Wednesday, March 4, 2020

YANDA ZAKA NEMO DUK LAMBOBIN WAYARKA DA SUKA BATA

Lura da yanayin yadda wasu zaka ga sun mallaki lambobin waya masu matukar mahimman ci a gurinsu amma da zaran sun rasa Sim kat nasu sai kaga sun kasa samo wayannan lambobin saboda tun farko basu sanya su a Email ko Drive nasu ba, toh akwai hanya mafi sauki da zaka iya samo wayannan lambobin koda kuwa kai ka goge su da hannunka

Dafari zaka shiga wannan Ling din:

https://m.facebook.com/mobile/messenger/contacts

Bayan ka shigeshi zai baka za6i da wace opera zaka bude, sai ka za6a duk opera da yafi kwanta maka arai sai ka bude da ita kamar yadda yake a hoto mai alphabet (A).
Idan Facebook naka na kan operan ka, zai bude maka kaga lambobinka  kamar yadda yake a hoto mai alphabet (M) amma idan Facebook naka baya kan operan ka zai nemi kasa password naka da numbar waya ko email da ka bude account naka dashi  kamar yadda yake a hoto mai alphabet (H)

 Sai ka log in bayan ka log in sai ka jashi sama zai nuno maka lambobinka kamar yadda kuke gani a hoto mai alphabet (M), duk numba da kake so sai ka ta6a zai fitar maka da asalin numbar  kamar yadda yake a hoto mai alphabet (D).

Insha Allahu rubutu na gaba shine YADDA ZAKA YI MAGANA DA KOWANI YARE A CHAT NAKA KO BAKA IYA BA.

Muna rokon Allah ya gafarta mana kurakuranmu ya kuma sa Aljannar Firdausi itace makomarMu baki daya. Aameen

No comments:

Post a Comment