©AJI NA ƊAYA DARASI NA UKU
®JERIN HARUFFA MASU KAMA DAJUNA DA KUMA YANDA AKE RUBUTA HARUFFAN LARABCI.
1. Haruffa masu kama da juna a rubutawa.
2. Haruffa masu kama da juna a wajan faɗa
1. Masu kama da juna a rubutawa su ne:
ب ت ث. Ba'un Ta'un. Sa'un
ج ح خ. Jimun Ha'un Kha'un
د ذ. Dalun. Zalun
ر ز. Ra'un Zayun
س ش. Sinun. Shinun
ص ض Sadun. Dadun
ط ظ. Ɗa'un Za'un
ع غ. Ainun. Gainun
ف ق Fa'un. Ƙafun
2 Masu kama da juna a wajan faɗa su ne:
ا . ع. Alifun. Ainun
ث س ص. Sa'un Sinun Sadun
د ض. Dalun Dadun
ذ ز ظ. Zalun. Zayun. Zadun
Yanda ake rubuta haruffan larabci.
Haruffan larabci suna da hanyoyi hudu da ake bi don rubuta su. Ma'ana kowane harafi a cikinsu yana iya cangawa gida hudu kenan kamar haka:
1 Hanya ta farko Rubutasu dai-dai.
Ana rubutasu dai-dai ne batare da sun hadu da juna ba a daya daga cikin dalilai biyu:
a) Lokacin da ake karantasu ko rubutasu dai-dai ba a cikin kalma ba.
b) lokacin da suka zo a karshen kalma ya zama kuma suna bayan harafi daya daga cikin wadannan haruffa shida ( ا د. ذ. ر. ز. و. ) ، a nan ma sai a rubuta su a tsin-tsinke kamar haka :
ا. ب. ت. ث. ج. ح. خ. د. ذ. ر. ز. س. ش. ص.
ض. ط. ظ. ع. غ. ف. ق. ك. ل. م. ن. ه. و. ي.
Alhamdu lillah wassalatu wassalamu Ala Rasulillah الحمد لله والصلاة والسلام على رسول الله
Sa'annan masu bukatar sauran darusa da suka ɓuce musu sai su Shiga wannan link kuyi liking kuma ku following domin samun Darsuka akan hakan 👇👇👇👇👇👇👇�
Page-https://www.facebook.com/111306253888584?referrer=whatsapp
No comments:
Post a Comment