Saturday, December 2, 2023

BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU

BULAGURON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF KASHI NA BIYU A kashi na ɗaya mun tsaya a dai-dai inda "Mai makon ma su amsa wannan gayyata da ya yi musu", sai ma suka ki ko saurarensa. Kuma duk da cewar an san larabawa da karimci, maimakon gwada wannan karimci nasu sai suka shiga yi masa abin da bai kamata ace ya fito daga bakinsu ba, a matsayinsu na shugabanni. In gajarce muku labari, fitowa ma fili suka yi ɓaro-ɓaro suka ce da shi, basa son ganinsa a wannan garin nasu. Da dai a kalla kamata ya yi ace Manzon Allah (S.A.Ws) ya samu kyakkyawan tarbo da kuma jawabi mai daɗaɗawa daga gare su Tun da yake sune shugabannin kabilarsu.
To amma maimakon haka, kurum sai ɗaya daga cikinsu ya kaɗa baki ya ce, 'Kai ne Allah Ya zaɓa a matsayin Annabi!' Wani kuma da ba'a ya ce: 'Duk yanzu Allah Ya rasa wanda zai zaɓa ya zama Annabinsa sai kai? Shi kuma na uku sai ya ce: 'Kai ni ba na ma son yin magana da kai, domin idan kai Annabi ne, yin gardama da kai jawo wa kai rigima ne, idan kuma kana kwaikwayon Annabawa ne, to don me zan ɓata lokaci na, ina magana da Annabin karya?" Manzon Allah (S.A.Ws) wanda yake kamar dutse ne wajen dauriya da hakuri, bai ɓata rai ba, kan irin abin da waɗannan shugabannin suka yi masa. Maimakon haka, sai ya shiga ƙoƙarin saduwa da talakawan garin. Amma duk cikinsu, babu wanda ya tsaya ya saurare shi. Maimakon haka ma sai suka nuna gara ma ya san inda dare ya yi masa, ya bar musu, garinsu. Lokacin da ya fahimci cewar duk irin abin da yake son nuna musu, ba za su fahimce shi ba, don haka sai ya yanke shawarar barin garin. To, amma su ma kyale shi ya fita lami lafiya, basu yi haka ba. Maimakon haka, sai suka tara fitinannun yaran garin, inda suka fito titi suna yi masa ature, kana suna (faɗa masa rashin kunya da bakaken maganganu), wasu kuma na jifansa. Allah Sarki! An yi ta jifansa da duwatsu, ko ina jikinsa yayi jina-jina, yadda har takai, takalmansa suka manne da kafafunsa saboda jinin da ke zuba. Ya bar garin cikin wannnan zullumi na bakin ciki. MU HAƊU A KASHI NA UKU Allah yasa mudace alfarman fiyayyen halitta Annbin rahama Muhammad (S.A.Ws) ✍️*Ahmad Musa*

TAMBAYA NA HUƊU (0004) MENE NE ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA

TAMBAYA NA HUƊU (0004) MENE NE ABUBUWAN DA SUKE KAWO NUTSUWA A CIKIN ZUCIYA To yan'uwa akwai abubuwan da malamai suka yi bayani cewa, suna kawo nutsuwa a zuciya, ga su kamar haka: 1. Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar duk wata shirka da bidi'a da abin da yake kaiwa zuwa gare su.
2. Shiriya da hasken da Allah Yake jefawa a zuciyar bawa, wanda duk lokacin da aka rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci. 3. Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da ilimin mutum ya yalwata, zai samu jindadi a zuciyarsa. 4. Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin Allah "Wadanda suka yi imani, zuciyoyinsu suna nutsuwa da zikirin Allah" Suratu Arra'ad aya ta (28). 5. Kyautatawa bayin Allah, saboda duk mutumin da yake yin kyauta zai kasance cikin kwanciyar hankali, kamar yadda marowaci yake kasancewa cikin kunci. 6. Fitar da kyashi da hassada daga zuciya. 7. Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida. 8. Barin baccin da ba shi da amfani. 9. Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin karawa akan haka. 10. Rashin cakuduwa da mutane sai gwargwadon bukata. Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke jawo bakin ciki da damuwa da kuma kunci. Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad 2\22. Allah Ne Mafi sani.

Wednesday, November 29, 2023

TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI?

TAMBAYA NA UKU (0003) MENENE BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI? Malam, menene bambanci tsakanin nifakul amali da i'itikaadi? To Malam: Nifaqul i'itikadi (wanda ake kudurcewa a zuciya) shi ne boye kafurci da kuma bayyana Musulunci, kamar yadda wasu mutane suka yi a zamanin Manzon Allah (S.A.Ws), duk wanda ya siffantu da wannan to ba musulmi ba ne, kamar yadda Allah ya yi bayani a suratul Munafikun. Amma nifakul-amali (munafuncin aiki) kuwa to shi ne wanda ya zo a cikin hadisin Abdullahi dan Amr inda Annabi (S.A.Ws) yake cewa: "Dabi'u guda hudu duk wanda suka kasance tare da shi, to ya zama cikakken munafiki, wanda kuma ya ke da daya daga cikinsu to yana da dabi'ar munafukai har sai ya bar ta: idan ya yi zance ya yi karya, idan aka amince masa ya ci amana, idan ya yi alkawari ya yi yaudara, idan ya yi husuma sai ya yi fajirci". Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: (34) da Muslim a hadisi mai lamba ta: (106). In mutum ya siffantu da daya daga cikin wadannan dabi'u guda hudu, to bai fita daga Musulunci ba, saidai yana da tawayar imani. Allah Ne Mafi sani.

Tuesday, November 28, 2023

BULAGORON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF: KASHI NA ƊAYA (01)

BULAGORON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF: KASHI NA ƊAYA (01) Bayan shekaru tara tun lokacin da Allah Ta'ala Ya fara saukan masa da wahayi, Manzon Allah (S.A.Ws), ya yi ta kokarin isar da sakon Allah Ta'ala ga mutanen Makkah, kuma ya dukufa don kokarin shiryarwa da kuma gyaran al'ummarsa. In ban da wasu 'yan kalilan da suka karbi sakon Musulunci, ko kuma suke taimaka masa ko da yake basu Musulunta ba, kusan sauran mutanen Makkah sun tashi ne haikan, wajen kokarin azabtar da Shi da kuma wulakanta Shi, tare da Sahabbansa.
Baffansa Abu Ɗalib, yana daya daga cikin mutanen kirki da suke agaza masa duk da cewar bai shiga Addinin Musulunci ba. Shekara guda bayan rasuwar Abu Ɗalib, sai Kuraishawa suka samu abin da suke so, inda suka kara tashi haikam wajen irin musgunawar da suke yi, ba tare da samun mai kwaban su ba. A can Ɗaif, wanda shi ne gari na biyu mafi girma a dukkan yankin Hijaz (watau kasar Makkah), akwai wata kabila da ake kira banu Thakif, wadanda suma masu fada a ji ne, kuma suna da 'yar dama. Don haka sai Manzon Allah (S.A.Ws) ya kama hanya zuwa garin na Ɗaif, domin kokarin shawo kansu, su shiga Musulunci, kana kuma su taimakawa Adddinin na Islama, tare da Musulmin da Kuraishawa ke ganawa ukuba, yadda a nan gaba kuma zai zama wata cibiya ko kuma sansanin yada Addinin Musulunci. Da isarsa Ɗaif, sai ya zarce (zuwa) (Jaula) ziyarar manyan hakiman garin, su uku, inda ya ziyarci ko wannensu ɗai-ɗai da ɗai-ɗai. Kana ya kira su don amsa wannan muhimmin sako na (Musulunci) da kuma bayar da tasu gudunmuwar ga Annabin Allah Ta'ala. Mai makon ma su amsa wannan gayyata da ya yi musu, MU HAƊU A KASHI NA BIYU Ya Allah kayi salati ga Annabin rahama Muhammad (S.A.Ws) *✍️*Ahmad Musa*

Tambaya NA BIYU (0002)SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) NE FARKON HALITTA?

Tambaya NA BIYU (0002)SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) NE FARKON HALITTA? Akwai hadisin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne farkon wanda aka fara halitta, sai dai hadisin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba (458), sun ce hadisin karya ne. Fadin cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ne farkon wanda aka halitta, ya sabawa Alkur'ani, ta bangarori da dama, ga wasu daga ciki: 1. Allah Ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad (S.A.Ws) mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah Ya tabbatar da cewa gabadaya mutane daga Annabi Adam aka same su, kun ga idan ka ce Annabi Muhammad shi ne farkon halitta hakan ya sabawa ayoyin Alkur'anin da suka yi bayanin hakan. 2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad (A.A.Ws), tun daga mahaifinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kun ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan. Zance mafi inganci shi ne : farkon abin da Allah Ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba (2653): "Allah Ya kaddara abubuwa kafin Ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa", Kun ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta, ba Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba. Allah Ne Mafi sani.

Monday, November 27, 2023

Tambaya NA ƊAYA (1) SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO?

Tambaya NA ƊAYA (1) SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO? Ya halatta macen da ba Musulma ba ta yiwa Musulma kitso, saboda a zance mafi inganci, al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace, shi ne daga guiwa zuwa cibiya, babu bambanci tsakanin kafira da Musulma a cikin haka, domin a zamanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Yahudawa mata suna shiga gidan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ba a samu suna yin shiga ta musamman ba, idan za su shigo, sai dai in kafirar ta na da wani sharri da ake jin tsoro, to wannan mace za ta iya suturta daga ita, sannan kuma mutukar akwai Musulma, to ita ta fi dacewa ayi hulda da ita. Allah Ne ma fi sani.

Saturday, March 12, 2022

AKWAI ABUBUWA DA YAKAMATA KUSANI GAMEDA AIKIN POLICE INTELLIGENCE OFFICER DA KUMA VEDEO DA AKE YAƊA WA DA SHI AKAN DCP ABBA KYARI

AKWAI ABUBUWA DA YAKAMATA KUSANI GAMEDA AIKIN POLICE INTELLIGENCE DA KUMA VEDEO DA AKE YAƊA WA AKAN DCP ABBA KYARI Hakia DCP ABBA KYARI mutum ne kamar kowa zai iya yin daidai zai iya yin akasin haka kamar yadda a fage na aikinsa zai iya yin kuskuri saboda kasancewar shi ɗan Adam ajizi, amma abin dubawa anan shin alkhirin sa ya rinjaye sharrin sa? DCP Abba Kyari shine fa wadda yayi nasarar kama Tawagogin ‘Yan ta’adda Har ‘Dari da Hamisin 150… a gurare daba-daban a kuma lokaci daban-daban, dan Allah mutambe kanmu shin DCP ABBA KYARI wani hanya yake bi har ya iya kama wa'yannan tawagogin yan ta'addan? Idan baku manta ba a shekara ta 2021 DCP ABBA KYARI ya tura kwararrun jami'an tsaro daga cikin yaransa, suka yi shiga irin na tsagerun yan ta'adda a wani gari cikin Jihar Imo a matsayin tarko na dabarun ɓadda sawu irin na INTELLIGENCE POLICE domin su kama wani kasurgumin 'dan ta'addan IPOB, kamar yadda zaku gansu a cikin hoto na farko, kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu
Da wannan ne yasa nake tunanin ɗaya cikin biyu zai iya faruwa gameda vedeo da ake yaɗawa gameda DCP ABBA KYARI Na farko kodai yazamana yayi aiki ne na dabarun ɓadda sawu irin na POLICE INTELLIGENCE OFFICER ko kuma anyi editing ɗin CCTV CAMERA ɗin ne aka bada shi ga hukumar NDALE saboda suyi amfani dashi gurin kama DCP ABBA KYARI domin yan ta'adda suci karensu ba babbaka, saboda akwai na'ura da dama da za'a iya amfani dasu wajen editing CCTV CAMERA kamar irin su 1. EaseUS Video Editor (Windows) 2. Video Editor (Windows) 3. HitFilm Express (Windows) 4. Davinci Resolve (Windows) 6. Avidemux (Windows) 7. Blender (Windows) 8. Lightworks (Windows) 9. Clideo Video Adjuster (Online) 10. Adobe Spark (Online) 11. Panzoid Video Editor (Online) 12. ClipChamp (Online) Waɗannan windows ɗin duk ana iya amfani dasu wajen editing vedeo a CCTV CAMERA, da wannan ne nake bawa hukumar NDALE shwara dan Allah tayi amfani da iMOVIE (MAC) saboda ta gano hakiƙanin vedeo dake CCTV CAMERA domin tabbatar da gaskiya Ya Allah kaine masanin abinda ke ɓoye ya Allah ka tabbatar mana da gaskiya kuma ka tona asirin azzalumai ✍🏻Ahmad Musa