Tuesday, March 10, 2020

TARIHIN ANNABI SULAIMAN(A.S)...5

 Abdullahi d'an Hamisu ya bada labari da isnadinsa, daga d'an mas'ud daga mahaifinsa, yace mun kasance tare da Manzon Allah(S.A.W)halin wata tafiya sai muka wuce ta wajan wata bishiya akanta akwai wasu 'ya'yan Kurciya guda 2 sai muka d'aukesu, sai wannan Kurciyar ta kawo 'kara gurin ma'aiki(S.A.W)sai manzon Allah(S.A.W)yace :-waye ya afkawa 'ya'yan wannan Kurciyar? sai mu kace mu ne, sai Manzon Allah(S.A.W)ya ce ku maida su gurbinsu.
        Ance Annabi sulaiman(A.S)ya ta'ba wuce wata turuwa akan hanyarsa ta zuwa mukibi, sai tururuwar take cewa, tsarki ya tabbata ga Ubangiji maigirma, mai yafi girma daga abinda ya bawa iyalan Annabi Dauda(A.S), sai Annabi sulaiman(A.S)yayi murmushi saboda maganar da wannan tururuwa ta fad'a, sai ya gayawa rundunarsa wannan magana, sai sukayi mamaki, sai Annabi sulaiman(A.S)Ya ce:-in baku labarin abinda yafi wannan ban mamaki? sai sukace na'am, sai yace:-wannan tururuwa ta kasance tana cewa, Kuji tsoron Allah a fili da 'boye, da kuma kyakkyawan nufi a gareshi ahalin wadata da Takauci, da kuma adalci lokacin fushi da lokacin yarda.
       An rawaito cewa, Annabi sulaiman(A.S) ya fita ro'kon ruwa a tare da shi akwai mutane da Aljanu, sai suka wuce ta gurin wata Tururuwa ta bud'e fuka fukanta ta d'aga hannayanta tana cewa, Ya Ubangiji mu halittace daga cikin halittunka ba mu da wadatuwa ga arzikinka, kuma kada ka kamamu da zunuban 'yan Adam ka shayar da mu, sai Annabi sulaiman(A.S)yace wa wad'anda suke tare dashi ku koma Ha'ki'ka   za'a shayar da ku da addu'ar wanin ku.
        Akwai kuma wata 'Kissa ta wadin Namli, wacce Allah Ubangiji(S.W.T)yace :- "KUMA AKA TATTARA, DOMIN SULAIMAN, RUNDUNONINSA, DAGA ALJANU DA MUTANE DA TSUNTSAYE, TO SU ANA KANGE SU(GA TAFIYA) "suratun Namli.
      HAR A LOKACIN DA SUKAJE KAN RAFIN TURURUWA WATA TURURUWA, TACE, YA KU JAMA'AR TURURUWAI ! KU SHIGA GIDAJANKU,KADA SULAIMAN DA RUNDUNONINSA SU KARKARYA KU, A HALIN BASU SANI BA"suratun Namli.
        Sha'abi da ka'ab sukace, Annabi sulaiman(A.S)ya kasance idan zai yi tafiya yana d'ora Ahlinsa da masu yi masa hidimada sakatarorinsa akan abin hawansa, su kuma dabbobi suna tafiya a gabansa tsakanin sama da 'kasa iska tana ri'ke da su,sun tafi zuwa yaman, sai suka bi ta madina wato birnin Manzon Allah(S.A.W)a yanzu, sai Annabi sulaiman(A.S)ya ce, wannan shine gidan hijirar manzon Allah(S.A.W)wanda za'a aiko a 'karshen zamani, Aljanna ta tabbata ga wanda ya bishi kuma yayi imani da shi, sannan sai suka isa harami sai suka ga gumakan da ake bautawa, wad'anda ba Allah(S.W.T)ba, sun kewaye d'akin Allah, lokacin da Annabi sulaiman(A.S)ya wuce d'akin ka'aba, sai d'akin ka'aba ya kama kuka, sai Allah(S.W.T)yayi wahayi izuwa d'akin ka'aba da cewa, me yasa kake kuka,? sai d'akin ka'aba yace, ya Ubangiji wani Annabi ne daga cikin Annabakawanka, kuma tare da mutane daga cikin masoyanka, sun wuce ta kaina ba su sakko gareni ba, kuma ba suyi sallah a guri na ba, kuma ba su ambace ka a da'irata ba, kuma wad'annan gumakane a kewaye dani ake bauta musu bayan kai, sai Allah(S.W.T)yayi wahayi a gareshi da cewa kada kayi kuka da sannu zan cikaka da fuskoki masu sujjada a gareni, kuma zan saukar da Alkur'ani a cikinka,kuma zan aiko wani Annabi daga cikin Annabawa a 'karshen zamani daga gareka. mafi soyuwa a gare ni,kuma zan sanya wasu bayi a cikinka daga cikin halittuna masu yin bauta, kuma zan wajabtawa bayina wani abin wajabtawa wanda za suyi ta kwad'ayin tahowa zuwa gareka, kuma zan tsarkake ka daga masu bautar gumaka da shaid'an........
zanci gaba insha Allahu.

Asha ruwa lpy.

No comments:

Post a Comment