Saturday, April 18, 2020

MAKIRCIN SHAIDAN KAN AL'UMMAR ANNABI (S.A.Ws) PART 1

Ali dan Abi dalibi ya bada wani labari da yake nuna makircin shaidan da yake shiryawa a hankali har ya rugurguza mana imani.

Wannan labari akan wani mutum ne mai imani da yawan aiyukan addini, da yake zaune nesa da garinsu domin kuwa garin
mamaye yake da alfasha.

A cikin wannan garin akwai wasu mazaje su uku ‘yan uwan juna da suke kula da
kanwarsu wadda ita ma babu ruwanta.

Wata rana sai sukayi shawara su dauke ta su kaita can wajen gari inda wancan bawan-Allah yake zaune ko ta kubuta
daga munanan dabi’un da suka mamaye garin.

Daga farko wannan bawan-Allah ya ki don kuwa yasan hadarin kadaituwa da budurwar da ba matarsa ba.

Amma sai nan da nan shaidan ya rada masa “kaga, kai ne mutumin da yafi kowa tsoron Allah a wannan waje.

Idan kaki karbar wannan yarinya har ta koma wancan garin, lallai da sannu zata lalace.” Don haka sai ya karbe ta.

Sai ya kar beta.

Da farko yana bar mata abinci a bakin kofar dakin ya tafi abinsa, sai shaidan ya dawo ya kuma rada masa cewa” ta yaya kasan cewa hakika tana samun abincin?

Zai fi ka rinka dakatawa kadan kana
tabbatar da cewa tana samun abincin ba wata dabbar bace ke cinyewa.” Saboda haka sai ya rinka tsayawa.

Bayan wani dan lokaci sai shaidan ya rada masa “kaga ga yarinya mai hazaka a kulle a gidan nan kai kuma gaka da irin wannan tarin ilimi.

Ba zai fi ba ace ka fara koyar da ita in yaso zamanta anan baya zama hasara ba gaba daya?”.

To daga nan fa sai ya fara koyar da ita darussa.

Da farko yana barin wani abu a tsakaninsu saboda gudun fitina, amma sai shaidan ya bashi shawara a zuci cewa ya kamata ya rinka kallon idanunta yayin karatun domin ya tabbatar da cewa tana koyon, ba barci kawai take yi ba abinta.

Daga nan fa shaidan yasan cewa tarkon nasa ya danu. A hankali a hankali har sai da mutumin nan yayi wa yarinya ciki.

Bayan hakan ya auku sai ya dawo ya rada masa cewa ”to fa kai ne mafi imani a garin nan.

Yanzu ko mutuncin ka ya gama yawo (in
har aka gano wannan katobara).

Abin da yafi sai ka kashe ta ka binne, in yaso sai ka cewa ‘yan uwanta ‘rashin lafiya tayi, kuma duk da kokarin ka na neman magani sai da cutar ta kashe ta’.
Wannan tabbas zai fi wancan abin kunyar”. Haka kuwa ya yi.

Da ‘yan uwanta suka zo duba ta, mutumin har da hawaye, yana basu labarin yadda cuta ta kamata, da irin kokarin da yayi na magani har ta mutu.

Babu wata jayayya suka yarda, don kuwa kowa ya san shi mutumin kirki ne.

A ranar da daddare duk su ukun sukayi mafarki cewa wannan mutumin ne ya kashe musu ‘yar uwa ya binne a wani wuri.

Da safe sukayi ta mamaki da ta’ajabi ga yadda duk su ukun sukayi mafarki iri daya, sai suka yi shawara da su je wannan wuri da suka gani a mafarki su tone.

Ai kuwa sai ga gawar yarinya har da juna biyu. Suka kamo wannan mutum suka tafi da shi cikin gari gaban jama’a.

Mutane suna can suna shawarwarin yadda za’a yi da shi sai shaidan ya zo masa ya nemi mutumin da yayi masa sujjada inyaso shi kuma zai fitar da shi daga wannan bala’i.

Da mutumin ya ga ba mafita sai ya yarda kuma ya aikata hakan (wal iyazu billahi).

Daga nan shaidan ya bace ya rabu dashi ya barshi a cikin masifa da halin da na sani.

Haka kuma wato shaidan bazai taba hakura ba har sai ya ga mutum ya cika.

Ya 'Yan Uwa kunji Fa Makircin Shaidan akan mu....Ya Allah ka tsare mu da Shaidan Alfarmar Annabi (S.A.Ws)

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Friday, April 17, 2020

DALILIN FARUWAR LUWADI DA MADIGO A DUNIYA

Akwai Wani GARI wanda ake kira da SADUMU, shi Wannan garin ba wani babban gari bane, kuma Mutanen da ke cikin sa duk kafiraine, su wayannan kafirrai sun kasance basa son baki, basu son bako ya shiga garin nasu na SADUMU.

To ganin Haka da SHAIDAN (LA) Yayi sai Ya rikida ya cenza suffa ya zama tsoho, sai ya nufi garin yana shiga sai ya fara tara wadannan mutane Yace dasu "Idan har kuna son baki su daina zuwa Wannan gari naku, to ga yadda zakuyi.

Sai kawai ya basu kansa yace suyi LUWADI da shi, da wasunsu sukayi sai yace to ku dinga yiwa maza haka, idan kuma matane, sai macce ta dinga neman 'yar uwarta Macce.

Sannan yace to duk wanda yazo Wannan gari naku sai kuce masa sai kunyi wannan abin da shi, to daga nan kowa ma zai dinga qin zuwa garinnan naku.

To Wannan mummunan abu da shaidan (LA) ya nuna musu sai yayi tasiri a zuka tansu, dan haka duk mutumen da yaje wannan gari sai kawai su bishi sai sunyi wannan abu da shi.

Wannan tasa Allah (swt) ya aiko musu da Annabi Ludu (AS) domin yayi musu gargadi akan wannan mummunar al'ada da sukeyi ya kira su zuwa ga hanyar shiriya.

La'anar ALLAH ta kara tabbata ga SHAIDAN (LA)

( Mai neman karin bayani ya duba RAUD L-UNUF ko kuma sasul Anbiya'I)

ALLAH YA TSARENI YA TSAREKU YA TSARE DUKKAN MUSULMI DAGA WANNAN BALA'I WAYANDA KUMA KEYI ALLAH YA SHIRYESU SU DAINA..

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Thursday, April 16, 2020

KARO NA FARKO A TARIHIN NIGERIA...

Shugaban kasa Buhari ya amince an war-ware bashin dake tsakanin gwamnatin Nigeria da kamfanonin samar da wutar lantarki, da kamfanonin rarraba wutar da masu dakon iskar Gas da ake amfani dashi, an biya su bashin su Naira biliyan 190, sannan aka kara musu da Naira biliyan 30 su samar da wuta na watanni uku masu zuwa, wannan ne karon farkon da aka war-ware bashin, tun bayan sayar da kamfanin samar da wutar da gwamnatin PDP karkashin jagorancin Good Luck Jonathan tayi a 2013.
.
Kamfanonin sun karbi Naira biliyan 220, shugaban kasar ya umarci Ministan wuta Saleh Mamman da manajan NNPC su dauki nauyin kula da samar da iskar Gas din kai tsaye.
.
Shugabanni kamfanonin sun tabbatar da kudaden sun shiga hannun su, tare da alkawarin samar da wuta mafi karanci na awanni goma sha shida a kowane rana.
Yankuna da dama na Nigeria sun fara shaida hakan, yayin da wasu yankin suke jira tukun.
Wutar da aka samar daga jiya 15 ga wata, shine irin sa na farko a tarin Nigeria, wurin yawa da kuma karfi.

Thursday, April 9, 2020

FADAN KABILANCI A SOUTHERN TARABAN NIGERIA, GA MAFITA

Firgici da razana na tashin hankali na kokarin kewaye yankunan din (Donga, Takum And Wukari Roads), Al'amarin yana so yasake girmama, ya kamata musani Kowane Mutum yana da hakkoki masu yawa a kan Dan'uwansa Mutum

Musamman abokin zamantakewa na Kasa ko Gari, ko Makaranta, da duk wani waje da alaka ta kan hada juna kamar wajan aiki da Makamantansu.

Babban ma'auni na hakkin junanmu a kanmu shi ne wanda ya zo a cikin Hadisai na cewa: "Mu duba duk abin da muke so a yi mana sai mu yi wa mutane shi, mu kuma duba duk abin da muke ki a yi mana shi sai mu guji yi wa mutane shi".

Misali;
Kana kin a wulakanta ka ma'ana baka son a wulaqantaka, kuma kana son a girmamaka, to a nan sai ka ki wulakanta mutane kuma ka
girmama su.

Wannan hadisi da za a yi aiki da shi, da Duniya gaba daya ta zauna cikin aminci, da ta Juya ta sama tsaftsaf, da so ya game tsakanin mai kudi da talaka, da mai ilimi da maras ilimi, da miji da mata, da 'ya'ya da iyaye, da malami
da dalibi, da mai mulki da wanda ake mulka, da dukkanin nau'i na mutane gaba daya.

Amma yau abin haushi,

Mai kuddi na kyamar Zamantakewa da Talakka, haka Mai Mulki na fifita kan shi fiye da talakka, Mata da Miji ba'a zaman Lafiya, Uba ko Uwa na Fada da 'Ya'yansa, Malami na Hassadar Dalibinsa.

Addu'ar Mu anan itace,

Ya Allah ka sa mu cika da Imani kuma ka debe mana Hassadar Junan Mu, Ya Allah ka bamu Lafiya Da Zaman Lafiya.

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Friday, April 3, 2020

TAMBAYA MAI MA'ANA KU TSAYA KU KARANTA

Nakasance inayin azumin litinin da alhamis. Sai ake cewa wai yanzu sha'aban yashigo Ramadan ya gabato wai bai halalta incigaba ba saidai inanjeyishi har bayan idi sallah incigaba shin malam hakane?

AMSA
*****
Watan Sha’aban wata ne da Manzon Allah (SAWW) yake yawaita azumin tadawwa’i a cikinsa fiye da kowane wata a bayan Ramadan. Kamar yadda
Uwar Muminai A’isha (Allah Ya yarda da ita da mahaifinta) ta ruwaito cewa “Manzon Allah (SAWW) ya kasance yana
azumi har mu ce ba ya shan ruwa, kuma in yana sha ruwa har mukan ce ba ya azumi.

Amma ban ga Manzon Allah (SAWW) ya cika wata yana azumi ba, sai na watan Ramadan, kuma ban gan shi yana yawaita azumi ba kamar
yadda yake yi a watan Sha’aban.” (Buhari da Muslim).

Ibn Hajar ya ce,"Wannan Hadisi dalili ne kan falalar azumin Sha’aban." (Fathul Bari Mujalladi na 4 shafi na 253).

A cikin Lada’iful Ma’arif shafi na 247 Ibn Rajab ya ce “Amma azumin Manzon Allah (SAWW) a mafi shaharar Sunnah ya ksance yana azumtar Sha’aban fiye da kowane wata.” Yayin da San’ani ya ce "A cikinsa (Hadisin) akwai dalilin cewa ya kebance Sha’aban da yin azumi fiye da waninsa.” (Subulus
Salam, Mujalladi na 2 shafi na 342).

Kuma Sayyada A'isha (RA) ta ce “Watan da Manzon Alla (SAWW) ya fi so ya azumnta a cikin watanni shi ne Sha’aban, sannan ya sadar da shi da Ramadan.” Ahmad ya ruwaito shi a Musnad, kuma Abu Dawuda da Nisa’i sun ruwaito shi, kuma Hakim ya ce Sahihi ne a bisa sharadin Buhari da
Muslim, yayin da Albani ya inganta shi a cikin Abu Dawud. Hadisi na 2124.

Akwai ruwayoyi da dama kan falalar yawaita azumi a watan Sha’aban, kuma malamai sun karfafa haka tare da yin maganganu a kai. Ni dai ban san in da akace baabu kyau azumtar SHA'ABAN ba.

JAN HANKALIN DA ZANYI ANAN

• Jama'a Kowane bangare na rayuwa ana lura da abin da ake kira da harshen nasara “Specialization” don sauraro
da auna mai magana a bangaren, da kuma bashi kima ko rashin kima.

Likita da cuta.. lawyer bangaren
kare tuhuma da sauransu…
'Politician' abin da siyasa…
“Engineer”… da dai sauran
bangarori na rayuwa.
To shin bangaren da ya shafi addini ba shi da irin wannan
“Specialization” ne? sai ka ga…

kowa yana tsoma baki game da abin da ya shafi addini? Kowa yakan yi fatawa sannan ya dage bisa matsayinsa, ko da kuwa ba zai iya karanto maka aya guda ta kur’ani daidai ba? ballanta ma a ce ya san harshen da wannan shari’a ta sauka da shi?

Magabata masu dimbin sani na
shari'a har Alla-alla suke idan a ka samu mas’ala sabuwa ya zamanto wani daga cikinsu ya hutasshe amsarta, saboda girman hadarin gaggawa cikin bayar da fatawa.

A kan hukuncin shiga garin da
annoba ya fadawa, sai da Umar
(RA) ya tara kusan dukkan
Sahabbai da suke tare da shi, ko akwai wanda ya taba jin
hukuncinsa, duk suka ce ba su da masaniyar hakan, sai daga can karshe ne, aka samu AbdurRahman bn Auf (RA) ya yi bayanin hukuncin…

JAMA’A LALLAI MU YI HATTARA! MU RIKA MAGANAR DA MUKE DA MASANIYA BISA HUJJA DA DALILI!

ABIN DA BA MU SANI BA MU CE
ALLAH SHINE MASANI.

*WALLAHU A'ALAM*

https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1

Thursday, April 2, 2020

YADUWAR ALFASHA NA KAWO CIWUKKA DA ANNOBA


Annabi (S.A.WS) yace “Alfasha bata taba bayyana a cikin wasu mutane har sukai ado da ita ba face annoba ta watsu acikinsu da ciwukkan da basu taba ganin irin suba.