Thursday, April 2, 2020
YADUWAR ALFASHA NA KAWO CIWUKKA DA ANNOBA
Annabi (S.A.WS) yace “Alfasha bata taba bayyana a cikin wasu mutane har sukai ado da ita ba face annoba ta watsu acikinsu da ciwukkan da basu taba ganin irin suba.
Basu kuma taba tauye mudu da sikeli ba face an kama su da tsananin fari, da kuncin rayuwa da zaluncin shugaba,
basu taba hana zakkah ba face an hanasu ruwan sama badon dabbobi bama da kwata kwata ba ayi musu ruwanba,
basu taba warware alkawarin Allah ba da alkawarin manzonsa face Allah ya dora makiyinsu akansu, makiyan suke dauke da sashen abunda suka mallaka,
matikar shuwagabannin su ba suyi hukunci da hukuncin Allah ba sai Allah ya sanya tsananinsu a tsakaninsu”.Ibn Majah 4019 da Ihya Kutub Al’arabiyah.
Annabi (SAWW) Yace “idan kukai kasuwanci irin na ruwa, kuka riQi bindinan shanu, kuka amince da hatsi (ma’ana kuka karkata zuwaga holewa rayuwa), ku kabar jihadi, to Allah zai buga kaskanci akanku
bazai cireshi ba har sai kun koma zuwaga (cikakken) addininku”
Sunan Abi Dawud 3462
Maktabatul Asriyyah, (Hadisi ne
Sahihi).
ABIN LURA:
<• Yaduwar alfahsha na kawo ciwukka da Annoba.
<• Tauye mudu= yana kawo fari, da kuncin rayuwa (kamar tsadar kaya da rashin kudin saye dss),
<• Zaluncin shugaba da Hana zakka= yana kawo hana ruwan sama.
<• Karya alkawuran Allah= yana janyo rinjayen makiya.
<• Rashin hukunci da littafin Allah=yana kawo tsanani tsakanin mutane.
<• Holewa da barin jihadi= yana kawo kaskanci.
MAFITA:-
~~~~~
Itace komawa zuwa ga cikakken
addini, in akai haka za aga canjawar Al’amura.
Yaa Allah ka kawo mana karshen wadannan matsaloli da muke fama dasu a Nigeria da Duniya baki daya Ameeen..
https://ahmadmusainc.blogspot.com/?m=1
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment