiman(A.S)yana zaune akan kujerarsa, lokacin da ALHUDA-HUDAN ya kusanci Annabi sulaiman(A.S)sai ya d'aga kansa sama ya shin fid'a fuka fukansa a 'kasa da jelarsa yana jansu domin nuna Tawaki'u ga Annabi sulaiman(A.S)Sai Annabi sulaiman yasa hannu akan ALHUDA-HUDAN sai ya funcika yana mai cewa ina kake ina nemanka, to zan azabtar da kai azaba mai tsanani, sai HUDAHUDA yace ya Annabin Allah kaji tsoran tsayiwarka agaban Allah, sai Annabi sulaiman(A.S)ya girgiza, sai ya yi masa rangwame, sannan sai Annabi sulaiman(A.S)yace ina ka tafi? Sai HUDAHUDA yace , kamar yadda Allah yake fad'a ackin Alkur'ani cikin suratun namli ayata 22 cewa:-

Zanci gaba insha Allahu

Musha ruwa lpy.