Tuesday, November 28, 2023
BULAGORON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF: KASHI NA ƊAYA (01)
BULAGORON MANZON ALLAH (S.A.Ws) ZUWA ƊA'IF: KASHI NA ƊAYA (01)
Bayan shekaru tara tun lokacin da Allah Ta'ala Ya fara saukan masa da wahayi, Manzon Allah (S.A.Ws), ya yi ta kokarin isar da sakon Allah Ta'ala ga mutanen Makkah, kuma ya dukufa don kokarin shiryarwa da kuma gyaran al'ummarsa.
In ban da wasu 'yan kalilan da suka karbi sakon Musulunci, ko kuma suke taimaka masa ko da yake basu Musulunta ba, kusan sauran mutanen Makkah sun tashi ne haikan, wajen kokarin azabtar da Shi da kuma wulakanta Shi, tare da Sahabbansa.
Baffansa Abu Ɗalib, yana daya daga cikin mutanen kirki da suke agaza masa duk da cewar bai shiga Addinin Musulunci ba. Shekara guda bayan rasuwar Abu Ɗalib, sai Kuraishawa suka samu abin da suke so, inda suka kara tashi haikam wajen irin musgunawar da suke yi, ba tare da samun mai kwaban su ba.
A can Ɗaif, wanda shi ne gari na biyu mafi girma a dukkan yankin Hijaz (watau kasar Makkah), akwai wata kabila da ake kira banu Thakif, wadanda suma masu fada a ji ne, kuma suna da 'yar dama. Don haka sai Manzon Allah (S.A.Ws) ya kama hanya zuwa garin na Ɗaif, domin kokarin shawo kansu, su shiga Musulunci, kana kuma su taimakawa Adddinin na Islama, tare da Musulmin da Kuraishawa ke ganawa ukuba, yadda a nan gaba kuma zai zama wata cibiya ko kuma sansanin yada Addinin Musulunci.
Da isarsa Ɗaif, sai ya zarce (zuwa) (Jaula) ziyarar manyan hakiman garin, su uku, inda ya ziyarci ko wannensu ɗai-ɗai da ɗai-ɗai. Kana ya kira su don amsa wannan muhimmin sako na (Musulunci) da kuma bayar da tasu gudunmuwar ga Annabin Allah Ta'ala. Mai makon ma su amsa wannan gayyata da ya yi musu, MU HAƊU A KASHI NA BIYU
Ya Allah kayi salati ga Annabin rahama Muhammad (S.A.Ws)
*✍️*Ahmad Musa*
No comments:
Post a Comment