Friday, March 20, 2020

SUBHANALLAH

Tun bayan da Mushirakan Larabawa suka kori Manzon Allah (SAW) daga garin Makkah yayi hijira tare da sahabbansa zuwa Madinah, daga baya Manzon Allah Ya sake dawo wa yaci Makkah da yaki (akayi Fathu Makkah), Musulunci ya kafu, shekaru sama da dubu daya da dari hudu da suka gabata ba'ayi wani lokaci da aka hana musulmai sallah a masallaci ba a fadin Kasar Saudiyyah har da Makkah da Madinah ba sai wannan karon

Jiya mahukuntan Saudiyyah sun bada umarnin rufe Masallacin Manzon Allah (SAW) dake birnin Madina da kuma Masallacin Harami dake birnin Makkah saboda masifar cutar annoba da ta addabi duniya (Coronavirus)

Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo yace:
Mu sani cewa lalle babu wata musifa da ta wuce a jarrabeka a cikin addininka, yau gashi ana ta rufe Masallatai, ana hana fitowa sallar Jam'i, har sallar juma'a da yawa daga kasashe sun bayarda sanarwa a dakata sakamakon wannan cuta, Lalle wannan abun tsoro ne! Kamar Allah Yayi fushi da mutane ne, yace: Ku fita ku bar min dakuna na (Masallatai) tunda barnaarku a bayan kasa tayi yawa.

Babbar musiba ce a rabaka da dakin Allah, a ce babu Umarah, babu Dawafi, babu sallar jam'i, lalle babu musibar da tafi musiba a cikin addini, tabbas Allah Yana fushi da mutane, Ya zama wajibi mu koma mu tuba ga Allah.

Allah Ka yafe mana, Ka kawo mana saukin wannan masifa Amin

No comments:

Post a Comment