Wednesday, February 19, 2020

TAKAITACCEN TARIHIN 'YA'YAN ANNABI (S.A.Ws), MATA:

TAKAITACCEN TARIHIN 'YA'YAN ANNABI (S.A.Ws), MATA:

1. Zainab (R.Ah) Ita ce babbar 'yar Annabi (S.A.Ws), kuma an haifeta shekaru biyar bayan aurensa na farko, lokacin yana da shekaru talatin a duniya. Ta kar6i Musulunci kuma an aurad da ita ga wani danginta Abul As bin Rabi. Tasha doguwar wahala sanadin rauni da Kuraishawa suka mata lokacin Hijirarta zuwa Madinah, wanda shi ne ya yi sanadin rasuwarta a farkon shekara ta 8, bayan Hijirah.

Ta haifi da mai suna Ali (R.A), da kuma diya mai suna Ammah. Ali ya rasu a zamanin Annabi (S.A.Ws). An ce wannan Alin shi ne mutumin da ya zauna a kuturin Annabi (S.A.Ws) a lokacin shigarsa Makkah, cikin nasara.

Mukan karanta cikin Hadisi kan cewar, wata yarinya ta kan hau bayan Annabi (S.A.Ws) a lokacin da yake Sujudah cikin Sallah; to wannan yarinyar dai ita ce Ammah 'yar gidan Zainab (R.Ah). An ce ta jima a duniya bayan rasuwar Annabi (S.A.Ws).

Sayyidina Ali (R.A) ya aure ta bayan rasuwar Fatimah (R.Ah), matarsa ta farko. An ce ita Fatimah da kanta a lokacin rasuwarta, ta nuna kaunar wannan auren ya auku. Basu haifu ba da Sayyidina Ali (R.A). Bayan da Sayyidina Ali (R.A) ya rasu, sai kuma ta sake auren Mughirah bin Naufal (R.A), wanda daga gareshi ne a ke jin kila ta samu wani da da ake kira Yahya. Ta rasu a shekara ta 50 bayan Hijirah.

Insha Allahu rubutu na gaba akan Rukayyah (R.Ah) 'yar Annabi (S.A.Ws). Muna kuma rokon Allah maji rokon bayi ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen ya Qadiyal Haajah

No comments:

Post a Comment